Sashe 63
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar Litinin kuwa na soma zuwa koyarwa a Babbar sakandare Government Day sakandare Jama'are. mijinyawa shi ya rakani har cikin Ofishin Shugaban makarantar ya ganni muka yi magana aka bani ajin turanci ina ɗaukar aji ɗaya jiniya kilas kenan ba siniya ba. Da ai makarantar firamare aka tambayomun, harma munje gwajin da akaimunne yasa aka dawo damu sakandare. Sabida akwai turanci a bakina sosai, kuma gwajin ta nuna musu nayi karatu ingantacce, tunda a gida ma Baba Sojanmu yana gurantar damu. A lokacin ba'a cika ɗaukan koyarwa a sakandare da takaddar sakandare ba, sai da Takaddar NCE gaskiya, amman ni dake kwana nayi ina adda'a an ɗaukeni sabida ana ƙarancin malamai gaya gaskiya. To taimakon Allah ne, kuma sunga nasan abubuwa da dama, gashi babu tsoro a maganata turanci zur_zur kamar ( Mrs jay malamar turancinmu da take horas damu) Kuma a lokacin takaddar sakandare mai ɗauke da sakamako mai kyau tana da daraja gaya, ba irin yanzu bane. Mijinyawa misali ko a firamare ba'a ɗaukeshi ba, karatun dai anyi ne ba ace ba'ayi ba. Wannan kenan. Nayi muku bayani da kyaune dan kada ku ƙalubalenceni wannan labarin a gaske ya faru a_kan karan _kan_kin kaina ya faru wallahil Azeem. A shekarar 1999 sunan makarantar Government Arabic college GAC) jama'are har zuwa shekara ta dubu biyu da ɗaya kafin aka sauya sunanta. To ni sanda na shiga tana a matsayin kwaleji larabci an kusa sauya sunan daf, dan watanni kaɗan nayi aka sauyata zuwa Government Day Duk da kasancewarta kwalajin larabci an haɗa ta da darussan boko na ɓangaren Arts don ba ma ɗalibai damar rubuta SSCE na WAEC ko NECO Darussan da suke bayarwa sun haɗa da turanci, lissafi, da tarihi hausa. Amman babu darussan kimiyya masu zurfi irinsu fizizs, kemistiri a tsarin karatun makarantar a lokacin da take amsa kwalejin larabci fa Allah yasa kun fahimta. Su Mijinyawa sune suka yita tana matsayin kwalejin larabci. Makarantar ta yaye manya_manyan masu riƙe da madafan iko na cikin gida Najeriya wanda in sunayensu za'a jero za'ayi mamaki. An kafa makarantar a alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da ɗaya. Nan mukai sallama da Mijinyawa aka nuna mun aji na shiga da Bismillah zuchiyata har tsalle take yi domin murna. ƙarfe ɗaya aka tashi A lokacin malaman mata mu uku ne duk sauran malaman maza ne. Cikin amincewar Ubangiji na soma koyarwa kuma abun daɗi da sha'awa yaran suna gane karatun nawa sai dai ƙalubalen farko dana samu shine na ciwon kai har jiri nake gani inna dawo gida sabida ihun karatu da ƙoƙarin nutsar da ɗalibai su saurari karatunma. Makarantar ƙauye ta bambamta da makarantar birni, haka ma yaran akwai bambamci. Kuma babu laifi ana karatu a jama'are ko wanne aji cike yake fam da ɗalibai babu laifi. To wannan koyarwar ta shafe mun kwatan damuwata sosai duk da gorin rashin haihuwa kusan sake tsananta yake yi barin in akayi haihuwa a dangi zamu je taron suna gabana har faɗuwa yake yi dan zaiyi wuya aje a dawo lafiya dole sai anyi mun shaguɓe ni kuma dana dawa makaraina zasu rabkeni, waɗannan sukai mun gorin kuma mutum biyu bakinsu ya karkace, sai da suka kwana biyu a haka kafin akaita