← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 77

Sashe 46

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

miƙo mun sadakina a hannuna harma yaimun ƙarin dubu ashirin akai, Innarmu ma ta bani dubu ashirin tare da ƙaramin da akwatin ɗan kunne ƙarami na gwal haka tai ma su Yaya Saratu ma. Tanadi ne da'ita sosai dan hatta su Rayya da Jinjin ta siya musu ɗan kunnen yana adane tana jiran lokacin bikinsu yayi ta basu, kamar yadda ta bamu. Allah sarki uwa mafi uba ko da uban sarki ne. Fitowa dani Baba Sojanmu yayi ayarin dangin Gawata da dangina suka rufa mun baya. Ko da muka fita mun tadda Yaya Zubaida da Yaya Jamila suna cacar baki faɗa ne ma ya kaure a tsakanin dangina da dangin Gawata akan motar da za'a saka Amarya sabida duk bus suka kawo. "To menene wai dan ta shiga bus shin wai ita wannan ɗiya taku da aketa yi mana wulaƙanci tun a kawo akwati ɗiyar gwal ce ko kuwa itace tafi sauran mata ne baiwar Allah amsarki nake jira? Duk Gawata ne ya jawo mana wannan yarinya sai kace zinare dan bala'i da masifa " Cewar Yaya Jamila da take son rikicin ya ƙara tsayi. Ai kuwa Yaya Saratu ta amshe da cewa. "Ai ko ba gwal bace tafi ƙarfin ɗan uwanku kuma kun sani wallahi. Ya za'ayi ace babu motar amarya sai a bus za'a kaita kamar kowa? " Inna Abida da Inna Mairamu ne suka iso wajen. Baba Sojanmu ya girgiza kai kawai ya shigar dani mota ya ajjiyeni. Zai saki hannuna saina riƙe hannun nashi, juyowa yayi muka haɗa idanu mukai shiru. "Hindu kije ki zauna da haƙuri, duk wata tarbiyya da iya zama da miji kin koya daga Ruwaiya bana jinku. Allah yayi albarka, ni da mahaifiyarki duk mun saka ma Aurenki albarka kuma da amincewarmu akayi." Hannunshi ya zare ya wuce ya koma cikin su Baba Dogara. Su kuma a waje anata rikici fa ƙata. Inna Abida tace. "Ko a amalanke akace muje sai mu je ai Saratu. Allah dai ya kyauta ko jeeb suka kawo ai dai a ƙauye zamu barota dai ko? To ku shisshiga muje kawai Yahanasu kuje ku shiga waccan ta gaban. Yarinya dai ta ja ma kanta, ita da cikar guri sun yi hannun riga. Bama tasan menene ƙauye ba wallahi, hakanne ya sanya ma ta amince. Ga kaya da Ruwaiya ta dandatsa sai dai a dawo da wasu dole" Luba ce ta shigo ta zauna kusa dani, da matasan ƴan matan gidanmu. Amaren da aka ɗaura aurenmu tare duk suna waje ganin gulma motar kaya ta wuce tare da su Akarami harda Qazzafi shima ya bisu abinda Inna Mairamu bai mata daɗi ba kenan. Ƙarfe uku da ashirin ayarin motocin amare da angwaye ta kama hanyar jama'are fuu muka fice a na'ibawa ajjiyar zuchiya na sauke sassanya har wata iskace naji tana shigata tako ta ina, sai naji kamar an saukemun Kano a kaina ne. Soyayya kenan. Haka mukaita tafiya a titi ƙawayen Amarya da su Inna Yahanasu sai abinci suke ci suna nishaɗinsu sai hira akeyi ana dariya da abincinsu suka tawo kula babba. Jallof ce lafiyayya da naman kaza da Innarmu taima ƙawayenta malamai. "Hinduwa ga abincin daure kici tafiyace mai yawa a gabanmu Allah kaɗai yasan yaushe zamu isa dan daga nan zuwa Bauchi ma nanda isha'i albarka bare mu ɗauki hanyar ƙauyan naku" Cewar Innah Yahanasu. Dake motar duk mune babu dangin miji ko ɗaya