Sashe 27
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
bala'in da zai faɗa kenan da ya barma mahaifiyarta riƙonta ya ɗauki nauyin komansu kawai. Saiya tuno sanda ita kanta mahaifiyar Asama'un data matsa akan ya Aureta ya kare mutuncin iyalin marigayi Amininshi. A lokacin ya nuna ma Hindu har taita mamaki ƙarfin halinta dan wannan shi yai sanadiyyar rugujewar zumuncinsu ma, tayi naci sosai har Allah ya ɓullo mata da miji da dai taga mijinyawa yaƙi karɓarta saita haƙura tayi aurenta tana gidan wani tanata hayayyafa abunta. Yau gashi ya lalata Asama'u ya kuma yi Auren cin Amanar Hindu, yanzune ya samu zarafin yin nazari harya gane girman cin Amanar da yayi ma Hindu, damma tana da dagiya da ƙi faɗi yasan da tuni zuchiyarta ta buga. Shi a halin yanzu tsoronshi Allah, tsoronshi rabuwa da Hindu bazaima iyaba sam. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da yake ji anata ta faman yi Qasimu bai jira an bashi izini ba ya kutsa kanshi, sai dai a irin yanayin daya riske Aminin nashi tabbas yasan akwai matsala. Kafaɗarshi ya dafa suka ƙurama junansu idanu. "Nasan dole za'a samu matsala Gawata. Bari kaji tunda dai Nanno ta shiga rabon alawa da goro na gayyatar biki Baraka matata babu irin kukan da bata yi ba. Gawata har zaginka Baraka saida tayi burki na taka mata, ta haukace kamar dai ita za'aima kishiya. Bafa auren bane matsalaba, ba kuma ca akwai kar kayi auren ba. Amman ka rasa wacce zaka Aura sai ɗiyarmu yarinyar da a babi na dattijantaka ko kai da'ita kuka rage saidai ku kalli juna kamar yadda zaka yi in ku biyu kuka rage a duniya kaida Sabira. Hindu mutum ce da rabin mutum jibi rayuwar da kuka gudanar a ƙauyannan shekara sama da ashirin baya jama'are ta jiya bata yau ba fa data samu ci gaba sosai. A rasa dame za'a saka mata sai auren yarinyar da mamane kaɗai bata bata ba. Ba'a duba ma Hindu ba sam, baka duba ba Gawata" Idanu mijinyawa ya lumshe kanshi na wani irin tururi. "Qasimu nayi wauta na tabka babban kuskuren da ba lallai in wanku a idanun Hindu ba abadan. Kai abokinane ko mutum na kashe zan faɗama nasan zaka taya ni birneshi. Qasimu kafin in Auri Asama'u saida muka gama lalube junanmu zinace kaɗai bamu aikata ba. Ashe Hindu tasan komai bayan ɗaurin aure duk ta turo mun komai a wayata" Shirune ya biyo baya na lokaci mai tsayi. Da ƙyar Qasimu ya ja hannun Mijinyawa suka zauna a saman kujera duk sukai tagumi, sai can yace. "Gawata ka kwafsa ma Hindu ka ɓarar da kimarka, mutumcinka abadan. Lallai baka da abinda zaka iya wanke kanka ko sakin Asama'u kayi, kayi a banza wai man kare. Me ya shigeka Gawata tunda nasan soyayyar shan minti ba naka bane ba halinka bane wannan zan iya shaidarka a ko'ina to ya akayi ita Hindu ta mallaki komai? " "Wallahi ban sani ba Qasimu. Nifa yanzu komai ya fice mun akaina bazan iya zaman aure da Asama'u ba, illahirin kunya nake ji. Asama'u ita ta ribaceni ta ja hannuna zuwa wannan. Qasimu daba dan na kai zuchiyata nesa ba da yarinyarnan tasa na aikata zina da'ita" Idanu Qasimu ya runtse yace. "Ashsha Gawata ashsha ni yanzu wallahi damuwata da wanne idanu za'a kalli Hindu ne kawai. Amman da idanun cin amanar zamu kalleta mu bata haƙuri amman fa ina da tabbacin ba zata taɓa haƙura ba" Mijinyawa yace. "Ko da na rabu da Asama'un? " "Ko da ka rabu da'ita. Kasan mata suna da yafiya amman basa mantuwa. Bazan ɓoye maka ba ni kaina haushinka nake ji Gawata ji nake kamar a busa ƙaho kamar zai iya fin sauƙi a wajenka. Kuma in ka rabu da Asama'u ka tanadi abinda zaka ce da Nanno ne akan dalilin sakin, da su Yaya Jamila da basu ƙi su ingiza Hindu wuta ba? Kada ma ka soma sake kwaɓa wani abun. Amman ina mai tabbatar maka ba lallai muje mu samu Hindu a gidanka bama tunda kaga ta turo maka saƙwannin abinda kuka aikata mata, shikenan ka rasa Hindu mace mai karamci da ɗa'a. Yanzu daure mu je cikin abokanmu aci asha zamu san yadda zamu ɓullo ma matsalar. Ka tara jama'a kaine uban biki, dole ka daure" Mijinyawa turjewa yayi akan bazai fita ba, a sallami kowa kawai, shi bazai iya zama da Asama'u ba. "Gawata wannan duka aikin banza ne. Wallahi Hindu