← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 77

Sashe 19

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

muke rayuwarmu mai tsabta kafin ya shigo da wannan bidi'ar. Yayi rikici sosai yayi rarrashin duniyan,damma ban biye mishi ba. Zuchiya ma yayi ya koma ɗakinshi nima na kulle ɗakina nayi kwanciyata. Sabida samun waje har ƙorafi kake yi akan mota da cefane sabida na wawantar da kaina ka ɗauka bansan me nake yi bane? Ai baka ga komai ba inka gaji sai ka ɗauki matakin duk da kake ganin shi ya dace aikin banza. Washegari kafin bakwai Asama'u tazo tace mun zasu wuce har gaban motar Mijinyawa Babba muka rakasu ni da yara. Mijinyawa yana gaban mota ashe dashi za'aje. Ni dai nayi musu Allah ya tsare hanya na ɗakko dubu biyar na damƙama Nanno nayi wucewata. Sai naji gidan yayi mun sarari sosai. Mijinyawa bai dawo ba saida ya kwana uku, ko sau ɗaya bai kirani a waya ba. Sai ranar da zai dawo a ranar ni kuma ina wajen aikina cike da farincikin kwantiragin da Bbc landan ta ɗaukeni suka ji suna son suyi aiki dani na shekara biyu kuma gidan rediyon kano masu karamci basu yi mun baƙin ciki ba tuni suka amince, gashi a yau ɗin ake sanar dani an maidani ɓangaren masu ɗauko rahoto wato rifota kenan aikin dana fi ƙauna a aikin jsrida kenan. Na ƙudurce a raina ko a gidanmu bazan sanar ba har sai lokacin tafiyata landan yayi tukunna. Ina cikin wannan murnar naita ganin kiran Mijinyawa wallahi nayi funfuruncus naƙi ɗauka daga gidan Rediyo ma madadin in dawo gida wallahi sai naƙi nayi wucewata gidan Yaya Saratu dan in wanke ƙuncin zuchiyata. Gidanta ita kaɗaice da yaranta takwas duk sun girma Autanta ma shekara sha uku. Tana zaune tana kallon tashar Arewa 24 ta jiyo sallamata. "Tabb yau kune a gari inji maƙi baƙo? Ban kuma daɗe da dawowa daga gida ba Inna Turai dai na barota tana naƙuda. Abinda yasa na dawo Baban Nafisane ya kirani yana hanya shi yasa kika ganni na dawo yanzunnan na gama girki shine na zauna" Zama nayi ina cire mayafina. Ahh kice yau amarya ce ke, banji turaren wuta na tashin ƙamshi ba, sai ƙamshin kaza" "Tukunna dai ai sai nan da awa biyu ko uku ma zai dawo, zo mu shige ma daga ciki" Miƙewa nayi muka shige ciki yaran duk basanan. Zama nayi a gadonta nayi dirshan. "Ina zuwa bari in ɗebo kayan ɗa'a in dama na damawa, kinsan fa ba wasa sai da tada komaɗa" Fita tayi muna dariya sai gata da kayan ɗa'a cikin basket Na Surayya Dee marubuciyar Halin yau. Su sanyi fuloshane, harda gimbiyar zabuwa a dafe cikin tsabta da ganin komai kasan cikin nagarta da ilimi aka haɗashi. Ga nasu garine dana ruwa duka dai. (08032773332) Duk mai so ya tuntuɓi Surayya Dee kai tsaye zaku dawo ku gode mun. Taita damawa tana sha, tana bani ina kaucewa sabida ai nima ina amfani da kayan matan Surayya Dee kuma nasan nagartarsu da ingancinsu bazan taɓa sha ina kan wannan ƙadamin ba. Ke dai kisha ni kinsan ina da nawa bani na haɗaki da Surayya Dee ɗinba ma. Amman sabida Allah saida miji yana hanya zaki soma shan magani shi da akeso kamar saura sati guda sai kasha yabi jikinka ai yafi aiki ma" "Ke nafa shassha wannan ƙarine fa sanyi fulosha ma da shan