← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 78

Sashe 9

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, Oga Habib, wannan shine dalilin da ya sa, nahad'a kayana dadaddare na gudu, batare da kowa na gidanmu ya sani ba. Koda na fita gida lokacin duhu ya yi sosai. Tafiya nake amma ban san ina zani ba, ga duhun dare ya farayi, gashi tsakaninmu da titi akwai nisa sosai, haka na kama hanya ina tafiya ina sauri ga damuwa da tayi min yawa, ga yunwa rabona da abinci harna manta, sai dai in naji yunwa ta daman in dama kunu insha. Damuwa da yunwa da gajiyar da na yi ce, tasa na yanke jiki na fad'i ban sani ba, shine kuka tsinceni ainda kuka gani". Hassana kallan Habib ta yi, ganin har yanzu bai fasa typing d'in da ya ke yi ba. Ita fa gani ta ke kamarma duk surutannan tana yin shine kawai amma bajinta ya ke ba. Hassana kallan Habib ta kuma yi, cikin fargaba ta ce, "Oga Habib Wannan shine da lilin barina gidanmu". Hassana ta yi maganar da dad'ewa , dan hattacire ran Habib zai bata amsa ma.Sannan zuwa can ya d'ago kai yana kallanta, sai da Habib ya gama yima Hassana kallan cin mutunci sannan ya ce, "ya sunan ki ma kika ce? ". Hassana bakinta harrawa ya ke wajan ba Oga Habib amsa da cewa, "Hassana". Habib Kallanta ya yi, ya ce, "Hassana ke ba abin tausai ba ce, idan ke abin tausai cema tom ni ban tausaya miki ba, kuma ni bazan tai makeki ba. Duk wadda ta gudu daga gidan Iyayanta tom yawan bariki ta fito, dan haka fitar min daga office ". Habib ya fad'i maganar cikin d'aga murya. Jikin Hassana rawa ya farayi dan sosai ta tsorata da Habib. Hassana kuka ta farayi, cikin muryar kuka ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri, Wallahi bayawan bariki na fito yi ba, kona zauna gidan b........ ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru. Habib nuna mata hanyar fita ya yi da hannu, ya ce, "fitar min daga Office na ce, stupid kawai! ". Hassana da saurin ta har tana d'an tintib'e ta fita daga office d'in. Saura kad'an Hassana su yi karo da Bilya shi kuma lokacin yazo shigowa. Bilya da d'an damuwa ya bita da kallo dan duk da bai san labarin yarinyar ba, sosai ta ke bashi tausai, acewar shi yarinya k'arama haka ace bata san ina zata ba. Bilya cikin tausan Hassana ya k'arasa office d'in Oga Habib.Bilya cikin girmawa, ya ce, "Barka da hutawa Oga Habib, ka yi hak'uri dan Allah ka kirani banzo da wuri ba, bana kusa ne". Habib kallan Bilya ya yi, sannan ya ce,fuskar shi a d'aure, alamun ranshi ab'ace ya ke. "Bilya me yasa ka kai k'arata wajan Momyna". Habib ya yi maganar cikin d'aga murya, dan shi aganinshi bai kamata ace yaron shiba, wanda ya ke ci ak'ark'ashin shi ya zartar da hukunci akanshi ace ya kai k'ararsa wajan mahaifiyarsa ba. Bilya cikin kame-kame ya ce, "Oga Habib ba...... ". Habib d'agama Bilya hannu ya yi, ya ce, "ka adana kala manka, amma kabar kama k'afa da son da Mahaifita kema, dan kar hakan yasa kaji zaka iya yin koma, wannan shine last worning da zanma, duk sanda ka sake ma hajiya complain akaina, daga ranar Bilya kabar aike a k'ark'ashin Sanat yoghurt". Habib na fad'in haka ya kalli Bilya, ya ce, " Bilya da kai da Baba Lami na baku, suspension na one month". Bilya da alamun tsoro ya d'ago kai yana kallan Habib, jin wai ya da katar da shi har wata d'aya.Bilya magana zai yi Habib ya nuna mai hanyar fita. Fita Bilya ya yi, batare da yace ko mai ba. Bilya na fita ya iske Hassana can bakin get d'in wajan tsaye, ta yi shiru ita kad'ai. Bilya gurinta ya k'arasa, kallanta ya yi sannan ya ce, "korarki ya yi ko? ". Hassana kai ta d'agama Bilya. Bilya shiru ya yi sannan, ya ce, " Ni Wallahi duk namarasa abinda zance miki, ni kaina yanzu haka ya dakatar dani aiki harna tsawan wata d'aya, ga aurena saura wata biyu masu zuwa, ni kaina yanzu kinga in da munyi haka dashi ba damar in kwana gidansu sai dai in koma d'akin abokina da kwana. Tom kuma itama Baba Lami bata san kowa ba a Abuja, kuma kinga ya dakatar da ita aiki itama, yanzu na san sai dai ta koma garinsu. Bilya shiru ya yi, yana tunanin yadda zai yi da Hassana amma bai sani ba,hakan yasa, ya ce, "Hassana ni yanzu ma kaduna zan tafi, ki zauna nan anjima kad'an zaki ga manager ya fito, zaki ganshi da red d'in shirt da black jeans. Ki mai magana, in dai ya amince ya d'auke ki aiki shikenan, Oga Habib babu ruwansa da d'aukar ma aikata". Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Tom Oga Bilya, wajan kwana fa?, in ya d'aukeni aikin? ". Shiru Bilya ya yi dan shi yama manta da wajan kwana sai yanzu ya tuna. