← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 77

Sashe 49

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ƙofar gida muka rakasu ayarin ƴan ɗakinmu. Na kalli unguwar da kyau na kuma kallonta da kyau hmmm akwai aiki ja ƙau. "To Hinduwa mu kam dai sai kuma sanda kika zo Kano zamu sake haɗuwa in Allah ya ƙaddara kinzo lokacin muma munzo kenan, tunda ba zama muke yi ba" "Tunda ku gwagwarene bare a biku duk garin da kuke ba. Ya kamata kuyi ma kawunanku faɗa ku nemi matan Aure" Cewar Yaya Zubaida kenan. Dariya Akarami yayi yace. "Ni kam da tawa a hannu shekara bazan kuma yi babu Aure ba. Sai dai kuyi ma Qazzafi magana ya nemo wata a cikin gida ko waje kunga muma sai a gangama ai mana auren tare ko wanne ya tare a bariki da matarshi, to yanzu ƙila ya mayar da hankalinshi akan Sailuba ta lungun Baba Lukumanu, ta jima sosai tana nuna mishi so duk da bata furta ba bama zata iya ba. To yanzu tunda ba Hindu sai yayi maneji ai." Qazzafi dai bai kula wannan zance na Akarami ba. Mun ɗan jima a tsaye harma Gawata daya fito a wani gida ya tawo aka gaggaisa fuskarshi sai hannuri take yi yanata satar kallona. Shi ya raka su Akarami mu kuma muka shige ciki ƙofar gidan danƙam da yara suna kallon su Akarami da kakinsu na sojoji. Mun shigo mun tadda faten shinkafa aketa sha na manja babu kyan gani. Muna shiga ɓarayina muka tadda Inna Yahanasu na haɗa murhun dutse. "Saratu aje a nemo mana cefane zamu ɗaura ko taliyace aci munfi ƙarfin wulaƙanci fatensu kuma a mayar musu dashi babu mai sha." Ai kuwa yadda akayi kenan sai cefane akayi suka dafa jallof mai lafiya da nama har dare suka yi ta, bamu muka ci abinci ba sai la'asar. Wannan girki yasa anyi rigima mai ƙarfi har maƙota Yaya Jamila ta shigo taita rashin mutumcin wai an rainasu ana ƙyamarsu lamarin daya haifar da rikicin da sai da maza dattawan gidan da su Gawata suka shiga aka kwantar da tarzoma Bayan lafawar komai Gawata ya shigo yanata bada haƙuri akan da daddare zasu sa ayo girki a kawo haka ma da safe. "Ai ku barshi wallahi bama so munyi girkinmu har dare kuma gobe ma zamu yi na safe muyi kuma na rana kafin mu kama hanya mu koma garinmu. Ai babu komai yaro kuyi duk yadda kuke so yana da kyau" Shi dai yaita bayar da haƙuri fitarsu babu daɗewa suka aiko nono jingim da fura kowa yasha ya more, ni dai ina gefe kamar kunne tunda ni suka fi haushi sama da kowa a hakanma tausar zukatansu kawai suke yi. Nan aka shiga rabon kayan fulawa aka kai na ɓangaren su Nanno komai randa guda aka aika musu harda ƙaramin buhun shinkafa aka kai musu. Wajajen Magrib akaita shigowa ganin ɗaki kamar hauka gungu_gungu aketa zuwa harda ƴan unguwa mai nisa da daddare sai gasu gungu _guda wai sunzo ganin waje mu dai mamaki ya ishemu kai subhanallah. Washegari sassafe suka dafa taliya da shayi akaci akayi hani'an Gawata ma yasa an kawo koko da ƙosai. Gidan babu hayaniya sosai sabida baƙi sun warwatse. Suma sha ɗaya nayi suka gama shiryawa basu yi girkin rana ba sunce a ƙoshe suke, sai dai kafin su tafi anyi mun cefanen kayan miya da yawan gaske harda ɗanyen nama da kai da ƙafafun rago. Har ƙofar