← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 77

Sashe 64

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

faɗa miki har an fidda anko an shiga shirye_shirye ka'in da na'in" Ahh kice Allah yayi Sanusi ya doke duk manemanki? Gaskiya na taya ki murna sosai ashe dawowa biki nan da wata huɗu ya kamani Luba Allah dai ya nuna mana lokacin. Kuma a garin nasu zaku zauna ko nan Kano?" "To har yanzu bamu sani ba yana dai ta fafutukar hakan to iyayenshi sunfi son ya zauna acan amman duk inda ta faɗi sha ne Hinduwa, nima fa ƴar ƙunar baƙin waken ce" Muna cikin hirar mu su Akarami suka dawo sallah har da Qazzafi aka shigo duk muka gaggaisa suka tambayeni mai gidan nawa. Innarmu ce ta leƙo ta kirawo Luba ta shigo ma dasu Akarami abincinsu ta ɗakko mana namu muma muna ci anata hira duka Innarmu dai babu zama tana can kula da miji. Luba sai bayan isha ta tafi lokacin ƴan matan ɗakin namu sun dawo suna ganina suka soma murna nan aka shiga hirar yaushe gamo. Gida mai daɗi yau nayi baccin farin ciki a cikin ƴan uwana na wayi gari cikin gatana gaba da baya. Ƴar tsarabar albasa dana kawo Innarmu ta karkasa, ta haɗa da sabulun wanki mai ƙamshi dan dai a fita kunya. Ni na dinga shiga ina kaiwa ina gaisawa da iyayenmu maza sai in bada albasar da sabulun, haka har maƙotanmu kaf Innarmu tasa na rabar da albasar a hakanma bata isaba ko su Yaya Saratu bata ajjiyema ba. Muna kan suyar masa ni da Innarmu muna hira tana tambayata yanayin zaman namu da yanayin jikin nawa sai ga su Yaya Saratu tana murna yau a motarta da mijinta ya canja ya bar mata tsohuwar tazo. Haka muka ɗunguma muka fita sanya alkhairi dukka gidan, masu murna da masu baƙin ciki dai. Daga haka kullum sai sunzo gida mun shiga kasuwa siyayyar abubuwan biki ana saura kwana biyu biki gidan ya ɗinke tam da baƙin nesa harma dana kusan. Sun sha mamakin yadda na tawo da ankona, kuma na lale kuɗi na ba Innarmu kuɗin lesiri ta bani. washegari aka shiga biki. Mune har Kaduna kai lefe sabida matar Akarami ƴar Kaduna ce kasanxewar a Jaji yake aikinshi dalilin haɗuwar kenan itama wanta soja ne abokin Akaraminne. Sun mana tarba ta girma da ƙarya sosai. Muma mun nuna bajinta da harkar girma a lefe sosai sukai mana tukuice mai tsofar da saida mukai mamaki, na fahimci Kaduna suna da ƙarya da son girmama sha'ani dan biki sosai suka haɗa na tarbar lefen kuma basu bamu shinkafa ba sai kayan fulawa da soyayyun kaji da ruwan gora da abun sha na kwalba kiret biyu. Muka kamo hanya muna jinjina girma da karamcin mutan kaduna. Sai magriba muka dawo a lokacin za'a tafi kai kayan lefen Qazzafi dasu Babawon lungun Baba Lukumanu, ai sai juyawa muka yi aka sake wucewa kai lefennan na samari uku. Ragowar an riga an tafi kaiwa amman ba'a dawo ba. Bamu muka dawo ba sai wajen sha ɗayan dare muka dawo tulus ni dai ina kwanciya sai bacci. Washegari innarmu ta miƙo mun dubu talatin tace kasonane na kuɗaɗen salalar lefen da muka kakkai shine aka kididdiba aka raba kowa abinda ya samu kenan. Nasa hannu nayi godiya na adana abuna. Ranar ɗaurin Aure muka saka atampar da muka fitar a ɗakinmu ai kuwa mun ɗauki magana sai cece kuce akeyi