← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 77

Sashe 36

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saka mata dubu goma. Ga takalmi da mayafi harda ɗan kunne da sarƙa da kayan kwalliya duka ya saka. Rigar mama da gwari na tsuma da ɗan kamfai kawai zan sai miki gobe ki tarkata kayan in an nuna ma matan gida ki kai gidansu Luba ɗinki." Bayan mun hallara a tsakar gida Baba sojanmu ya kama koya mana lissafi muna zaune muna aikin daya bamu ga fitilu irinna sojoji masu bala'in haske an kange kowanne ƙoƙarinshi ya amsa tambayoyi biyar ɗin da Baba Sojanmu ya rubuta. Muna rubutun ina jiyo hatsaniyarsu da Innarmu lallai ranta ya ɓaci dan bata fiye ɗaga muryarta a saman na Baba Sojanmu ba, mun dai san ba kanwar lasa bace shi kanshi Baba Sojanmu na kiyaye rikici da'ita. Nasan fishinta na da nasaba da maganganun da Baba Nagoɗi ya yayyaɓa mishi a gaban su Inna Abida. A fusace ya fito ya sani aikin karɓan takaddun kowa akan gobe da daddare in anyi maki za'a babbamu. Mun shiga zamu kwanta muka tadda Innarmu sai faɗa take yi a tsaye hancinta har hunhuna yake yi tsabaragen faɗa. Washegari ma da sabon rikicin dai aka kuma tashi sabida Innarmu ta zagaya ta nuna abinda Gawata yayi kamar yadda kowa yayi, nawa sai ya zama gutsiri tsoma ni nama tafi gidansu Luba kai ɗinki Ashe har rirriƙe Inna Mairamu aka dinga yi wai zata daki Innarmu sabida tace in duk maza sun ƙare bazan auri Qazzafi ba. Shine tace mai zaiyi dani gajera dani mai kama da agwagwa wajen gajarta kuma wai mummuna. Na riƙe wannan maganar sosai dan a kunnena ta dira ni kuma nayi alƙawarin in dani da Qazzafi ne kaɗai mutane da muka rage a duniya saidai mu mutu a haka ina da riƙo sosai da rashin mantuwa, sai dai zan yafe in an matsamun a hakanma ba komai nake iya yafewa ba. Haka dai wunin ya kasance Innarmu tana ta girke_girke ga fenti anayi mana na lungunmu da duka ɗakunanmu dan baƙin Biu ma suna hanya yau dangin Innarmu haka akayi dasu zasu iso sabida su taimaka ma da Innarmu wajen hidimar siyayyan kayan ɗakin Amare Baba Sojanmu da safe ya basu abinda yake a hannunshi na kayan katako da duk abinda ya dace uba yayi mai son yin bajinta saita cika, ya ɗakko atampa da shadda ya ba Innarmu yaba Inna Abida, kayan Kitchen dama iyaye ke yi. Innarmu ta jima tana tarinta a ɗakin Innarsu Luba ƙarƙashin gadonmu da saman sib ɗinta cike da kayayyaki. Saman sib kuma zannuwan gadone masu bargo shaƙe da buhu biyu. Wajajen magriba sai ga dangin Innarmu su Inna Yahanasu da Inna Yalewa da Inna Hewa. Dukkansu ciki ɗaya suka fito da Innarmu kuma a Biu suke Aure sai Inna Hewa dake aure a chad tana Auren hamshaƙin mai kuɗi. Abin daɗin shine dukkansu da iliminsu kuma suna aiki. Ai gida kam ya soma ɗaukar haramin yare dan dai a falo suka bace sukaita yara yaren kanuri anayi ana dariya ga biski da miyar margi Innarmu ta tarbesu dashi. Ana idar da sallah yaro yazo yayi kirana na sulale na fice. Mun daɗe sosai da Gawata muna hirarmu a tsaye cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Kayan marmari da balangu ya kawo mini harma muka isa inda Luba suke zance da Sunusi suka gaisa kana Gawata ana isha yai mun sallama ya wuce. Gidanmu ya ɗauki