rabuwarku ma shine mutumcinka, ta bala'in yi maka da ƙauna. In kaci gaba da riƙe igiyar aurenma, rayuwar ta gama muku daɗi. Wacce macece zata kama irin wannan iskanci da abu ta kaza... Da kuka yi ta rufa maka asirinka ma. Wallahi ko Barakace misali ta kamani haka, wallahi Jama'are da kewayanta kab sai sunji mena aikata. Bata ƙara zama gidana." "Qasimu ni ya zanyi dan girman Allah. Taya zan wanke laifina a wajen Hindu. Da wacce siga ma zan sameta mu tattaunane Qasimu? Wallahi Hindu bata rageni da komai ta ɓarayin ɗakinmu ba. Asalima kullum tamkar sabunta kanta take yi. Ga wani ƙamshi na dindindin da take yi. Wallahi babban tashin hankalina baya wuce, yadda naita zagi gami da aibata albarkatun jikinta. Wallahi kuma abunda nake ta cewa ba gaskiya bane. Hindu cikakkiyar macece wacce tasan kanta a ta ko ta ina. Qasimu ba gaskiya nake ta faɗa ba. Kuma wallahi bansan me ya fusgeni nake ta wannan shirmen ba. Me yasa na biye ma Asama'u? " "Son zuchiya mana Gawata da rashin tsoron Allah subuhanahu wata ala. Yarinyar da tayi maka tayin wannan lamari babba. Ai kamata yayi taci na jaki, kuma kada ta wuce wata guda tim a aurar da'ita tunda dai an samu matsala. Amman dake ka zama ɗan babbar abu ta kazan.... Sai kawai ka biye ma kiɗan kukaita canja salo_salo na rawa. Tur wallahi ka bala'in bani kunya. Wallahi Hindu ba zata taɓa ma uziri ba, jarabawa kawai zamu yi" Qasimu kam ya sulle Mijinyawa soso harda sabili. Ya sake ɗora mishi damuwa mai tsananin gaske. Ganin damuwar tayi yawane yasa Qasimu ɗan sassautowa daga fishi mai tsananin daya shiga. Yaita bashi baki kuma. Haka dole Qasimu ya jashi suka koma gidanshi akaci gaba da gabatar da liyafar cin abinci. Ya gagara kiran Hindu a waya sam. Asama'u sai kiranshi take yi tare da tura mishi wasu irin saƙwannin batsa. Tare da fayyace mishi yadda take ɗoki da zumuɗin su kasance daren gobe tare. Ranar mijinyawa ya gane dare da tsawo yake dan da ƙyar garin Allah ya waye mishi Tunani, gami da namadar komai su suka aureshi, kokkone ya haɗe mishi da giya. Da ciwon kai ya tashi mai tsanani, ga zazzaɓi kau a jikinshi, tsokokin jikinshi da hantarshi har kaɗawa suke yi. Bazai iya rayuwa mai kyau babu Hindu a gefenshi ba. Abu ɗaya ke sake sassare mishi guiwa tare da tsittsinka mishi gaba, sanin sarai wacece Hindu mace mai tauri, da ra'ayin riƙau, da dagiya akan gaskiyarta. Ƙarfe takwas daidai aka gama loda jama'a a mota da kayan Amarya da Nanno dasu Yaya Jamila suka cajeshi kuɗaɗe masu kauri Haka aka tawo a jere motoci ƙananu huɗu guda biyu ta Mijinyawa da abokanshi, biyu kuma amarya da ƙawayen Amarya sai kuma bus babba da aka zubo dattijai da yaran mata gayya suka yi mai yawan gaske suka ɗauki hanya. Tunda aka kama hanya Mijinyawa dake kusa da Qasimu a zaune ya jingina bayanshi da jikin kujerar motar ya rufe idanunshi ba bacci yake yi ba asalima yana jin abokanshi suna hira masu cewa ya buɗe musu ƙofa suma zasu shiga neman Aure na biyu, sai masu ganin da dai ba Asama'u ya Aura ba. Sai kuma masu tunasar dasu ba haramun ya aikata ba nan suka raba kansu uku akaita musu ana dariya gami da ɗaga murya. Ango shi kuma babu abinda yake yi mishi daɗi mafita da makomar zaman lafiyarsu kaɗai yake hange. Ji yake yi yana jin nauyi da kunyar haɗuwa da Hindu fiye da kima, har wani tsoronta ke ratsa jikinshi. Fatanshi, burinshi Allah yasa ta yafe mishi, in taƙi baisan ina zai tsoma ranshi ba. Asama'u kam sun gama bazan taɓa iya riƙw igiyoyin aurenta ba tabbas. ƙirjinshi sai dokawa kawai yake yi fat_fat_fat. A haka Allah cikin ikonshi da buwayarshi suka shigo garin Kano da yamma, ruwa akeyi sosai a Kano damunar farko farko ce amman ruwan da ake makaɗawa kamar irin watan agusta ɗinnan tsakiyarshi watan marka_marka. A haka suka shiga cikin gidan kayan Amarya kam ba'a fito dasu ba suna cikin mota rufe ruf da tamfol. Su kan abokan ango da ango kasa fitowa a cikin ruwan suka yi. Dan ruwane ake makaɗawa mamakon gaske. Amma mata tuni suka fito sukai ciki a guje a cikin ruwan. Su kuwa saida ruwan ya tsaya cak wajajen magriba kana suka ɗunguma suka fito kai tsaye ɓarayin Hindu suka nufa.