lemo nake yi mishi tsabar yadda yake fatattakar sanyi. Hinduwa ai dole in dage insha magani in gyara jikina har dilka duka nayi wanda na siya a wajen Mrs Bukhari sirrin gyaran jikin matan Sudan, na matsi duk nayi amfani dashi shima na wajen Surayya Dee ɗinne. Ni so nake yi ma inje aimun ɗinki a ɗinkeni gam wallahi. Nace. Ai kuwa akwai wacce na sani ta'iya sosai nata gashi da saurin warkewa kuma tasan aikinta sosai, duk da ban taɓa yi ba ta dai taɓa yima Luba kuma ta yaba sosai." "Allah sarki saida kika ce luba na tuno mijinta yayi auren ko? " Hmmm yayi aure munje mun yi biki. In banda sha'anin maza sai su baki ga amaryar ba babu wayewa sam sakandare kaɗai ta gama. Na dai siya mata kayan mata basket guda na Uwargida a hannun Surayya Dee tana kan gyara kanta zuwa lokacin da Allah zai sa miji ya waiwayo kanta" Muna cikin hirarmu muka jiyo kiran Innarmu a wayar Yaya Saratu wai Inna Turai ta haihu ɗa namiji. Mun jima sosai muna hira sai dab magriba na wuce lokacin Baban Nafisa ya faɗa mata ya shigo kano. Bani na isa gida ba sai bayan magriba. Ai kuwa a falo na samu Mijinyawa ya cika yayi fam kamar zai fashe. Yarane sukai mun sannu da zuwa na amsa musu, Abinci Azgar ya kawo mun ko wanne ya nufi ɗakinshi. Sannu da dawowa ashe yau zaka dawo ka baro su lafiya? " Wani mugun kallo yayi mun. "Daga ina kike kuma baki ga kiran wayata bane? " Daga gidan Yaya Saratu nake bayan na baro wajen aiki. Kiranka kuma ban gani ba" Ai sai ya miƙe ya soma nuna ni da yatsa. "Ke bari kiji bazan ɗauki wannan sauye_sauyen da kika ɓullo mun dashi ba. Na fahimci sauƙin kaina yasa kin soma rainani. Wallahi idan kika yi wasa aikinma ajjiyewa zaki yi tunda nina biya miki kuɗin makarantar kuma ina da ikon hanaki zuwa. Na lura a wajen aikin ku ake zigaki. Ya kike nema ki kassaramun kuzarina Hindu kin hana ma zuchiyata salama, na roƙeki da girman Allah ki sanar dani me nayi miki ni mai baki haƙurine kema kin sani. Amman kin ƙi sai lulluɓeni baibai kike yi" Dariya ma ni wallahi ya bani yadda yake haƙilo akan ɗan canjawata. Au ashe duk abubuwan da nake yi muhimmaine kuma anaso duk wata mace ta yisu? Maza kenan nasan kunanan wasu na ganin wautata kuna ganin tamkar bazan ɗauki mataki ba ko? Mataki da hukunci sunanan tafe kubi karatun cikin nutsuwa karatune na nazari bana zallan nishaɗi ba. Hmmm mijinyawa duk abinda ka faɗa gaskiya ne. Kai ka biya mun kuɗin makaranta badan a gidanmu ba zasu iya biya mun ba. Aiki kuma a gidanmu aka nema mun, aikinnan babu abinda bai yi maka ba. Aikina yana da mahimmancin da babu abinda zaisa in barshi wallahi idan sama da ƙasa haɗewa zata yi aikina yana hannuna babu gudu babu ja da baya. Babu shakka ashe ka'iya gori har ƙwaƙwalwarka ta iya tuno maka kai ka biya kuɗaɗen karatuna ashe?" Abincina na ɗauka na shige ɗakina na yi zamana a kan gado. Sai gashi ya biyo ni waje ya samu ya zauna na lura jikinshine yayi sanyi. Banyi niyyar cin tuwon ba amman naita turawa ina haɗiyewa dan in cusguna mishi. "Tutar so" Ya kirayi sunana da murya mai kauri. Bai jira na amsa ba babu buƙatar hakan yasan bazan taɓa amsawa ba. "Ba haka kika saba yi mun ba. A baya