sai direba da yake bare saina sa hannu na karɓa rabona da abinci tun jiya da daddare babu ma wanda yake tani bare a bani abincin inci. A hankali nake tauna abincin ina tunano yadda muka tsara rayuwar Aurenmu yadda zata gudana. Ina fatan kada mu samu cikas dan zama da uwarmiji dole sai mutum ya kiyaye da duk abinda zaiyi, mu kuma rayuwa mai kyau cike da soyayya muka tsara. Murmushi nayi ina hango ɗakina a idanuna muna guje_gujen soyayya ni da Gawata, ko muna cin abiinci muna hirarmu ta soyayya. Da wannan tunane_tunanen harna gama cin abincin ta miƙo min mirinda na karɓa na shanye tas nai gyatsa dan na ƙoshi dam. Mun daɗe muna tafiya duhu ya rufa, gudu muke yi babu sararawa a jajjere muke tafiya motoci biyar huɗu ta mata ɗaya ta ango da abokanshi. Bamu muka tsaya ba sai takwas na dare a wani ɗan ƙauye a cikin gidan mai. Anan mukai la'asar magriba isha ina fitowa daga masallacin mata Gawata ma yana fitowa idanu muka haɗa muka sakarma juna tattausan murmushi mai ɗauke da ma'anonin da mu kaɗai mukasan abinda hakan ke nufi. Zuwan Yaya Saratu tasa ya wuce sum_ sum ni kuma na lumshe idanuna tare da binshi da kallo. Motarmu muka koma Yaya Saratu ta siyo mana gurasa da tsire da yawa ta miƙo mana. Abokan ango suka miƙo mana ruwa da kaji da Lakasera motarmu ta sake ɗagawa bamu muka shiga jama'are ba sai wajajen sha ɗayan dare gari yayi duhu dunɗum ya ɗaure babu wutar lantarki ko kaɗan. A ƙofar gidan motocinmu suka tsaya. Mata da tsaffi suka tare mu da guɗa yiriri_yiriri. A mugun galabaice duk muka sakko mukai ayari aka shiga daga ciki kai tsaye ɓangaren su Nanno aka wuce dani ga hayaniyar ƴan biki nan muna jiyowa daga ragowar ɗakuna. "Maraba lale kune a darennan sannunku da zuwa ku shigo mana" Cewar wata mace da bansan wacece ba. A tsakiyar ɗakin Nanno aka zaunar dani ina cikin mayafi kirib. Gaisuwa ta gudana a tsakankaninsu kafin Inna Mairamu tace. "Ga Amarya mun kawota. Tana hannun Allah tana hannunku a riƙeta da Amana dan Allah Hindu yarinyace mai hankali" Innah Yahanasu tace. "Ƙwarai kuwa tana da hankali da kuma biyayya. Allah dai ya basu zaman lafiya" "To Ameen dare yanzu yayi kamata yayi kuje ku kwanta zuwa safiya a zagaya da'ita ɗakunan sauran mazauna cikin gidan bisa al'ada. Akulu a bisu da abinci a nuna musu ɓarayin nata, ga acibalbal nan ki tafi musu dashi." Miƙewa nayi jikina a sanyaye tarara ni tunda muka shigo ƙauyen naga yadda yake damma darene ga duhu duk saina karaya fuskar Gawata kaɗai nake tunowa inji salama sai ƙarfi yazo mun, kuma ni jarumace gaya. Nifa in a rami zai sani muddin tare nake dashi babu komai. Ƙarasawa akayi damu ɓarayin nawa gasunan guda biyu nawa yasha fenti ruwan omo haka muka kutsa kai muka shiga ɗan ƙaramin tsakar gidan. "To ga ɗakinnan ku shiga can kuma Amaryar wanshi ne a ciki abokin tagwaitakarshi tare duk akayi bikin." "To mun gode sosai" Yaya Saratu ta faɗa. "To bari a kawo muku abinci da taburmai" Ta faɗa tare da miƙama Yaya Saratu aci balbal ɗin dake hannunta. Mu kuma muka shiga da sallama zuwa ciki. Nan naji su Yaya Saratu suna salati da hmmm da hmmm abakunansu akwai magana mai yawa nasan da ba dan idanun