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "Hassana ki ci gaba da zama nan, idan kika ga Oga Habib ya fito, ki je ki sa ke rok'anshi, k'ila ya amince". Bilya na kaiwa nan, ya yi ma Hassana fatan alkairi ya tafi. Hassana cigaba da zama ta yi kamar yadda Bilya ya ce mata, tana jiran fitowar Oga Habib. Hassana har 8:00pm tana gun zaune, tana jiran taga fitowar Oga Habib amma shiru, Hassana tunini ta rik'ayi k'ilama ya tafi bata sani ba, inda ta je sallah. Wata zuciyar ta ce mata, tom idan ko haka ne ina zata kwana,uhm tom wai in ma naganshi lallene ya taimakan d'in. Hassana na cikin wannan tunanin taga motar Oga Habib ta fito. Hassana da saurinta har tana tuntub'e ta matsa wajan motar Habib d'in, shikuma lokacin ya tsaya yana ma mai gadin gun magana. Hassana ko kafin tak'arasa Habib ya yi ma motar shi key. Hassana tsabar furgici da rashin sanin yadda za tayi, kawai sai ta zauna gun tana kuka. Hassana na nan zaune tana kuka kamar wata ta b'abb'a, manager gun ya fito domin tafiya gida. Tsayawa ya yi ganin mutum a zaune, kuma bisa ga alama kamar kuka ya ke ji. Tsayawa manager ya yi ya fito daga motarshi, inda Hassana ta ke zaune tana kuka ya k'arasa. Tsananin hasken gun yasa tun kafin ya k'arasa ya k'are mata kallo. Kallanta ya yi da kyau sannan cikin siririyar muryar shi ya ce, "ke lafiya?, zaki zo nan ki zauna da daddarannan? ". Hassana da sauri ta d'ago kanta tana kallan manager. Manager ko jin Hassana ta yi shiru tana kallan shi, ya sa ya k'ara cewa, ", ke bakya ji ne! ? ". Ad'an tsawace ya yi maganar. Hassana kallan Manager ta yi, cikin muryar kuka ta ce, "Bansan ina zani ba ne". Manager da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "kamar ya baki san ina zaki ba?, tom waya kawoki nan? ". Hassana kai tsaye batare da tunanin komai ba, ta ce, "Oga Habib ne ya tsinceni shida Oga Bilya, shine ya kawo ni nan, ni kuma bansan kowa ba a Abuja, kuma ya hana in sake zuwa mai gida". Hassana ta idasa maganar cikin kuka. Manager shiru ya yi yana mai ci gaba da kallan Hassana, dan shi gaba d'aya bai gane takan maganarta ba. Manager waya ya ciro ya kira Oga Habib. Kira d'aya Habib ya d'aga yana tambayar manager lafiya, dan manager bai cika kiran shi airin wannan lokacin ba. Manager ko Habib na d'agawa ya ce, "M. D. Dama wata Yarinya ce nan na gani wajan get zaune tana kuka, shine dana tambayeta ta ce min wai kaika kawota, ni dai gata nan bama wai gane kan zancan nata nayi ba". Habib ba tare da tunani wata yarinya ba ce, dan in yaga dama yanada girki. Habib shiru ya yi sannan ya ce, "Manager kawo ta nan gida". Habib na cewa haka ya kashe wayarshi. Manager ko kallan Hassana ya yi, ya ce, "zo mu je". Hassana motar manager ta shiga. Manager gidan Habib ya kai Hassana kamar yadda Habib ya ce mai, ya kawo ta.Daya ke duk masu gadin gidan sun san Manager hakan yasa suna ganin shi suka bud'e mai get d'in ya shiga. Manager direct falon Oga Habib ya nufa, Hassana na biye da shi, sai kalle-kalle ta ke. Hassana azuciyarta ta ce, "Tabbas dole Oga Habib ya yi wulak'anci, ga kyau, ga kud'i, ga ilimi". Manager ko da ya je bakin k'ofar Habib nocking ya yi. Kasan cewar Habib ya san manager ne ya sa, ya ce, "yashigo". Manager shiga ya yi, da Hassana da ke biye da shi. Hassana sosai ta rud'e da had'uwa irin ta falon Oga Habib. Ko mai na falon milk & Orange ne. Habib ko kallo d'aya ya yi ma Hassana ya gane ta. Hakan yasa cikin d'an fad'a ya ce, "Manage dama wannan yarinyar ce? ". Manager cikin girmamawa ya ce, "M. D, ita ce". Habib kallan manager ya yi ya ce, "Manager me za ayi mata? ". "Tom M. D, nima dai ban sani ba, amma idan na fahimce ta kamar bata da wajan zama ne". Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, "Dame za a tai maka miki? ". Hassana cikin sanyin muryarta mai cike da rauni ta ce, "Dan Allah aiki nake so kuban, sai kuma gurin da zan rik'a kwana". Manager kallan Oga Habib ya yi, sai yaga Habib ya d'auke idon shi akan shi. Hakan yasa manager ya ce, "Shikenan za ki rik'a mana swapping & mopping, morning &evening , zaki iya?" Manager ya kalli Hassana yana tambayarta. "Eh zan iya ". Cewar Hassana. Manager batare da tambayar Habib ba dan yasan in dai ya ce Habib zai tambaya, tom ba abin cewa zai yi ba, amma in ko ya riga ya yanke hukunci ya san sai dai ya yi mai tsiya daga baya. Hakan yasa manager ya ce, "Shikenan wajan kwana kuma sai ki rik'a kwana site d'in 'yan aikin gidan nan". Hassana cikin jin dad'in abin Manager ya ce, ta ce, "Nagode sosai, Allah ya saka maka da alkairi ". "Ameen". cewar manager. Manager Kallan Habib ya yi jin bai ce komai
Chapter 9 · 0% Book details