haramin ƙamshi fa washegari aka soma yi ma amare gyaran jiki namu na al'ada, su Innarmu da Inna Yalewa kuma suka shiga kasuwa ganin kayan gado wanda tunda aka kawo sadakinsu Yaya Saratu Innarmu ta bama kafintan aikin kayan gadon. Kafin su dawo Ƴan kwantagora da su Zaria ne dangin su Inna Mairamu da ƴan kaduna, katsina sukaita zuwa gida ya cika ya tumbatsa sosai. Ranar sakun lalle aka zaɓi masu zuwa jere ai kafin washegari ranar ɗaurin aure maƙota da ƴan cikin gida sai tattauna irin kayan da akaima su Yaya Saratu akeyi, gaskiya Innarmu akwaita da ƙoƙarin fidda ɗa kunya ko da kuwa bashi zata ciyo dan ko sallane ana azumi saura wata biyu ta game mana ɗinki an goge an adana kuma kaya masu tsada. Munyi daban sosai da yaran cikin gidan namu. Ga Baba sojanmu in dai zaka yi karatu sakamakon jarabawarka zata yi kyau to zai iya maka komai sabida yadda yake son karatu. Shi yasa su Yaya Saratu duk ƴan boko zasu aura. Ranar Juma'a aka ɗaura Auren ƴan mata gomannan rigis anata zolayarmu akan muma ba zamu shige shekara huɗu a ƙasa ba sabida mune masu tasowa. Sai rawar kai sa'annina suke yi masu neman suma su samu suyi saurayi. Tun ranar laraba muka wayi gari da ƙunshin gargajiya da Inna Yalewa tayi mana. Tare da Amare kitso ma su sukai mana guda ɗari da hamsin akayi mun irin kitso na al'adar kanuri wanda wasu zasu yi baya wasu zasu yi gaba gefe da gefe na amare dai yafi namu siri_siri shine bambancin, ragowar Amaren kuma gidajen kitso da gyaran jiki da lalle suka je. Biki yayi biki ƙawayen Innarmu malaman makaranta da lauyoyi duk sunzo sun kuma bata gudunmawa sosai kasancewarta mai yi ce sosai itama. Abincin da akayi a ɗakinmu kala uku akayi saɓa'in ƴan cikin gida daga masu shinkafa da miya sai masu fate, da masu yin jalof da kifi haka Amman mu munyi masa, munyi tuwon shinkafa da miyar taushe, mun yi burabusko da miyar margi wanda akayita da kifi karfasa ɗanye tillafiya kenan. Bayan ɗaurin Aure da yamma muka wuce wajen walima. A wajen walima ma mun raba masa, da cincin, da abinci harda tsokar nama sai jus. Ana tsaka da walimar Luba ta taɓani na juyo muka haɗa idanu. "Gawata yana waje yazo tun ɗazu kizo muje muna waje da Sunusi ne. Da sauri na miƙe da leda biyu a hannuna wanda nayi mishi zubi na musamman. Tun daga nesa muke jifan juna da kallon_ kallo kafin in ƙarasa inda yake sai kawai naga Qazzafi a gabana yana mun murmushi yana saye da kayan sojijinshi da anininshi biyu. "Giwar mata wannan irin kyau haka sai kace ranar bikinmu gaskiya kinyi kyau sosai sai ƙamshinku na al'ada kike yi wanda yana daga cikin abinda yafi ɗaukata, amman a cikin abubuwan da suka ja ra'ayina harda gajartannan taki wacce ta dace dake" Kallonshi nayi nace. Yaya Qazzafi yaushe ka dawo? " "Yau na dawo dani aka ɗaura Aurenma. Ina zaki je kike gaugawa haka? " Baƙone dani bari inje in sameshi kada yaga kamar nayi mishi wulakanci " Kafin ma yayi magana nayi gaba zuwa wajen mijinyawa yana saye da yaji mai masifar arha da wannan nacacciyar tashi ka fiye nacinnan dai da baya sauyata. "Barka da isowa Tutar so. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara wannan halittar. Tutar so wato wannan gajartar taki da yanayin yadda zubin zatinki yake bazan ɓoye miki ba dole ya ɗebi hankalin duk lafiyayyen namiji, kitsonnan yayi mun kyau ina fatan in dinga ganinshi a kanki ko da yaushe idan munyi Aure" Gawata kenan kalamanka suna mun daɗi sosai. Sai inji na sake son wannan gajartar tawa da wasu mutanen suke amfani da'ita wajen zagina basu san da Allah suke yi ba ni Hindu menene nawa tunda haka Ubangiji na yaso ya ganni. Gashi sai Allah ya bani dogon miji ingarma" Murmushi yayi ya dube kanshi yana kallona. "Na fahimci kamar yadda jikinki yake burgeni kema haka jikina yake burgeki musamman ƙirjina ko? Kada ki damu zan kula miki dashi zan ci gaba da ɗaga ƙarfe, wannan ɗinma a ƙauye ne da bamu da abun yi shine muka saka kanmu wannan aiki ni da su Abdulƙadiri" Yauwa ka tuno mun ni kam menene matakin karatunka naga dai ka iya rubutun hausa sosai kuma ina yawan ganinka kana karanta littatafan yaƙi, kwanaki ma na ganka da littafin dare dubu da ɗaya" Yana wasa da zoben azurfan hannunshi yace. "Iyakata makarantar sakandare na kammala ta gwamnati a ƙauyenmu iyakar matakin karatun nawa kenan a hakanma mun samu, karatun ma sai a hankali an dai kammala" Banji komai a raina ba sai jinjina yadda zan bayyana Gawata a matsayin miji. Ni dai a wajen soyayya na lalace har aka tashi a walimarnan bashi ledar walimar nashi, nabi ayarin ƴan gidanmu muka koma gida. Da daddare a gidan Yaya Saratu ni dai na kwana ragowar suna gidan Yaya Zubaina Washegari aka yi wunin biki shikenan taron biki kuma ya ƙare. Bayan kwana biyu da gama biki baƙi duk suka watse mu kam dama tun monday muka koma makaranta. Qazzafi yaso in bashi lokaci na amma naƙi fur na dinga mishi yawo da hankali. Sau uku yana ganina da Gawata a ƙofar gida muna zance a haka hutunshi ya ƙare ya koma bariki a kudu yake. Gaga_gaga A haka har Watan Azumi ya tsaya ga karatu, ga rana, ga azumi. Ƴan matan gidanmu samarinsu suka soma musu bajintar azumi Gawata ma yayi mini daidai ƙarfinshi ba'a raina ba, duk da dai Innarmu ta ɗanyi ƙorafi kaɗan, a hakanma bata san wasu abubuwan ni na ƙara ba. Da sallah yayi mun atampa da shadda da takalmina sukos ja mai kyau da jan mayafi. Haka dai tafe_tafe. Sannu sannu ar mun zana jarabawarmu ta ƙarshe a makaranta mun bar makanta muna murna kamar yadda sauran ɗalibai ke murna. Bamu cika sati ɗaya da gama karatun ba Baba Nagoɗi yasa aka tarkato kawunanmu kusan mu goma muma. "Ko wacce cikinku ta turo mana wanda take so zuwa jibi mu ganshi mu yi mishi tambayoyin daya dace, ayi bincike a kanshi kafin manya su shigo ciki, batun ci gaban karatunku kuma, Soja ya tsaya muku, sai kun soma jami'a za'ayi Auren kuma bai ɗaura nauyin karatunku akan mazajen da zaku aura ba. Shi yaji zai iya zai dinga biya har ku kammala, shi yasan cukurɗa kurɗar da zai yi aikinma ya samu in kun kammala karatun. Ko a cikinku akwai wacce bata da tsayayyene? " Duk mukai shiru ko wacce tana da masoyinta. Baba Dogara yace. "Ko wacce tana fita zance, kayan azumi da samarin suke kawowa ai yana isowa kunnuwanmu." Baba Sojanmu yace. "Ni naso a barsu su soma jama'a ko matakin na uku ne sai suyi Aurensu sa ƙarashe a gidajen mazajen nasu, kada ayi sharaɗi da wani ya saɓa
Chapter 36 · 0% Book details