roƙona bakin ya sake. A ciki harda Shafa matar Yaya Salihu. To wannan ja'ibar ta ɗan sassauta gorin gaya. Haka mijinyawa zai kwana a kaina yana yi mun adda'a babu wanda ya sake sanin halin da nake shiga mijinyawa shi ke ci ya cinye, haka in zai kaini gidan magani mu amso babu mai sani. Tafe_tafe har lokacin bikin gidanmu ya gabato saura sati biyu, ni kuma inaso saura sati guda in tafi. Atampopina guda huɗu na cira ni da mijinyawa muka shiga Bauchi muka sako su leshinne ban samu ba, amman supern na samu na bada ƙananun super guda biyu an bani super babba irin ta ankon sak sai sauran kuma na karɓo kuɗinsu muka dawo gida naci gaba da haɗa kayana. Ranar da zan tafi da sassafe na fito zan ma su Nanno sallama na tadda Uwatale zata haihu tana naƙuda. Bikin yayi daidai da hutun ƴan makaranta da aka bayar. "Kije Allah ya tsare muna cikin halin kula da mai haihuwa ne" Cewar Inna Ladi. A babbar tasha mijinyawa ya saka ni a mota kai tsaye zuwa kano. "Naso ace na rakaki sai in dawo to amman kuɗinne babu shiyasa kawai na haƙura watarana a motata zan tuƙaƙi in kai ki in da rabo." Ƴan kuɗaɗen jarinshi ya tarkata ya danƙamun dan ya fiddani kunya kawai. Idanu na lumshe kawai inaji uwa in zubar mana da hawaye, rayuwar fa tayi mana tsauri sosai hatsin da zamu ci sai dai mu auna, ranar daya carke mishi kuwa sai dai mu sha shayi da biredi mu kwanta, ko in Mijinyawa Babba ya dawo yana ƙoƙarin kawo mana tsaraba da hatsi sosai duk da uwatale na adawa da hakan amman dai bata isa shiga tsakanin ƴan uwan ba, shaƙuwar dake tsakaninsu da ƙarfi sosai. Babu wanda yasan halin ƙuncin da muke ciki a gidan muna iya bi da talaucinmu muna ɓoye sirrinmu sosai. Albashina na farko tare dashi muka shiga kasuwar Galdimari wacce take ci ranar talata anan muka siyo hatsi da kayan miya bushasshe da duk abinda muke da buƙata. Shine mukaita amfani dashi har watan ya ƙare, aka sake wani biyan a lokacin kuma ina shirin wannan tafiyar da zanyi sai ya hana in taɓa kuɗin a hakanma bani da kuɗin motar da zan dawo gida na tafiya kaɗai gareni da kuɗin ɗinkin biki sai kuɗin lesiri dana ƙullo, kuɗin daya bani kuma su takalmi, mayafi, ɗan kunne da sarƙa zan siya, ga tafiya Maiduguri shima bikinne. Motarmu saida ta cika kana yaimun sallama, kafin ya tafi na siya mishi rogo da ƙuli yayi mun godiya ya fita a tashar, dan nasan baida ko ficika, muma motarmu ta fita muka ɗauki hanya fetal tunanuka cike da kaina. Rayuwar a haka zata ci gaba da tafiya ƙila rayuwata a cikin wannan ƙauyen zan gamata babu lallai in samu cika burina dana iyayena fa. Ga lamura sai sake taɓarɓarema mijinyawa yake yi ina ganin dole in bashi shawara ya fita nema kamar yadda sauran ƴan uwanshi da abokanshi suke fita sabida gaskiya samarin garin basu fiye zama ba in ba lokacin damuna bane shine suke dawowa domin gabatar da noma da zaran hatsi ya dawo gida zasu tattare nasu ya nasu su koma inda suka fito. A haka cikin wannan tunanin muka shiga Kano da yamma sakaliya muka sauka a tashar unguwa uku. Ni dai magriba na shigo layinmu anata kiraye_kirayen sallah na shiga da sallama da akwatina da ƴar tsarabar da bata taka kara ta karya ba a bugu aka dai ce motsi yafi laɓewa. Dake su Innah