gida na rakasu har saida naga tafiyarsu Gawata ya rakoni na shiga ɓarayina. Jikina yayi wani irin sanyi ƙalau, sai na jini babu guiwa. Ina shiga na saka sakata nayi shigewata ciki ina ƙarema ɗakin kallo yanzu ne na samu zarafin kallon komai cikin nutsuwa. Wani sanyi nake ji yana gangaromun kawai yanzu nan ɗakin aurenane ni da Gawata da yaranmu zamu rayu a ciki. Masha Allah, Allah shine abun godiya mai girma da ɗaukaka. Kitchen ɗina na shiga komai fes dashi kaya a jere gwanin sha'awa sosai tire na ɗakko tare da basket mai hannu na fito tsakar gidan nawa na baza kai da ƙafafun ragonnan a tire na ɗaura bisa katangar ɓarayina dake ba bisa gareta ba sosai danma bani da tsayi da zan iya hango mutanen cikin gidan. Kayan miyan kuma na juyesu a basket masu kyau dasu gwanin sha'awa. A gefe can wajen inuwa na ajjiyesu Naman kuma na shige dashi ciki na kunna risho na ɗaura tare da saka musu kayan ƙamshi tunda babu wutar lantarki a jama'are ga firji da kayan kallo amman dai sun zama abun ado kawai. Gawayi na fita na ɗakko wanda suka yi girki suka kashe na kara biyu a jikin rishon na koma na share tsakar gidana tas nice harda saka ruwa da omo na wanke sumintinnan tas har wani ɗan rumfar gini da akaimun da ginannen murhun itace a wajen saida na wanke, wajen wanke_wanke na da wanki wani ɗan rami akayi kamar bawon wanka na turawa da rariya a ciki, daga gefenshi kuma radunanane guda uku shaƙe da ruwa, sai buta ɗaya da suka ajjiye mun sabida ban ɗakin waje. Kunji Amarya da gyaran gidanta da kanta ko? Tsakar gidan yayi mugun dattine, bafa ƙaramin tururuwar zuwa ganin ɗakina aka dinga yi ba. Shima wannan ya taka muhimmiyar rawa a zaman jama'are gaskiya. Ina sauke naman na ɗaura ruwan wanka kana na turare ko'ina da turaren wutana irinna mrs Bukhari turaren wuta ɗan gaske wanda sai dai kace tsada ba dai rashin riƙe ɗaki da musulmin tattausan ƙamshi ba, kuma dama abu mai kyau da nagarta yana da tsada sosai. Ƙamshi wani babban sirrine na ma'aurata sosai macen da tasan kanta dole a ganta da humrori da turaren wuta na gasken ba wannan itace da ruwan banzan ba. Wanka nayi na sallaci azahar. Sai murmushi ke kubce mini wallahi har sanda nake sallar. Sabida murna ji nake zuchiyata kamar zata fatso ta fito Ina kan sallaya ina jan carbi naji anata doka ƙofar ɓarayina da sauri na cire hijabina na fito na caɓa ado nasa sabuwar atampa mai tsadar gaske na sha ɗauri ga ƙamshin Humrori ina bazawa. Ina zare sakata naga wai matan maƙotane da basu samu shigowa ganin ɗaki ba suka shigo kusan su bakwai ko wacce da goyo kamar haɗin baki, sun dame da ƙazanta wani ƙarni_ƙarnin Mama suke yi dake masu shayarwane. "Amarya munzo ganin wajene dama a tsanake maƙotankune, lokacin da ake tururuwar mu bamu zo ba, mun fi son mu zo a tsanake mu kashe ƙwarƙwatar idanunmu" Murmushi nayi musu tare da musu iso har ciki duk suka lalleƙa suna santin waje, tare da labarai iri da kala. Na ƙolla musu kayan garar fulawa sukai mun sallama Na bisu zan rufe ƙofa kenan aka aiko yara da kwanon abinci wai ya kawo mini. Nasa hannu na karɓa dama yinwa nake ji sosai gashi kayan fulawar ko son