Sashe 43
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
JAMA'ARE:.
"Kinji halin da ake ciki Nanno, wannan dalilin yasa na tawo afujajan sabida a samu ayi abinda ya dace, zan yi magana da Qasimu yayi ƙoƙari mu gina inda zata zauna"
Cewar Gawata da isowarshi kenan ko ruwa bai sha ba ya tari Nanno da wannan magana ga Nawata a zaune yana jinsu. Ga kuma Goggo Akulu ƙanwar Nanno itama tazo daga Misau acan take Aure.
"Mijinyawa ni gaskiya in shawara zan baka ka haƙura da yarinyarnan kawai ka huta ma ranka. Iyayen yarinyarnan sun nuna basa sonka to dole ne, ni a halin da ake ciki wallahi ko ƙaunar yarinyar nima bana yi. Ya za'ayi suce dubu ɗari kuɗin sadakinta sai kace zinari ko lu'u lu'u zamu siya, gonaki nawa zaka cire ka siya da dubu ɗari. Sannan ina zamu samu dubu ɗarin sadaki ga na kayan akwati tsakani da Allah fa. Ni dai kawai kayi zamanka a nan ƙauyen ita kuma ka barta ta Auri wanda iyayenta suke so. Bikinku tare kasan za'a haɗa dana ɗan uwanka. In fa a ƙauyannan ne baifi a kashe dubu ɗarin ba da sadakin da lefe na alfarma da gini dukka dubu ɗari zata yi fa. Wannan maƙudan kuɗi har ina. Akulu kina jin yaron naki fa irin jarabar duniyar da zai kwaso? "
Goggo Akulu tace.
"Wallahi naji Yaya ni amman ina gani tunda su yaran suna son junansu Yaya ki sa mai haƙuri kawai ayi a wuce wajen. Kora da hali suka yi mai sabida ya nuna gazawarshi su samu hujjar cewa dama ba auren bane ya kaishi ba. Kinga ita yarinyar zai zama ya tsinkata sosai. Jibi fa yadda duk ya fice a hayyacinshi ya rame kamar wanda yayi ciwo fa. Yaya kiyi haƙuri kawai suje su samu iyayensu su sanar dasu halin da ake ciki. In yaso ba sai a haɗa auren ba kawai shi Nawata da kuɗinshi sannan Uwatale dubu saba'in ma ya isa a gama hidimar komai na bikinta."
Nanno tace ai ina ita bata yadda ba ba za'a Auri Hindu ba, a taƙaice ta tsani Hindu kamar yadda iyayenta suka tsanar mata ɗa. Damma duk wannan dambarwar kulleshi a sell bata sani ba, da batun takadda da yasa hannu, dama abubuwa da dama.
Gawata sai ya zama kamar majinuni sai sambatu da roƙon Allah yake yi. Qasimu da Nawata, da Abdulƙadiri ne sukaita rarrashinshi.
"Ka sassautama kanka in Allah ya kaimu gobe muje Azare mu samu Kawu Saminu mu yi mishi bayanin komai shi kaÉ—aine zai iya rarrashin Nanno tunda shine makwafin uwa da uba a wajensu."
Cewar Nawata kenan.
Wannan maganar bata sa Gawata zuchiyarshi ta nutsa ba har saida washegari suka isa Azare su uku suka gurfana a gaban Kawu Saminu tukunna su kai mishi bayanin duk abinda ke tafe dasu ga ba lokaci kwana biyu kaÉ—ai ya rage musu na wa'adi.
"Toh naji bayananku Mijinyawa ƙarami gaskiya iyayen yarinyarnan babu dattijantaka tattare dasu ko kaɗan. Amman ba zaka kunyata ba in sha Allah.
Sai dai fa a siyar da gonakinku na gado a raba a baka naka kayi hidimar da zaka yi dashi tunda kwanaki ma ɗan wajen Ladi ya tayar da maganar konakin. Yanzu abinda za'ayi duba da ƙarancin lokaci bari in shiga in kintsa sai mu kama hanya umm"
Tashi Kawu Saminu yayi ya shiga gida ya shiryo suka kamo hanyar jama'are sai yamma suka iso.
Tunda Nanno taji muryar wanta a tsakar gidan yana gaisawa da abokan zamanta ta ɗaure fuskarta tayi kicin_ kicin dan ta riga da tasan zuwa da dawowar zancan ilai kuwa ko da ya shiga aka gaisa sai ya shiga tausarta yana bata magana bata musu dashi dole ta amince amman fa ta ƙullaci Hindu sosai. Kunji inda ƙiyayyar ta samo asali ko?