su Innah mairamu ba da naji maganganu a darennan. Wani irin turirin zafine a ɗakin kamar gidan biredi. "A gaskiya inaga sai dai mu yada zango a tsakar gida kawai ɗakinnan bazai zaunu ba. Kuzo muje tsakar gida kawai. Dole muka fice tsakar gidanma ba zata ɗaukemu ba mun cika tsakar gida mun cika ɗakunan sai kwasar wasu akayi zuwa sassan gidan. Tabarma manya manya aka baje mana duk muka zauna Yaya Saratu ta shiga rabon wata jalof ta masifa ƙandas babu man kirki bare kayan miyan kirki babu maggi sai gishiri cakwai harda nama tsoka guda guda yankan firit firit. Nima aka miƙo mun loma ɗaya da nakai bakina na tauna ƙuƙus kusan uku a jere da dabara na haɗiye shinkafar kawai nayi gum amman ban kuma gigin sake sanyawa a bakina ba. Wallahi kowa kasa ci yayi dole aka jujjuje a fantekar da suka kawo mana ga yinwa ga dare. Har su Yaya Saratu saida suka fita ko zasu tarar da masu abun siyarwa amman babu kowa sai karnukan ƙauye. Haka suka dawo gashi motar kaya bata isoba bare muci gara, ko su Qazzafi su shiga gari su nemo mana wani abun,kunji wannan? Bayan ko wacce ta kwanta da yinwar cikinta sauro da zafi suka hanamu bacci dole kowa ta miƙe zaune ni dai ina kwance ina ɗigar zufa ko kaya ban sake ba da lace a jikina zafi kamar zai halakani. Sai jefin asuba gari yayi sanyi muka samu muka runtsa asubar fari muka tashi shida da rabi sai ga motar kaya tare da su Akarami su kam a wani ƙauye suka nemi waje sukai kwanciyarsu sai da sukai sallar asuba suka tawo. Ina cikin uwarɗaki ina kallon silin ɗin saman ɗakin da tagogin ɗakin su Qazzafi suka soma shigo da kaya tare da abokan Gawata. "To ai wallahi kayannan ba zasu yi ma ɗakinnan ba wannan gandama gandaman royal yaushe zasu zauna a ɗakinnan. Akarami ku fita da kayannan waje zamu soma shinfiɗa kafet a ciki da waje tukunna. Mu yinwa ma muke ji sai mun karya mun yi wanka ya kamata ayi wannan aikin" Cewar Inna Yahanasu. Qazzafi yace. "To bari a jibge kayan a tsakar gidan asan an sallami mai motan" Ni dai ina tsaye, su Luba ne suka zari bokatai aka nuna musu rijiya suka soma jidon ruwan wanka kowa na watsawa yaji daɗi a jikinshi. Nima aka saka mun naje nayi na fito Inna Yahanasu ta bani wata koriyar atampa mai tsada na saka da sabon ɗankunne da sarƙa humra ta miƙo mun daga cikin humrorin aurena da suka tawo dashi daga Biu na mutsuttsuka ko ina ta ciki da wajen kayana, banyi kwalliyaba kwalli na zirara kawai na zauna a tabarma. Sabida dangin Gawata sun so tozartamu abincin da muka kasa ci wallahi shi aka ɗumamo aka haɗo da ruwan kokko babu ko sikarin kirki aka kawo mana. Hmm nasan ramawa suke yi suma layi ya zagayo kansu. "Hmmm mutanannan da rigima suke neman mu Innah Abida jibi abincin jiya suka sake ɗumamo mana dan wulaƙanci. Kunga bari in fita in nemo wannan ango da abokanshi su kawo mana abinda zamu ci ko mu dafa da kanmu" Fuu ta fice bansan yaya suka ƙare ba sai ga shayi da madara cikin babban robar fenti da biredai da ƙosai cikin fanteka abokan ango sun shigo dashi. Ƙanwar Nanno ce ta shigo dan taga an wuto mana da abinci. "Au shinkafarce bakwa so shine ba zaku yi magana ba zaku
Chapter 46 · 0% Book details