← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 77

Sashe 7

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lalurar mijinyawa. "Babu damuwa Hindu ki nutsu ki kula dashi ai Mijinyawa gudane harda ɓari, Allah dai ya bashi lafiya" Hmmm Murmushin gefen baki nayi tare da yi mishi godiya mukai sallama. Asama'u ce ta shigo mun da shayi da soyayyar doya da miyar ƙwai. Kai na ɗaga mata dan lokacin na riga na kira wayar Baba Sojanmu harya ɗauka nagagga kiran mutane da yawa harda kiran Azgar. "Hinduwa ya jikin shi Mijinyawan? " Baba Sojanmu jikinshi Alhamdullahi yanzu ma nake shirin zuwa asibitin." "To shikenan muma yanzu muke kintsawa Akarami zai kawo mu tare da iyayen naki, sai munzo. Ko akwai wani abu da kike so a tawo miki dashi? " A_a bana buƙatar komai Baba Sojanmu" "Shikenan Hinduwa sai mun zo" Haka mukai sallama saida na fito wanka na kira Azgar ina karyawa. "Ammi kun tawo ne? " Tukunna nima banji daɗi bane amman nan da minti talatin zamu ƙaraso in sha Allah. Yaya jikin Abban naku ya farka kuwa? " "A_a bai farka ba yanzu ma cuku cukun shiga dashi ɗakin Tiyata akeyi shi yasa nake ta kiranki kizo kafin a shigar dashi" To shikenan Azgar gamunan zuwa" Na kashe wayar tare da karyawa a gurguje na kintsa na fito Asama'u na riƙe da basket. Wai saida matar Gambo da matar Ado suka gammu mun fito a tsakar gida dan kuturun wulaƙanci suke tambaya ya mai jiki. Da sauƙi mun gode" Na basu amsa a ɗaure nayi wucewata. Muna tafe ina tunane_tunanen da ni kaina bana iya tantance komai. So nake yi ƙwaƙwalwata ma ta huta amman ina sai tafasa take yi. Muna shiga ɗakin muka tarar ana ƙoƙarin jan gadon da Mijinyawa yake kai za'a wuce dashi ɗakin tiyata. Jikinshi ya kumbura sosai har fuskarshi da babu rauni saida ta kumbura suntun. Hannun Azgar na riƙe kawai. Mijinyawa Babba yace. "Hindu ayita adda'a dan Allah kuyi haƙuri da ganin idanunki baki samu bacci ba shi yasa ma baki zo da wuri ba" Kai kawai na ɗaga mishi bazan iya cewa uffan ba. Haka aka fice da Mijinyawa muka bisu har gaban ɗakin tiyatar sai dai sun umarcemu da mu koma bakin can babban ɗaki. Haka muka dawo Asama'u ta zuba musu kayan karyawa suna kan karyawa Su Baba Sojanmu suka iso shi da Inna Ruwayya wato Ruƙayya ake nufi da yaren Kanuri itace mahaifiyata. Doguwar baƙar kanuri mai gajeren hanci da zanen fashin goshi dogo, hancinta hagu da dama duk a ɓule suke ta saka barimar zinare a duka hudar biyu, gata da gashi, son gyara, ƙafarta kullum da baƙin lalle dan mu dai bamu taɓa ganin fararen tafukan hannayenta dana ƙafafunta ba. Inna Ruwayya ba kyakkyawa bace in kallo ɗaya zakayi mata. Amman tana da abubuwan da suka saka tafi Inna Abida kyau gashin da take dashi mai yawa, domin ko da yaushe tana faɗa mana gashi yana ɗaukar kaso hamsin bisa ɗari na kyau. To wannan gashi da salon kitsonsu na Kanuri ya fito mata da martabarta, haka zalika hujin hancinta ya haskata sosai, uwa uba laushin fatarta da sheƙin da fatar take yi shima wani abune. Muma duk ta ɓula mana hancinmu hagu da dama kuma tun muna yara ta maƙala mana zinare a hancin namu, hudar kunne kuwa huɗune damu a jejjere. Innarmu itace ta Biyu a wajen Baba Sojanmu yaranta goma cib, Shida mata huɗu