"To shikenan Yaya na amince. Amman a ina zai samu kuÉ—in lefe da sadakin da suka yanka mishi, ga batun gini? "
"To Habiba tunda gadon yarannan ba'a gama rabawa ba, kwanaki ma ɗan wajen Ladi ya tayar da ƙayar baya to a saida gonakin a raba aba kowa tunda ba nomar suke yi ba a ciki, hayarsu kawai akeyi. In yaso ko guda ɗaya ce babba sa bari su mijinyawa Babba da mijinyawa ƙarami ko gaba in sun tara ahali zasu yi noma. Amman kafin a siyar ai ga Akulu tana nan bata rasa kuɗi tunda adashen gonakai take ma maza magidanta banda mata da take yi ma. Sai ta ara mishi ya kashe wutar gabanshi in aka gama saida gonakan aka raba sai ni da kaina in cire miki kuɗinki. Hakan yayi muku? "
"To shikenan ai Yaya babu damuwa bazai gagara ba ai kamar dubu ɗari biyar ya isheshi ya riƙe a hannunshi a gama komai da komai ko?"
"Lallai wannan yarinya tsadarta tayi yawan da ya wuce tunani amman yaya zanyi tunda Yaya yasa baki hmmmm dubu ɗari biyar fa Akulu? Tunda nake ban taɓa ganin maƙudan kuɗaɗe irin wannan ba"
Haka dai maganar ta ƙare Goggo Akulu dai a kwai kuɗi dubu ɗari biyu a jikinta take ta ɗauka ta ba Gawata akan a soma shiri.
Babu shiri suka wuce gidan magajiya wacce kusan kaf layin ita ke haɗama samari kayan Aure har adashe take yi musu, shi kanshi Nawata ya soma zubi a wajenta daga baya ya soma zubawa a asusu, babu shiri ya ɓalle asusun suka je wajen magajiya.
"To yanzu kaya kace za'a haÉ—a kamar na dubu É—ari da hamsin zuwa É—ari biyu harda akwati. Kai kuwa Gawata Æ´ar gidan sarkin ina zaka Aura?
Yarinyar sarki Aminu ado bayaro ce? Tunda nake haɗa lefe a ƙauyannan ban taɓa haɗa na dubu ɗari tim ba"
Magajiya ta jinjina abun sosai da sosai.
"Magajiya ai Tutar so tafi ɗiyar sarki a wajena. Wannan lefen a gidansu za'a karɓa da haƙurine kawai sannan dan Allah a ɗebo atampopin masu haske ruwan binni, pamtimotinma a ɗakko ruwan ƴan gayu"
"To naji. Akwatuna dai ina dasu seti uku daban daban bari insa Indo ta jawo maka ka zaɓa, gobe sassafe zan shiga Bauchi in siyo duk abinda ya dace kada ma kaji komai"
Nan ta kira Indo ta tuƙo akwati mai taya sonsonet a wannan lokacin su ake yayi. Mai ruwan madara ya zaɓa hawa uku babban lamba 1 sai mai binshi, da kuma na saman mai turawa, magajiya ta bada shawarar ya siya da wannan ɗan kutumburin na can saman wanda yawanci daddamu da Qur'ani ake sakawa wasu kuma su shaƙeshi da ɗankunnaye da sarƙa.
Nawata kuma kayan dubu hamsin yace a haÉ—o mishi akwati É—aya da mitsitsin na saman haka akeyi a lokacin shima hakan na yara Æ´an gata ne.
Washegari da yamma kuwa saiga Magajiya da akwatuna ciki_kici ta shigo dasu, kafin kace me maƙota suka cika gidan suna mamaki.
A lokacin su Gawata suna can cikin gida anata gini sun siyo bolo É—in laka sabida babu lokacin da zasu buga bulo da kansu.
Tsarin yadda suka ɗakko ginin nasu da bambamci shi Nawata banɗaki da madafi duk a waje yayi ma uwatale, sannan ɗakunan falle _falle saɓanin Gawata da yayi Kitchen a falo, banɗaki a uwarɗaki amman iyakar na wanka, sai akayi na tsugunno a tsakar gidan sabida ita ƴar binni ce ba a ƙauye ta rayu ba da estira ɗaki falle ɗaya a gefe, sai wani kwarmi da akayi da rariya a wajen kamar wajen wanke _wanke dai haka, da kuma wani gini da akayi Kitchen ne na tsakar gida na murhu.
Dukkansu abokansu ke tayasu aikin ginin sabida ayi sauri ayi abinda duk ya dace.
Suna cikin aikin ginin suka soma jiyo hayaniyar mata.