a cikin gida, ko wanne ɗaki fa sunyi nasu amman namu shine mafi tsada kuma sun san ƙa'idane mu ƴan ɗakinmu komai muna nuna mu mune wannan a haka Innarmu ta ɗoramu akai, shi yasa duk abu in ba mai tsada bane bai fiye damunmu ba. Daga cikin iyaye aka wakilta suka wuce kaduna ɗaukar Amarya zuwa barikin sojoji dake cikin Jaji. Mu kuma muka wuce aka ɗakko matar Qazzafi zuwa gidan daya kama A Ɗorayi duk da ance inya tashi tafiya zai wuce da'itane. Masha Allah gidan na zaman mutum ɗayane, kuma iyayenta sun kwankwatsa mata kaya sosai babu laifi, wajajen goman dare Yaya Saratu ta tuƙomu muka wuce gida a motarta. Washegari kuma muka wuce wuni a barikin sojoji jaji gidan Yaya Akarami. Ranar muka saka leshinmu muka fito shar damu, itama danginta da ƙawayenta duk leshi suka daka masu tsada. An sha wuni anci an sha wajajen ukun yamman muka baro bariki zuwa gidan ƙawar Innah Yahanasu dake malali anan muka kwana washegari muka koma gidan Amarya da safe wajajen goman safe a lokacin Akarami ango yana gidan jiyan aka rakoshi bayan isha. Su Innah Yahanasu suka haɗasu sukai musu nasiha muka ga waje a tsanake sannan Akarami ya dafo mana shayi da wainar ƙwai muka sake karyawa,sannan fa muka ɗauki hanyar gida. Biki ya ƙare ƴan nesa sun kokkoma mu kuma muka ɗauki haramar tafiya Maiduguri. Ranar da zamu tafi Baba Sojanmu ya titsiyeni da batun komawa makarantata. Ta inda yake shiga wallahi ba tanan yake fita ba. Tsabaragen faɗa har hunhuna yake yi. Saida na sanar dashi ma ai na soma koyarwa a sakandare ne fa ya sassauta mun, na bashi haƙuri sosai kafin muka wuce. Nanma anyi biki sosai na manya an kashe nera satinmu biyu muka dawo kano na kuma yin sati guda ya kama sati huɗu kenan na hau haramar komawa gida kuma. Kafin na tafi saida muka sake gazaye gidan angwaye, na yi sabon kitso na sabunta ƙunshina dake lallaɓe nake yi ba mai fulawa ba. Innarmu ta harhaɗamun tsaraba sosai harda su garin tuwo da shinkafa, dasu man shanu da kifi bushasshe da mukai guzirinshi da yawa daga Maiduguri, banda wanda aka babbamu tsaraba, muma ko wacce ta cire kuɗinta ta siya, da komai na abinci saida ta ɗibamun tace nayi tsaraba dashi Baba Sojanmu yace aimun miya ya siyo kaji biyu Innarmu tayi mun miya nice harda kuma yin cincin na ƙara akan wanda na tattara na biki, ana gobe zan tafi na shiga kasuwa na siyo abubuwan da nake da buƙata, su Yaya Saratu yaji ta dakamun ta bani dubu goma, Yaya Zubaina kuma kuɗi ta bani da dambun nama tace naita ci a hanya, Jinjin kuɗi ta bani, Fulawa na siya na ba Innar su Luba taimun Gurasa mai gishiri da mai sikari ta kwano biyu dama sana'arta kenan Ranar talata sassafe nayi sallama da Kano muka ɗauki hanyar Bauchin yakubu. Da misalin ƙarfe shiddan yamma Acaɓa ya saukeni a ƙofar gida da akwatina da buhun kayan tsaraba rigi_rigi. Mijinyawa yana zaune a kututturen dake ƙofar gida yayi tagumi, duniya tayi mishi ɗaurin lemar minti, ganina ne yasa ya miƙe da sauri ya taya mai acaɓa suka sauke buhun kayan tsarabar garin tuwo kamar ya fashe a cikin buhun ma dan harya soma zuba. "Taimaka mu shigar ciki kawai bawan Allah" Cewar Mijinyawa, tare suka shiga ni kuma na biyosu