maza, mazan ɗakinmu gabaki ɗayansu Sojojine. A ɗakin Inna Abida tana da Yahuza shine kaɗai soja. Sai inna Abida itace uwargidan Baba Sojanmu wacce akayi musu Auren zumunci iyayensu wa da ƙanine a gidansu Inna Abida Baba sojanmu ya girma Mahaifin Inna Abida shi ya saka shi a aikin Soja inna Abida da wannan take ƙafafa sosai. Inna Abida macece gajera mai ƙiba, gata da ido da hanci kamar biro. Yaranta goma sha huɗu cib. Bakwai maza bakwai mata. Sai Inna Turai itace Amaryar Baba Sojanmu, ita ba tsohuwa bace gata da kyau fara sol da'ita. Yaranta huɗu duka ƙananane babbar Ƴarta Tahira a js 2 take, ga cikin na biyar a jikinta goɗai_goɗai dasu. Gidanmu gidane na yawa da tarin al'umma da tarin matsallalun da sannu zaku gane kan gidan da ɗabi'un kowa. "Hindu, Mijinyawa Babba sannunku ya shi Mijinyawa da jikin? " Cewar Baba Sojanmu dake miƙa ma Mijinyawa Babba hannu. Duk da yaso nokewa saida Baba sojanmu ya bashi wannan hanu suka gaisa harda Azgar. Su Inna suka tsallako suka taddani akan tabarma harda abinci suka tawo niƙi_ niƙi Nan aka shiga gaishe_gaishe. Baba Sojanmu yana zaune a benci tare dasu Azgar. "Hinduwa to ki kaimu muje mu ganshi mana ko tunda abinda ya kawo mu kenan. Cewar Inna Abida tanaso ta ganshi sabida ta samu damar barbaɗa zance a cikin gida ba.. " Ai bama sai mun ganshi ba, a gabanki Akarami yake sanar mana ko sutura babu a jikinshi, ina ke ina kallon siriki a haka" Cewar Innarmu wacce Hausarta take a gurɓace da irin harshen garinsu. "Nima dai haka na gani, ni ɗakinma bazan iya shiga ba" Cewar Inna Turai da irin tata Hausar ta Fulanin usil. Basa ma ciki an shiga dashi ɗakin tiyata bamu san yaushe za'a fito dashi ba" Hakan yasa zancan baiyi tsawo ba. Masa da miya suka kawo mana masar da ita muka ci muka rayu duk kwanan duniya da safe ita muke ci, wasu suci da miya, wasu da sikari, wasu da ƙuli. Guda biyu Innarmu ta zuba mun bayan ta zuba ma Azgar da Mijinyawa Babba. Ban musa mata ba na karɓa na cinye. Sun ɗan jima isowar su Gambo da matansu ne yasa Baba sojanmu ya miƙe. "Mu zamu wuce Allah ya bashi lafiya ni da daddare zan dawo' Kuɗi ya ƙirga dubu ashirin ya ba Innarmu ta miƙo mun. Akarami ya bani dubu sha biyar, Innarmu ta bani dubu goma su Inna Abida sai taɓe baki kawai suke yi. Har wajen motarsu muka rakasu ni da Azgar da Asama'u da Baba Sojanmu yake ta tsokanarta tana dariya. Suna fita motar su Yaya Saratu ta shigo ƴan ɗakinnmu. Yaya Saratu, Yaya Zubaida, da Firdausi, Rayya, da Jinjin, nike bin Zubaida sauran duk ƙannena ne, Yaya Saratu kuma itace babba a ɗakinmu Obarol. ( Maman Twins gafa obarol ta mata kuma an samu) Sun tawo da abinci kula kula suna nan har aka fito da Mijinyawa daga tiyata aka dawo dashi ɗakin hutu, sai dai sun hana a shiga a duba shi. Azgar da Mijinyawa Babba tun safe suka tafi, mijinyawa aiki ya wuce, Azgar kuma wanka yaje yayo, sai ya tawo da Sabira wacce ta dawo daga makaranta. Wajajen azahar su Yaya Saratu suka tafi daidai lokacin Ƴan jama'are suka iso mata biyu da namiji guda. Inna Dubu itace kishiyar Nanno mahaifiyar mijinyawa, sai matar ƙanin Nanno Inna Duduwa, sai ƙanin mahaifinsu Mijinyawa Kawu Tanko. Cikin girmamawa da kame kaina na gaishesu tare da