Sashe 34
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Shekarun baya:.
Ina tsaye a ɗakin Innarmu sassafe saye da kayan makarantar Asiya bayaro. Ina gyara zaman hijabina. A lokacin ina SS2 kuma nice shugaba a ajinmu sabida ina da ƙwazo da hazaƙar karatu sosai. Duka yaran Baba sojanmu ba daga nan ba sabida duk dare in sha Allah saiya koya mana karatu tare damu da yaran gidan baki ɗaya harma da yaran maƙota da iyayensu suka zo suka roƙa musu.
Bikine damu na Ƴan mata goma a ɗakinmu akwai Yaya Saratu da Yaya Zubaida ɗakin Inna Abida Akwai Haula, akwai Mabaruka, sauran kuma daga ragowar lungunanne. A lokacin shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidanmu. An Aurar da maza guda biyar suma lokaci guda wannan shine Aure na biyu wanda iyayenmu mata suka ci buri ko wacce so take tayi ma ɗiyarta kayan ɗaki na bajinta da burgewa sosai. Mu kuma Ƴan matan gidan burin ko wacce shine saurayinta ya fito da'ita. Fargabata guda ɗaya ce ina Gawata zai samu kuɗin da zai fitar dani kunyar ankon da aka fitar har kala uku a gidannan, banda takalmi, kuɗin ɗinki mayafai, da sarƙa da duk zamu yi amfani dasu. Su Fatsiman Inna Abida da muke tsararrakun juna, da Aminan Inna Mairamu, da Khadijan Lungun Baba Nagoɗi duk samarinsu sun sallamesu da komai da komai harda kuɗin liƙi ƴan ashirin Ashirin. Saurayin Fhatsuma ma ya kawo, Inna Abida da kanta ta fito da kayan ta nuna a tsakar gida.
Rayya ce ta dafani tace.
"Yaya Hinduwa kizo Innah tana waje tana jiranmu tafiya zata yi in baki fito ba"
Jakata na rataya na fito falonmu riƙe da takalmina a hannuna sai a bakin ƙofa na saka na ratsa gidan namu muka fice.
A motar Innarmu Honda ladys kwaraɓaɓɓiya na tadda su Akarami da su Yaya Saratu a ciki, a lokacin suna jama'ar bayaro kano.
A cinyar Yaya Saratu na Zauna, Akarami ya ɗauki Rayya a gaba mu goma sha ɗaya ne cib a cikin motar harda Innarmu dake tuƙamu. Itama malamace a makarantar tana ɗaukarmu darasin islamic sutodis a wannan lokacin, kuma tana ɗaukarmu darasin turanci.
Kamar kullum muna tafe muna hira har muka iso makaranta.
Idanu muka haɗa da Gawata yana wajen sana'arshi ta sai da lemo a ƙofar Asiya Bayaro.
Murmushi ya sakarmun mai kwantar da hankali. Idanuna na lumshe ina mai sakar mishi da nawa murmushin.
Wannan murmushin shi ya riƙeni har akayi tara.
Luba muje ki rakani in kaima Gawata wainarnan dan Allah in É—an ganshi inji daÉ—i."
Dariya tayi tace.
"Hindu Duwaf amman kina yaudarar Gawata dan nasan in sama da ƙasa zata haɗe a gidanku baza'a taɓa bari ki Auri wanda ba ɗan boko ba kuma talaka ma. Yadda Baba Sojanmu yake girmama boko da masu karatun boko hmm wallahi ki kiyaye naga kunyi zurfi sosai shekara ɗaya kuna soyayyarnan ina jiye muku ranar rabuwarku. Kinsan fa a gidanku babu mai goya miki baya ki Auri ɗan cirani"
Illahirin jikina sai ya mutu mus. Abinda duk Luba ta faɗa gaskiya ne sabida da wasa nasan ba za'a taɓa yadda da Gawata a matsayin surukin gidanmu ba, bana tunanin ma yayi karatu fa gaskiya amman zan tambayeshi. Abunda na sani shine duk runtsi duk wahala bazan taɓa yadda a rabani da Gawata ba, dan zan iya rasa raina.