Mairamu sune ƴan farkon gida dasu na soma gaisawa. Sai kallona take yi tana dariya. Jin muryata yasa Qazzafi ya fito yana washe baki. "Ahh manya ashe zaki zo kune ƴan farkon zuwa kenan, ya mai gidan naki? Yana lafiya ba dole in zo ba auren manyan yayu guda" "Ah lallai Duwaf kenan muje in kai miki akwatin mana. Yanzunnan Baba Sojanmu ma ya dawo sunje aiki Gombe sun dawo" Tare muka wuce na dinga gaisuwa lungu_lungu har muka iso lungunmu a falo muka tadda Baba Sojanmu yana zaune da kakin sojoji ga tsarabar manshanu da nono harda fura yayo musu. "Hinduwa kece a tafe har kin zo bikin? " Na gurfana a gaban Baba Sojanmu muka zuba ma juna idanu muna murmushi da jin daɗin ganin juna. Nice mace ta farko a gidanmu a lokacin da take Aure a uwa duniya, sai daga baya Salamatu Mijinta ya samu aiki a ƙasar waje ya tafi da'ita. "Ya Gawatan ba tare kuka zo bane, ke kaɗai kaddai ya bari kika niƙo gari?" Ba tare muke ba ni kaɗai nazo Baba Sojanmu yanzu Qazzafi yake faɗamun dawowarka daga Gombe kenan ga man shanu na samu na wanke kaina" Dariya yayi mun kawai. Muka gaggaisa da su Innah Abida Innarmu tana madafi can na barota ita ke da turaka yau tanata hidimar tarbar miji. Ciki muka shiga ni da Qazzafi a ciki muka tarar da Yaya Soja da Akarami suna shirin tafiya sallah dan yanzu za'a shiga. Akwatina Qazzafi ya ajjiyemun suka rankaya har da Baba Sojanmu zuwa masallaci. Mayafina na cire na zauna a bakin gado ina sauke numfashi inajin wata iska na shigana ga hasken lantarki tauwar ya mamaye dukkan ɗakin. Waje yasha gyara an raba ma Innarmu ɗakinta ya zama ciki da falo ga fenti da kujera an saka mata a falon waje yayi kyau gaya. Ga atampopinan bandir bandir na anko innarmu ta jibgo dama ita ke kawo duk atampar ankon bikin gidan. Ina zaune tamkar wacce ta wanke makanta Innarmu ta shigo da nata kason tsarabar Baba Sojanmu. "Hinduwa ashe zai barki kizo da wuri haka? Hmmmm kije kiyo alwala kiyi sallah kici biski" Baki na washe mata na tashi na fita na ɗauro alwala na dawo na gabatar da Sallah ina kan sallaya Luba ta shigo da sallamarta. Ahh Luba duniya ashe har labarin zuwana ya shiga gidanku? " Dariya muka yi duka ta zauna kusa dani tace. "Kinsan dake ƙawancan Innah Mairamu ya sake ɗinkewa da Innarsu Sadiƙa harta shiga ta fesa musu zuwanki wai kin rame kin lalace ƙafafuwanki harda kaushi. Ni kuma dana shigo saina samu akasin hakan, gashi kinsha ƙunshi ƙafarki shar." Jikina na kalla shar dani atampa mai tsada ce a jikina sabuwa ban taɓa sakata ba, takalmina da jakata ma sababbine fil haka lafayar dana naɗo sau biyu kacal na taɓa sakawa shar dani ko na birni ba zasu nuna mun komai ba wata takwas a ƙauye baici ya ragargazamun yanayina ba. Sannan duk da bana ta'amali da wayayyu ina karance_karancen littattafan hausa wanda babu duniyar da basa leƙawa babu wata iriyar wayewa da basa kawo mana, tare suke tafiya da zamani kafaɗa da kafaɗa. Ikon Allah Innah Mairamu dai zafi take ji dan naƙi Qazzafi kuma ni bana nadamar kasancewata a ƙauye Luba wallahi Aure daɗine dashi babu abinda ya kaishi daɗi musamman in mace tayi dace da miji mai tausayi" Shewa Luba ta saka ta bani hannu muka tafa tabb. "Nima Aurenmu da Sanusi saura wata huɗu in