ganinsu banayi na kasa ci gashi jingim kuma. Ina shiga na buɗe kwanon. Taliyar hausa na gani a cikin ruwan manja tana iyo. Rufewa nayi nayi jigum wallahi bazan taɓa iya ci ba gashi yinwa nake ji, zuchiyata take ta soma tashi ma. Agogo na kalla biyu har ta gota ai saina miƙe na shiga Kitchen na fita da turmina waje na ɗauki roba da wuƙa na fita. Jajjayen kayan miya nayi na koma ciki na tsaida sanwar shinkafa jallof gongoni uku na wadatata da nama da maggi mai star, ga jajjagen yaji tafannuwa nan da nan gida ya ɗauki ƙamshi, ina cikin girkinnan naji ana wani irin bubbuga ƙofa kamar za'a cire mun ita. Fita nayi na buɗe ƙofar Inna Ladi kishiyar Nanno nagani. "Hindu kece kika ɗaura girkine gida ya karaɗe da ƙamshi? " Murmushi nayi nace. Eh wallahi nice na ɗan ɗaura sanwa" "Wa yace miki mu haka muke yi wannan wacce iriyar fitsarace yau daga watsewar ƴan biki miji bai ko shiga ɗakinki ba zaki nuna rashin kunyarki da zumuɗinki akan bainar idanun surukai? Lallai mijinyawa da jajawur ɗin aiki a gabanshi. Ki jini kada ki sake ɗaura ko ruwan shayine in ba sati guda kika yi a gidannan ba. Mu ba haka muke yi ba gida duk ya ɗau magana. Haka akeyi yau ɗinnan biki ya watse fa amman sabida ƴan boko ku dama baku da ta ido shine har ƙamshi ya karaɗe gida" Tana dasa aya ta wuce fuu. Ni kuma nayi tsaye kawai illahirin mamaki ya cika ni. Nasan amarya bata girki saita kwana bakwai amman babu laifi a ciki danta ɗaura girkinta. Lallai dole saina kiyaye sha'anin ƙauyawa abun azimun ne zama da sirikan kenan takura da saka idanun tsiya. Komawa ciki nayi na sauke abincina na zuba a kwano naci na sha ruwa abina. Ina zaune ƙwalam har bayan isha duhu ya rufa sosai na kunna acibalbal ɗin da tunda muka zo aka bamu na ɗaura a saman alkuki. Kafin magriba na shiga da kayan miya da wannan naman kai cikin ɗakin dake kusa da namu. Ina jiyo hayaniyar abokan mijinyawa Babba da suka rako ango amman ni sai wajajen sha ɗayan dare Gawata ya shigo da abokanshi hannun Qasimu riƙe da leda ƙarama ta jiƙe da mai Abdulƙadiri kuma yana riƙe da hannun Ango. Nan aka gaggaisa dai suna nuna farin cikinsu da ganin wannan rana suka ɗaura da yi mana nasihu, kana sukai mana sallama suka fita. Ɗagowa nayi muka soma kallon ƙuda ni da Gawata da naga yayi wani irin kyau na musamman. Murmushi muka sakarma juna ya riƙe hannayena biyu a cikin nashi. A karon farko da wani namiji da ba ɗan gidanmu ba kenan daya riƙe mun hannuna. "Tutar so tunda kika mun irin wannan sadaukarwar kika baro birni kika biyoni ƙauyanmu ni kuma zan zame miki garkuwa bango abun jinginar rayuwarki, na yadda in ƙuntata ke ki samu farin ciki. Nayi miki alƙawari duk daren daɗewa zan mayar dake Kano mu rayu acan tare da yaranmu in sha Allah su samu karatu mai kyau ginanne kuma. Nafi ko wanne namiji sa'ar mace a rayuwata. Kin fi ƙarfin in haɗaki da wata mace ko da ana ha maza ha mata ke kaɗaice tilo a gidan Gawata daga ke babu ƙari" Sai yayi shiru ya sauke kanshi ƙasa me yake tunawa oho ban sani ba. Sai na katse shirun ta hanyar cewa. Mu godema Allah daya ƙaddara wannan auren duk da iyayena
Chapter 49 · 0% Book details