← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 77

Sashe 72

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafi ya karatu ya iyayen naki, kina jin labarinsu? " Murmushi tayi tace. "Suna lafiya tare muke dasu anan ba'a Najeriya suke ba Ammi" Gaban mamaki. masha Allah nayi tunanin turoki karatun suka yi. Nan aka haifeki ne Nafi? " "A'A a Gombe aka haifeni mu fulanin Gombe ne Ammi. Abbanmu aikine ya kawosu nan bamu daɗe da dawowa ba mu, amman shi ya kai shekara ashirin yana zaune anan" Magana take yi hausa_hausa turanci_turanci ( kun tuno da Uzairu Zuchiyata? Dariya zata halakani). Mun taɓa hirarmu cike da wayewar kai. Azgar na kira a waya na haɗamu mukai magana a tare harma na ba su Shamsiyya suka gaggaisa kana yayi mana sallama. Muma lokacin komawarmu aji yayi muka ɗunguma muka koma, nan muka bar Nafisa da Nabila tunda su ba lekca garesu ba abu suka shigo yi. Tilis muka koma gida yau dai kam na gaji sosai. Ina shiga gida kiran Yaya Saratu ya shigo mun. Bayan na ɗaga mun gaisa tace. "Mutan landan baki fiye shiga group ɗin gida ba. Qazzafi matarshi ta haihu tun shekaran jiya. Innah Turai ma ta haihu, sai Auren Salamatun Innah Abida daya mutu anata tattaunawa a group." Baki na buɗe ga murnar samun ƙaruwa, ga ta'ajibin mutuwar Auren Salamatu. Yanzu Salamatu duk yadda take ɓare soyayya da Dr sai da ya saketa. Ita da take ganin babu macen data kaita sa'ar Aure a gidanmu ita da tayi Aure suna rayuwa a ƙasar waje? " "Ke dai bari ai gidan ya ɗauka in faɗa miki, da zaman gidanma gagararta yayi, ko tsakar gida bata isa ta fito ba kin dai san yanayin gidan namu. Ai kunya take ji sabida irin ƙafafa da jiji da kan da take yima mutane in suka zo. Tai ta saka suturu masu tsada tana ganin kamar mu wuya ma muke sha. Komai tace Dr Dr to Dr dai ya sallameta kuma dukka igiyar ta ƙare" Baki na buɗe. Kika ce igiyar ta ƙare me tayi da har zai mata saki uku haka? " "Hmmm Hindu gidanmu ana munafurci ƙaƙas wallahi, shi yasa duk runtsi tunda kana aiki ka zauna a ɗakin aurenka. Ashe a baya sau biyu yana sakinta Innah Abida suna rufewa hatta Baba Sojanmu bai san da wannan saki na baya ba. Ina wani zuwa da suka yi tayi kusan wata biyu a gida? To lokacin ma ashe ba auren. Aka shiga aka fita kafin iddar ta sauka a kanta aka dawo da'ita. To kinji abinda yake faruwa aure da Dr ya ƙare" Kaina na jinjina ina mamakin gidanmu da jama'ar cikinshi. Gidan yawa masifa ne wallahi. Da yawa ƙalilanne mai daɗi amman gutsiri tsoma sunnar gidan yawa ce. To Yaya Saratu yaran fa? " "Waɗanne yara kuma da sun riga sun girma Ummi tana jama'a ita da Baba Sadiq ragowar suna ɗakin mijinsu. A can ta barosu daga ita sai kayanta danma ta tsira da gwala gwalan da take zuwa tayi mana ƙarya dasu. Hmmmm Hindu Mijin Zubaida fa ya ƙara Aure jiya Amarya ta tare" Ai ba shiri na buɗe idanuna da suke rufe ina saurarenta. Sai naji abun wani iri. Aure kika ce fa Yaya. Shine bata ko faɗa mun ba?" "Hindu kenan ai zaucewa Zubaida tayi damma Innarmu nata ƙarfafata. Wallahi yayi aurenshi yarinyar mai gidanshi na wajen aiki ya Aura. Wai ashe yarinyar tun tana shekara goma a duniya aka bashi aurenta