Sashe 22
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turmi na jawo na zauna a kusa da Akarami. Baba Nagoɗi ne ya shigo ɓarayin namu da sallamarshi. Cikin ladabi muka gaisheshi ya amsa da fara'a. "Hinduwa ina labaran na ganki sassafe a gidan, ince dai lafiya ko? " Lafiya lau Baba." To_to_ to ya jikin shi Mijinyawan ya warware ko? " Da sauƙi sosai Baba" "Allah ya ƙara sauƙi Ruwayya kirawo mun Soja wani abunne ya taso a ɓarayin Dogara. Zamu je yanzu kice ya sameni a lungun Dogara" "To shikenan bari a taso shi. Ke Hinduwa zo ki zuba masarnan a tanda ina zuwa" Wucewa ciki tayi Baba Nagoɗi ya ɗauki masa biyu ya wuce Lungun Baba Dogara. Su Baba Lukumanu sukaita zuwa suna wuce wa Baba Sojanmu ne ya fito shima. "Hindu kece sassafe haka lafiya dai ko? " Baba Sojanmu ina kwana? " "Lafiya lau bari inje in zo sai mu gaisa da kyau" Wucewa ciki yayi Innarmu ta zauna ta kalleni tace. "Duk da ke me ƙoƙarin ɓoye damuwace ni mahaifiyarki ce na tabbatar kina da damuwa" Idanu suka zuba mun. Hakane Mijinyawa ne zai ƙara Aure" Murmushi Innarmu tayi, Akarami kuma ya harareni. "Kishiyar kike tsoro kenan ke da kike da tauri kamar tsandauri? Mu bar maganar bari in sallami mutan gidan in mun shiga ciki ma tattauna inba haka ba kinsan halin gidan namu" Cewar Innarmu Ni dai bance komai ba ɗaki na shige nayi kwanciyata, daga nan ban san me kuma ya faru ba sai buɗe idanuna nayi naga Innarmu da Akarami a kaina suna tayi mun tofi. "Innarmu sun saketa. Sannu Hinduwa dama ashe baki rabu da ciwonnan ba har yanzu? " Innarmu tace. "Allah ya kyauta kawai dama su basu fiye barin mutum gabaki ɗaya ba. Sannan sukan kawo ziyara a lokacin da mutum yake cikin ɓacin rai ko cikin murna, to duk macen duniya bata son kishiya, babu wacce take murna da zuwanta sai dai fa dole, kaga kuwa dole su motsa. Bari inje in samu matan gidan munafukai kowa ya baza kunne yana son jin ƙwaƙwaf" Fita tayi ina jiyota tana musu bayanin mutanena ne suka tashi ba wani abun bane. "Wani abunne ya faru da'ita da suka tashi?" "Me zai faru da'ita yau Hinduwa ta soma hawa makaraine Abida, koko dai son jin abinda babu ruwan mutum a ciki. In da matsala ai dole zaku sani balle matsala bama fatanta. Na zaci kun cire rai da jin matsala daga gidan Hindu shekara sama da ashirin ai shi kaɗai ya'isa abun nunawa babu yaji, babu kawo ƙara" Shigowa tayi tana maganganu, Innarmu bata da daɗi kuma bata barin ta kwana sam. "Hinduwa tashi ki zauna muyi magana kinga nema kike yi ki tona mana asiri a cikin wannan gidan, Allah ma yasa makaran basu yi tonan silili ba ihu kawai sukai tayi suna nannaɗeki" Ina daga kwance nace. Innarmu na baro gidanne bazan taɓa komawa ba har abada na rabu da Mijinyawa" Bakina tayi saurin rufewa tace. "Kul kada ki bari ko ƴan uwanki suji wannan maganar balle Baba Sojanku. Hindu sabida zai ƙara aurene zaki ce kin rabu dashi, yaranki fa sannan saida kika gina gidanki kika gina shi kanshi mijin zaki tsallake ki barshi da wacce zai aura ta more ita kaɗai. Kada ki mance nifa nice ta biyu a wajen mahaifinku bayan ni yayo wata matar, ke kishiya fa ba wata abar tsoro bace in dai mace tasan