"Duwaf tunanin me kike yi ne haka? "
Hmmm tunanin makomar wannan soyayya da duk wanda yayi yinƙurin rabata tamkar ya rabani da rayuwatane nake yi."
Ƙarasowarmu bakin get ne ya katse mana hirar tamu gaishe da Baba mai gadi mukayi kasancewata ɗiyar malama Ruwayya yasa yake barinmu fita duk sanda muka zo kuma yana gani iyakarmu wajen Gawata ne ba wani wajen muke tafiya ba.
Gawata na zaune a gaban teburinshi na kayan marmari yana shan lemo. Ganinmu ne yasa yayi murmushi idanunshi farare cike dam da farin kwalli wanda baya taɓa rabo dashi duk ya caɓe ya zazzago ( wa ya tuno da Yaya Hambali a daidai wajennan?)Rigace ƴar shara a jikinshi, na wani yadi mai ruwan kunun kanwa, ya goɗe harya gaji da koɗewa, sai dai tas dashi babu ko sofane na ƙazanta.
Luba dai tace kwalline na asirin ƙifil shi yasa ma nake mutuwar sonshi. Amman sharri take yi mishi sabida bata sona dashi, ranar data soma faɗi nayi dariya harda fitsari.
"Tutar so ta Gawata, Æ´ar makaranta barkanki da isowa. Luba sannunku da zuwa ga benci ku zauna"
Bencin ya tashi ya bamu muka zauna shi kuma ya zauna a kututturen itacen dake fuskantarmu, yayi banza da kanshi wajen kallona.
Masar na miƙa mishi dake leda taji ƙuli da albasa yasa hannu ya karɓa yana godiya.
Sai muka zuba ma junanmu idanu, ni dai sai kallon ƙirjinshi mai tudu nake yi wanda a gaskiya yana daga cikin abinda ke burgeni gaya a tattare dashi. Murmushi yayi mun shima ya dubi ƙirjin nashi ya dawo da kallonshi wajena.
Luba ta miƙe ta koma ciki ta barmu.
"Ya shirye_shiryen biki Tutar so? "
Anata shiryawa biki saura sati guda.
"Allah ya nuna mana, gobe da rana zan shiga kasuwa in siyo miki angon in sha Allah da duk abinda ake buƙata. Amman Tutar so... "
Nasan abinda zaka ce in sha Allah ranar biki zaka zo ƙofar gidanmu, daga lokacin zaka ci gaba da zuwa gida muna zance tunda na shiga SS2 saura shekara guda muyi kandi, ya kamata a san da zamanka."
Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"To aimun alfarma gobe da daddare inzo har gida in kawo miki ankon mana. Nasan unguwar taku wajen zuwanane acan nake saro kayan marmari. Kimun kwatance zanzo"
Murmushi nayi mishi tare da mai kwatancen gidanmu. Saida aka buga ƙararrawa na tashi na koma makaranta.
A haka muke zancan Gawata bai taɓa zuwa gidanmu ba tsawon shekara guda muna soyayya duk ranar da akace asabar da lahadi ne babu makaranta, tofa haka duk zan damu, danma yana rubutamun wasiƙa mai daɗi ranar Juma'a da'ita zan tawo gida, inta nanatawa, gashi ya mugun iya rubuta kalaman soyayya masu kaifi.
Ranar da zamu yi hutu kuwa ba ƙaramin ɗagama Gawata hankali nake yi ba, haka zai ta rarrashina idanunshi duk suyi jawur a haka muke rabuwa.
Ana tashi a makaranta muka tarkato Innarmu ta dawo damu, yau Juma'a ne babu islamiyya babu karatun dare na Baba Sojanmu, da wuri muke bacci.
Wannan kenan
To kun dai soma jin asalin gundarin labarin Mijinyawa mai lemo ko?
Ina Ummin mama, da Fulani, da Mamanmu, da Mamanzee, da Maryama, na Munira.
Mutumin naku ashe mai lemone a ƙofar Asiya Bayaro
Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR
TSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA GOMA
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.