ni ɗan gatankine wanda kike gatantawa ta fannoni daban_daban ta fannin abinci, ta fannin mu'amalar aure, ta fanni kulawa dani, da gidan baki ɗaya. Ki duba rayuwar da muke gudanarwa mai kyau, a baya kaɗan har guje_guje muke yi da juna musamman ranakun hutu. Asabar da lahadi kuwa muna fita da daddare muci abinci a waje tare da yara ayi nishaɗi. Amman tunda na dawo daga asibiti ba'a sake yin wannan ba. Bakya zuwa ɗakina kona kwana a naki ɗakin babu ko hira a tsakaninmu, dan Allah me nayi miki ki sanar dani mu haɗu mu gyara rayuwar gidanmu tayi kyau. Duk kin rikirkitamun lissafina yana neman kwancewa duk wanda ya kalleni yasan ina da damuwa, ni tsorona kada su Azgar su gane halin da gidan yake ciki" Shiru yayi yana saurarena Bada ban ina duba abubuwa da yawa ba ai da wani labarin akeyi ba wannan ba. Mijinyawa nace maka babu komai yanayin rayuwane kawai. Ai dama ba zamu taɓa dauwama a haka ba inta riritaka ina tarairayarka kamar dan kai nazo duniyar ba. Wannan duniyar Allah ya haliccemune domin mu bauta mishi" Miƙewa nayi na shige banɗaki na wanko hannuna da bakina na fito. Ban ganshi ba amman nasan masallaci ya tafi. Ko da ya dawo bai shigo ba, ni kuwa harna garƙame dama ɗakina. Da safe dake ranar asabarne sai ƙarfe takwas na fito fes dani nayi wanka na saka atampa riga da siket. Naga falon babu kowa amman Sabira ta gyare ko'ina sai ƙamshin Halud lamba wan na mrs Bukhari yake tashi. Na jiyo muryoyinsu a Kitchen saina nufi can. Hmm mijinyawa yana gabas gas kuka yana ta aikin suyar doya ga miyar ƙwai sai dahuwa take yi.. Azgar kuma yana haɗa kofuna da filet da zai fita dasu. "Kin tashi barka da fitowa, kije falo kiyi zamanki Tutar so yanzu zan kammala in fito, kiyi sarautarki yadda kike so, takawarki lafiya" Kai na gyaɗa kawai yaran duk muka gaisa na fita. Laptob ɗina yana kan cinyata ina duba asament ɗin farko da aka bani monday zanje wani taron ƴan siyasa in ɗakko rahoto su suka turo da gayyatarma da kansu. To bayanai nake karantawa suka fito tare da dure komai a gabana. Dani mijinyawa ya soma, nasa hannu na karɓa. Nagode" Nace dashi, naci doyata da miyar ƙwai na kora da shayi, yanata jana da hira, ina amsawa a taƙaice kuma babu fushi, ko ɓacin rai bare damuwa tattare dani sam, abinda yafi komai ɗaure kai kenan. Da naga tara tayi nace dashi. Zani gida Inna Turai ta haihu zanje" Baki ya washe. "Me muka samu, yaushe ta haihu? " Namiji, jiya ta haihu." Mayafina da jakata na shiga na ɗakko takalmina na hannu na fito. Naso in tafi da yaran duka, Azgar yace mun karatu yake so yayi saina barshi Sabira kuma ta bini muka je. Haka mukaita sintirin zuwa gida har ranar suna. Asament ɗina na farko na gane aikin rahoto ga ɗiya mace aikine mai ƙalubale ainun, hakan naba mace damar shiga maza, sanin manyan mutane, shiga inda batai tunani ba, da shiga inda baima dace ace tana mace ta shiga ba, tsaiwa a wajen da batai zato ba, tambayoyi ga wanda bata taɓa tunanin zasu haɗu ba. Taron ƴan siyasa na farko da naje ɗakko rahoto ƴan jarida da gidajen tv da rediyo sun halarci taron sosai. Amman mu biyu ne mata a masu ɗaukar rahoto
Chapter 19 · 0% Book details