kanta. Kaga Akarami bamu waje maza wannan ba karatunka bane" Fita yayi ba tare da yace komai ba. Innarmu Asama'u fa zai Aura yarinyar da tsugunnawa in haifeta ne kaɗai banyi ba. Wallahi aurenta da zai yi ko kusa bai tayar mun da hankaliba, zamanne yazo ƙarshe kawai" Zama ta gyara da kyau tace. "Hindu kenan, ai wannan kaɗan daga cikin butulci da sakayyar wasu mazan kenan. A fuskar addini baiyi laifi ba tunda akwai aure a tsakaninsu. A al'adance ana barin halak dan kunya. Nasanki da jarumta da dakiya sosai banyi zaton wannan abun zai tashi hankalinki ba sam, kuma na yarda dake Auren Asama'u bazai girgiza duniyarki ba. Duk da kishi halittane, kuma kishin abun so gaskiya ne. Yarinyar da rainonki ce itace zata ɗaukeki a gidan da da tallafinki ya tsaya da ƙafafuwanshi, mijin da kike da tasiri a rayuwarshi shi zaki bar mata akan me? Dangin mijinki da facalolinki da suke son ganin faɗuwarki su zaki bama ƙofa suga bayanki? Hindu yanzu duk idanu a kanki suke kuma kowa ya baza idanu da kunne dan son ganin irin haukar da zaki yi, ko wanne irin mataki zaki ɗauka. In da nice ke kuma in kin yadda na isa baki umarni to ba shawartarki nake yi ba umarnine ki koma gidanki ki ɗauki idanu ki zuba ayi komai a gama kamar yadda ba'a iya sanin logonki har ƴan uwanki kada ki sake asan kina da rauni akan kishi. Kada ki ɗauka amanarki aka ci. Ki daure ki danne Hindu ki rufa mun asiri ki tuno da yadda akayi auren da sharaɗin Baba Sojanku a kanki in kin mance na tuno miki kinsan a sharaɗinku babu yaji babu kawo ƙara kin sani. Kuma in sama da ƙasa zata haɗe kinsan babu mai sauyashi, kaifi ɗayane shi. Daga nan ki wuce gidanki kije ki zauna ki lallashi zuchiyarki kada ki bari damuwar komai ta taɓa lafiyarki, kinga makaranki har sun soma kawo ziyara, da sannu zai yi nadamar abinda yayi miki ke dashi sai kun zama tamkar sirikarshi tsabaragen kunyarki da zai dinga ji, me akayi akayi Asama'u, me kuma akayi_akayi Mijinyawan shi kanshi, ai yasan alfarmar da akayi mishi, ya kuma san kin mai tazara. Irin tazarar da in ba rayuwarshi da kika shigaba ba lallai ya kamoki ba. Yanzu haka ma da sauranshi bai kamoki ba sai ya jira wallahi. Kuma ki sani ko da taji daɗinshi na ɗan lokaci ne akwai lokacin da zai zo in ance ya kalleta ma sai yaji kamar an haɗashi da aiki, in akace ya taɓata sai yaji tamkar ƙasa ta tsage ya faɗa." Miƙewa tayi ta fita. Ni kuma na lumshe idanuna ina nazarin maganganunta da sharaɗin dake kaina da irin kafiyar, da dogiyar Baba Sojanmu wanda na gado daga wajenshi na ƙara a saman na mai sunana. Ga kuma abubuwan da suka wanzu tsakanin Asama'u da Mijinyawa dake dawo mun wanda wannan sirrin na burneshi har abada ƴan uwana ba zan bari suji ba, ko babu komai dan yara da irin yadda ya soni a baya zan alkinta mishi mutuncinshi, duk da shi bai alkintamun nawa ba, amman a idanun yaranshi yana da girman darajar da ya kamata in basu dama suci gaba da girmamashi abadan. Amman batun in zauna ni da Asama'u mu haɗa miji, wallahil azeem babu shi, babu_babu, ba kuma za'ayiba wallahil ƙudrat, hukuncin dana ƙudura a zuchiyata shine mafitata babu mai hanani aikata wannan