da akwatina a baya da sallama a bakina na shigo cikin gidan. Duk suna tsakar gidan sai bina da ido suke. Ana washe mun baki na bogi. Ɗakin Nanno na wuce da sallamata su Inna Ladi suna zazzaune a tsakar gida. "Tica uwar karatu yanzu kike tafe kenan? Sunan da suka dawo ce mun kenan. Wallahi kuwa innah na sameku lafiya? " "Ahh lafiya lau ya kika baro angwaye da iyayen naki? " Duk suna lafiya sunce a gaisheku ma" Muka gama gaisawa nasa ƙafa da sallama na shiga ɗakin Nanno Uwatale tana bakin gado a zaune tana ba jaririyarta nono sunyi kyau uwatale tayi ƙiba sosai. Kallonta nayi da jaririyar suka bani sha'awa sosai ko ni sai yaushe zanga nawa ɗan ko ƴar oho wata Tara da Aure. Nanno na zaune tana kaɗin lagwani Uwatale mai jego masha Allah mai muka samu ne kawota" "Baki ga Mama take sha ba ai kya bari inta ƙoshi sai ki karɓeta" Nanno ta tsinkani ba shiri naji wani abu ya tsargamun. Zama nayi muka gaisa da Nanno uwatale ko kallona bata yi ba gudun kar in shareta ace ina baƙin ciki shi yasa nace. Uwatale ina wuni kin sauka lafiya? " Kunga yadda tayi da baki kuwa tace. "Lafiya ya kika baro ƴan gidanku? " Lafiya sunce a gaisheku. Nanno bari in shiga in huta" Na miƙe nayi tafiyata, ko ƴar ban tsaya ɗauka ba. Tozali da nayi da mijinyawa a tsakar gida ya ciro kayan buhun ya adanasu a ɗakin shirgi yana juye garin tuwon daya zube a buhu a cikin bawo, ya sanyaya ruhina. Wani kallo yayi mun mai fassarori da dama. Murmushi na sakar mishi na ƙarasa kusa dashi ya damƙe hannuna muka lumshe idanu. "Tutar so ashe zaki iya irin wannan daɗewar ba tare da kin duba wanne hali ni zan shiga ba? Sati huɗu fa" Sai kunya ta kamani Ai kuwa da daddare na yadda mijinyawa yayi kewata sosai sau uku ya neme ni duk da ba wannan bane na farko ba amman da wannan daren ya bambanta sosai. Washegari dashi muka kunce tsaraba ina mishi bayani tsarabar yana taya ni muna juye kayan hatsin a robobin da muke adana kayan abinci. Tare muka ƙulla cincin da gurasa muka bama matan gida da tsirarin maƙota. Sai da muka je gaishe da Nanno na samu aka bani Zainab na ɗauketa nayi shiru ina kallonta amman a ƙasan zuchiyata inajin ni sai yaushe zan rungumi nawa ɗan ko ƴar, yaushe ma ciki zai shiga cikin marata ya kwanta, ko dai juyar ce da gaske? Mijinyawane ya katsemun tunanin nawa ta hanyar karɓar Zainab ya riƙeta yana jijjigata ni kuma sai kallonsu nake yi ina jin sha'awarsu. Sai abun ya tasirantu sosai a zuchiyata. Wasa_wasa sai rashin haihuwa ya soma damuna ainun kullum cikin tunani nake. Sai ciwona ya soma takuramun gashi a lokacin kusan da koyarwar da nake yi muka dogara nike yin komai a gidan har murjin taliyar hausa ake kawo mun na kuɗi inayi ina ɗan samun kuɗin shiga. Mijinyawa ba wai zama yayi ba dole ya haƙuri da sana'ar shayi ya shiga bin su Qasimu, dubu Ashirin na kuma dunƙula na bashi, yana duk abinda ya samu wahala dai ana shanta babu wadataccen kuɗi sai yayi wata guda a wani ƙauyen ko cikin Bauchi inya tashi dawowa baya dawowa da wani abu mai yawa kuɗin da yake dawo dashi baya isata inci abinci na wata in an haɗa harda kuɗin albashina to a ciki nake siyan itace,
Chapter 64 · 0% Book details