yake ta renon soyayyarta yanzune takai munzulin girbi. Yarinya ƙarama Sa'ar Batulunta fa kayan takaici. Ai ko kishin za'a haɗaka gara a ɗakko maka wacce zaku goga macuwat. Amman daɗin ma tana aikinta ta sake samun matsayi a ma'aikatarsu yaranta sun girma ba haihuwa yanzu take yi ba. Mu dai shawarar da muka bata shine ta ja gefe ta basu waje suci karensu ɗanye babu babbaka. Gidane taci gida, yaranka koma menene duk inda aka buga sune manya babu wani ɗa da za'a haifa ya fisu matsayi. Kafin a mori ƴaƴan Amarya an mori naka, ba da abinda Innah Abida take gadara ba kenan harma take ganin mu ba ƴaƴa bane? " Hmmm ni ai tuni na dawo daga rakiyar rijalu suna yin abinda suke sone a sanda suke so. Mune muke da hanya ɗaya su hanyoyine dasu. Abinda na fahimta da maza a binciken da na yi maza suna da son kai, sannan su a kullum sun fi son abu sabo. Wannan son abu sabon ya ja ma mata matsaltsalun da mazan kuma suka gujesu kuma asalin abun dominsu ya faru. Mata na shafa man sanya fari domin maza, mata na shan ƙwayoyin bature sabida jikinsu da zatinsu ya fito domin maza, mata na kashe kansu da zumar ƙiba,masu ido da kwalli kuma a saka musu ruwa, ko ai musu allurar ƙiba da farin, mata na zuwa ai musu ɗinki, mata na shan magungunan mata da suke birkita musu yanayin tsarin halittarsu, mata na cushe _cushen magungunan mata domin su tsuke al'aurarsu wanda daga ƙarshe ake barinsu da ciwo, naga wacce gabanta ya rifta, naga wacce gabanta ke fitar da mugunya, naga wacce gabanta ke ɗoyi wallahil azeem. Ku tambayi likitoci ku sha labari. Nima a baya nayi kuma na samu matsalar da nasha zuruftun asibiti sosai kafin Allah yasa na dace, cutar sanyi ce ta kamani na sha baƙar wuya. Mune ƙarin gashi, duk abinda mace fa zatayi sabida ta burge saurayi, miji ne, da duk wannan abun haka zai ajjiyeki ya ɗakko wacce bata kai rabin rabinki ba ya faɗaɗa darajarta gaban mamaki. Duka waɗannan ababe dana lissafo, ba hasashe ko shaci faɗe bane abune da yake faruwa damu mu mata, in bai faru dake ba, ya faru da maƙociyarki, ƙawarki, yarki, mahaifiyarki, ƙanwarki, ko ƙanwar mijinki. Mata wallahi mu yi ma kanmu faɗa nifa yanzu ko murmushi nayi wallahi nayi ne a ƙashin kaina bana buri da fatan in burge uban kowa face kaina. Muma sai mun koyi son kanmu a duk yadda muke. Babu abinda ma yafi komai takaici kamar irin matan da suka ɗauki aure yi dole ko mutuwa. Suke ganin rayuwa ba zata kai musu ba sai da namiji A kullum ina buga misalina da layla Ali othman. Kuga yadda rayuwa ta kai mata bayan mutuwar aurenta, ku dubi yadda ta tsaya ta mayar da hankalinta ta jajirce ta tsaya da ƙafafunta. Mijinta na yanzu kuga yadda yake girmamata, ku duba wayewa da fahimtar rayuwa tattare da'ita. Gogewarta tana bani sha,awa da ace mata haka muke son kawunanmu muke rabuwa da mazajen da suke neman halaka rayukanmu da ba haka ba. Hmmm bari in tsaya kafin ace mun kwangilar yahudawa na karɓo kamar yadda ake ce ma Layla ta raina maza hahaha harna tuno rikicinta da magaji. ( Ummu Nabeeha, dake muka tattauna Rikicin Layla da magaji, a lokacin da abun ya faru) Wanda ya san zancan mu haɗe a kwament sekshan. "Hindu kina