abun face ƙudurar Allah. A hankali naji ina samun sauƙi a zuchiyata. Murmushi kawai nayi tare da girgiza kai ina hasaso yadda zanma mijinyawa. Saiya gaji da halayena yaji ya tsani kanshi, dama rayuwar baki ɗayanta, zan fice fit a cikin rayuwarshi, ko da daga kanshi maza sun gama ƙarewane. Kuma nayi imanin sai rayuwarshi ta girgiza, ta dawo salab. Shigowa Innarmu tayi da masa da miya ta ce. "Tashi kici Hinduwata ki sha maganin ciwon jiki kiyi kwanciyarki, in yamma tayi kya koma gidanki. Shi mijinyawa yasan gida kika gudo?" Bai sani ba, tunaninshi wajen aiki naje" "To na dai san a lokacin da yace miki zai ƙara aure, kuma ya faɗa miki Asama'u zai Aura. Fatan alkhairi kawai kika yi mai ba tare da nuna karaya, ko mamakin lamarin ba, ina da yaƙini a kan ki" Ajjiyar zuchiya ta sauke. miƙewa nayi na karɓi masar na soma ci kenan Baba Sojanmu ya leƙo daga bakin ƙofa ya tsaya yake tambayar Innarmu abinda ke faruwa" "Naji gida ya ɗauka wai Hinduwa gidanta babu lafiya har makaranta sun tashi. Dama ihun da nake jiyowa nata ne? Mu mun ɗauka a wajene ai" "Ohh ni Ruwayya. Su dai dake fatan da suke yi ta samu matsalane a Aurenta sabida sun san dambarwar da akayi kafin auren. To iyakar shekarun da suka shuɗe baici ace sun haƙura da son ganin bayan Aurenta ba? Ciwonne kawai ya tashi babu komai a tsakaninta da mijinta." "Ke Hinduwa hakane? " Eh Baba Sojanmu babu komai. Dama tun ina hanyar zuwa nake jin wani iri" Kai ya gyaɗa yace. "To Allah ya ƙara sauƙi sai ku koma wajen mai maganinku ai" Eh mun koma ina kan shan magani kwana biyunnan abun na taɓani" Shiru yayi baice komai ba, sai can yace. "Allah ya kyauta ya bada lafiya. Ya batun Mastas ɗinki Hindu yafa kamata ki jona karatunnan yana da matuƙar amfani '. Ilimi jogone babba" Zan jona in sha Allah nayi maka alƙawari zaka yi farin ciki dani" Murmushi muka yi dani dashi ɗin Ya saki labule ya fita. "Kinga ni kuma kinji ko? Dama ai kinsan babu auren da idanun kowa yake kanshi irin wannan auren naki. Ki daure ki rufa mana asiri dan Allah" Innarmu sai duk ta tashi hankalinta. Shikenan Innarmu nayi haƙuri zan kuma koma zanyi duk abinda kika ce" "Yauwa Hinduwa nagode miki. Shi kuma mijinki a tsakaninku kinsan irin yadda zaki tafiyar dashi ke macece, duk macen data zama wulaƙantacciya ƙasƙantacciya ita taso, ba'ace ka wulaƙanta kanka ba, ke kika san logon mijinki. A baya Mahaifinku ya taɓa yi mun wani abu lokacin daya Auro Turai ranar girkina ya shigo yake roƙona in siyar mishi da kwanana. Hindu ranar itace rana mafi zafi da muni a gareni, kuma shine dare mafi tsayi. Banyi musu ba na siyar mishi, sabida in ban karɓi kuɗinba ma zai tafin sabida a lokacin Amaryace ludayinta shi ke kan dawo. Inma ya zauna a wajen nawa ni dashi ba zamu mori daren ba asarar daren za'ayi. Gashi ko da wasa bana son yasan menene logona. Kuma nasan dole ya sanar mata zai zo siyan kwana. Kema kinsan ina ji da kaina, na kuma san mutumci, da kimar kaina gaya. Hindu ranar na gane dare da tsayi yake. Turai ta gama kwanaki biyunta, ita kuma Abida ita ya dace ta je turaka, tako shirya tayi girki taje. Hmmmm in taƙaice miki saida na shekara