tambayarsu hanya, suka tambayi mai jiki na ce musu da sauƙi. Ban sake bi ta kansu ba, sunata hirarrakinsu a tsakankaninsu harsu Ikilima matar Gambo da Sajida matar Ado suka ƙaraso nan Inna Dubu ta shiga nannan dasu sune surukan arziki, ni kuwa ko a kwalar rigana bana neman yaddar kowa a da balle a yanzu da akayi walƙiyama halin Mijinyawa ya fito, badan albarkacin Ƴaƴa da bani da amsar da zan basu ba wallahi Allah da babu abinda zan sake takowa inyi a asibitinnan. To bana so kima da darajar Mijinyawa ta zube a idanun ƴaƴanshi da basu da tamkarshi, inna danne na daure ai zai dawo gida kuma abinda ya faru ya daɗe da faruwa ba gogewa zaiyi ba. Sannan bazan nuna damuwata ta yadda za'a gane logona ba sam Namiji bai isa yasa mun hawan jini ba sai dai in saka mishi ina dalilin da sai dai muita ƙona kanmu muna haska rayukan maza? Mijinyawa zan bashi mamaki wallahi zai girgiza da lamarina. Ƙarfe uku nayi Azgar da Asama'u sukai mana sallama suka wuce makaranta. Maƙotanmu na layi suka yo gungu guda suka tawo dubiya. Wajajen magriba aka bamu damar shiga duba Mijinyawa amman da ɗaya da ɗaya, a lokacin Mijinyawa Babba dasu Ado duk sun zo. Haka akaita shiga nice ta ƙarshe dana shiga Nayi shiru ina kallon fuskarshi ƙwaƙwalwa kuma na aikin ɗora mun bidiyonshi na tsaraici da irin sambatun da yake ma yarinya ƙarama a waya. Ya zubar da kima da duk darajarshi, nima ya zubarmun da daraja da kimata wacce har abada bana jin zata dawo wannan kimar. Maza basa tsoron Allah da tuntuntuni akan mutuwa. Allah ne fa yaso tunama Mijinyawa asirinshi dalilin ma da yasa yayi haɗarinnan kenan har wayarshi ta iso hannuna. To wai yanzu in bai farka ba ya mutu me zaije ya faɗama Allah? Jiya gashi da ƙarfinshi da lafiyarshi yau kuma gashi a kwance baisanma a duniya ko a lahira yake ba. Wannan ayace agaremu wallahi. A tsayen da nake na tuno wata baiwar Allah da take neman shawara a wajena tayi mun saƙon murya take faɗa mun irin zinace_zinacen da mijinta yake yi sai nace mata ta bani lokaci zanyi tunani akai kafin in bata shawara. Bana so kai tsaye ince ta kashe aurenta a samu matsala. Dan na fahimci mata zasu kawo maka ƙaran mijinsu yana cin zarafinsu ƙololuwa amman da zaran kace su haƙura da auren wata ba zata sake kulaka ba. Wata saita soma maka lissafin ita yaranta take ji, ko kuma kuji tana cewa adai duba a bata wata shawarar. Mijinyawa ya dawo ya sameni a ina nazari ya zauna a gefena. "Bani labarin damuwar dake shinfiɗe akan wannan Kanuriyar fuskar mai annuri da nagarta Tutar so." Murmushi nayi a kullum kalamanshi suna sanyaya mun ruhina tare da faɗaɗamun sadari na. Nan na bashi labari kaji_kaji abinda ke faruwa bani shawara in bata. Hmmm kunsan me yace?. "Duk macen data zauna da mazinaci jakace bata san ciwon kanta ba, bata son lafiyarta, kuma kice bata ma kanta adalciba inta zauna" Sai gashi yau na kamashi dumu _dumu da nuna ma mace tsaraici, anyi zinar, ba'aiba ban sani ba tunda ban gama bin chart ɗin ba. Sannan ba lallai a chart in samu tabbacin anyi zina ko ba'aiba. Amman ina da tabbacin sunyi zinar hannu, sunyi ta ido, sunyi zinar waya kuma. Mininyawa kenan wallahi idanunka sai yayi kiliya. Wucewa nayi
Chapter 7 · 0% Book details