jina kuwa? " Naji muryar Yaya ta ratsa dodon kunnena. Inaji na tafi wani tunanin ne kawai Yaya Saratu" "Hindu inaso dama nayi miki magana akan mijinyawa. Nasan halinki da tauri, da kafiya, Hindu da kuma fishi, Wannan dalilin yasa kowa ya ƙyaleki baya ko yi miki maganar mijinyawa bare Asama'u" Idanuna na lumshe kawai inaji da ana iya mayar da zamani baya irin yadda na taɓa gani a wani shiri na Indiyawa yadda suke murɗa agogo a dawo baya da tuni na murɗa makarantar da mijinyawa ke sana'ar lemo ma wallahi bazan yadda in shiga ba. "Hindu ina fatan kuna waya da mijinyawa dai yanzu ko? Bai sake zuwa ya kawo ƙorafinki a wajeba ba dai tun wannan zuwan na farko, kuma batun tafiya da kika yi babu saninshi, wallahi yace ya lamunce miki, ya kuma yafe mala'ikun Allah su shaida, dan haka ba kya cikin tsinuwar mala'iku. Hindu ni ko dan sabida Asama'u bana so ki rabu da mijinyawa wallahi" Murmushi nayi nace. Me yasa sabida ita Yaya Saratu? Na ja numfashi tare da gyara zamana. "Yauwa bana son uwarta, ko ita, ko Uwatale ɗaya a cikinsu yayi nasara a kanki. Hindu ba zaki iya nuna kamar baki san Asama'u mijinyawa yake Aure ba ki zauna ko dan maƙiyanki ba? Wallahi nasan kaɗan daga cikin dakiyarki ne wannan. Na sanki farin sani tun kina yarinya ƙarama, nasanki da shanye abu, da dakiya" Dariya nayi gajera. Yaya Saratu kinsan tunda na taso ni bana yin abu sabida mutane zasu ce, ko gudun suce. Bana daga cikin matan da suke kashe kansu dan su burge maƙiyi, kana ai su Uwatale na riga na gama dasu. Ni naso zama da mijinyawa, ni kuma nace na barma Asama'u shi har abada dan wallahi billah bazan taɓa iya mishi biyayyar aure ba, ba kuma zan taɓa bari ya kwanta dani ba. Kinga kuwa wuta zan shiga in nace naji na gani zan zauna dashi dan kawai in burge su Uwatale. Naji sitatiment ɗinki ma na ɗasu da kika ce wai gara duk runtsi mutum ya zauna a gidan mijinshi, sabida gudun gulmace_gulmacen ƴan gida. Hindu ba haka take ba Yaya Saratu. Ni bana yin komai domin kowa. Yaya Saratu Asama'u fa" "To yaya zaki yi da sharaɗin Baba Sojanmu? " Saina dawo zan san yadda zanyi" "Amman uwar Asama'u ba ƴar halak bace. Hindu narantse miki da Allah zan nemi har garin da take aure inje in gargasa mata maganganu ko Allah zaisa in huce, zuchiyata tayi sanyi. Ko yaya mijinyawa yake iya gudanar da mu'amalar Auratayya da yarinyar da shi ya zaɓa mata suna ta girma a gabanshi. Hindu dole ki ƙi shi kaiii ina wallahi ina bayanki Hindu" Dariya muka kwashe dashi da haka mu kai sallama na ajjiye wayar na wuce banɗaki nayi wanka na ɗauro alwalar magriba, ina fitowa Shamsiyya na shigowa da waya a hannunta. "Hindu Nagoɗi kinga irin zagin da maza suke yi miki kuwa akan rubutun da kika yi. Dan Allah bakya jin wani iri? " Lallai shamsiyya sai kace ba ƴar jarida ba? Mu da aka sanmu kamar aljanu dan naci da kafewa. Jibi yadda muke saka mutum yayi aman abinda ke zuchiyarshi ya fesama al'umma, in bai yi wasa ba sai dai ya shiga ɗaka yayi kuka mun ruftashi. Hmm wannan zagin ni ko buɗewa banyi ba. Saima ranar da nafi nishaɗi nake dubawa. Wannan zagin a wajena matattakalace ta ɗaukaka. Ana
Chapter 72 · 0% Book details