← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 78

Sashe 37

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana ko naganin Habib ya fad'i ta afka bedroom d'in Hajiya Turai ta rufe tana nishin wahala".

Habib ko ya d'an dad'e a kwance gun yana nishin wahala dan sosai ya fad'i dan gefan bakin shi sai da ya fashe".

Hajiya Turai ko ganin Habib bai tashi da wuri ba, da sauri cikin damuwa ta k'asaro inda ya ke kwance. Hajiya Turai na juwa ta kamo hannun Habib da niyyarta ta ta da shi. Habib naji ana tab'a shi ya tashi da sauri, ya nufi bedroom d'in Hajiya Turai inda yaga Hassana ta shiga, sai dai kashh, yana tura k'ofar ya ji ta kam-kam. Haka Habib ya tsaya sai bugun k'ofar ya ke kamar zai karyata".

Hajiya Turai gudin kar Habib ya jima kan shi ciwo ganin yadda ya ke bugun k'ofar ya sa ta tashi ta zo zata kama hannun Habib d'in, ya kai mata duka, da sauri ta kauce bai sa metaba, ta zauna tana mai tausayama d'an nata guda, tare da mai addu'ar Allah ya bashi lafiya, ya dawo mai da hankalin shi".

Habib ya dad'e gun yana wujijjiga k'ofar kamar zai karya ta, yana wani irin nishi. Sannan zuwa can ya kwanta bakin k'ofar , ya dad'e yana malele kuwa agun, sannan wani wahalallan bacci ya yi awan gaba da shi".

Hajiya Turai cikin tausayama Habib ta zo gaban shi ta zuk'unna tana kallan k'asan leb'anshi inda ya fashe fad'uwar da ya yi. Hajiya Turai tanan zuk'unne hawaye na zuba mata kad'an-kad'an na tausayin d'an nata. Hajiya Turai ta dad'e gun zuk'unne kusa da Habib sannan ta tashi, ta lek'a ta window ta hango Hassana kwance akan love chair d'in bedroom d'in, sai malele kuwa ta ke. Hajiya Turai magana ta yi a hankali gudin kar Habib ya ji, ta ce, "Daughter zo ki bud'e min".

Hassana tashi ta yi ta bud'ema Hajiya Turai k'ofar. Hajiya Turai ko bayan tashiga kallan Hassana ta yi da ke ta juye-juye tana cije baki ta ce, "Daughter yaji miki ciwo ko? ". Hajiya Turai ta fad'i maganar da alamun damuwa".

Hassana cikin cije baki ta ce, "A'a Mommy ". "Haba daughter me yasa zaki b'oyemin bacin gashiinan sai cije-cije kiki, bari in kira doctor ya duba minke".

Hassana rik'e wayar Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Mommy karki kira doctor dan Allah, nina san maganin nan ne irin narannan akasa a abincin nan, dan iri d'aya da yadda nake ji ayanzu haka".

Hajiya Turai cikin mamaki ta kalli Hassana ta ce, "Daughter magani kuma?, wani maganinin?, waya zuba muku maganin?".

Hassana da sai yanzu ta ankara da barin zancan da ta yi, shiru ta yi. Hajiya Turai ko kuma maimaitama Hassana tambayarta ta yi, ta ce, "Daughter kimin bayani mana kinyi shiru?, bangane ta kan maganganunki ba, waya zuba muku magani?, kuma maganin me akazuba muku?, karki damu kinji daughter yi min bayani nima nasan wasu abubun da ke faruwa, amma ba duka ba, fad'amin waya zuba muku maganin?".

Hassana cikin sanyin muryarta, ta ce, "A'a Mommy ba wai ina nufin anzubamana magani bane, amma dai irin yanayin da Oga Habib ya ke a yau, da irin wanda ya shiga kwanaki iri d'aya, kuma nima iri d'aya da wanda na tab'a shiga". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Shi maganin da ke magana wana irine? , kuma waya baki maganin?,".

Hassana cikin na tsuwarta ta cigaba da zuboma Hajiya Turai bayani kamar haka, "Mommy ranar da nafara ba Oga Habib maganin sha biyun dare, tom aranar Aunty Farida har na tafi sai ta biyoni da magani wai kince in sha in ba Oga Habib ya sha, sai na yi mamakin abinda Aunty Farida ta ce, jin harda ni, amma koda na tambayeta na ce, Aunty Farida ni kuma, sai ta ce min wai itama ta sha, kuma anba kowa yasha, wai ni na wane wannan zan sha, ta tsareni nasha agabanta, ta ban na Oga Habib in bashi, kafin in ba Oga Habib nashi maganin sai nake jina wani iri duk ba dad'i, kafin wani lokacin nakasa ba wanda taban inba Oga Habib. Washe gari ta ke tambayata wai me Oga Habib ya yi min nace mata ba komai ta ce min wai k'arya ne, nan dai da na rantse mata sai ta yarda, shine ta ce amma ban bashi maganin da taban ba in bashi, na ce mata Eh, amma yau zan bashi, nan tai ta min fad'a harda mari". Shiru Hassana ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, " kuma Mommy ranar da aka d'aura auran nan ma haka abin ya faru,ranar ma ta kawo min magani wai injiki in ba Oga Habib, tom Wallahi Mommy da nabashi maganin ranar ma baki gani ba, Allah ne yakwaceni daga hannun shi. Washe gari shima tazo tana tambayata wai Oga Habib ya kusan... ". Shiru Hassana ta yi dan sai taji maganar tayi nauyi, bazata'iya maimai kalar tambayar da Farida tai mata ba".

Hajiya Turai ko tun kusan farkon maganar Hassana ta fahimci maganin da Farida ke ba Hassana ta ba Habib , sai dai abin sosai ya d'aure mata kai, da mamakin dalilin Farida nayin hakan. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce,".Daughter daga yau kikina jina ko, kar wanda ya k'ara baki abu ya ce injini kiba Habib ki amsa ki ka yi amfani da shi". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "kin iya girki? ". "Eh Mommy na iya". "Tom daga yau gudin samun matsala ki rik'a muku girkinku acan, kar wani ko wata ya kuma baki abu ya ce injini, ki amsa ki yi amfani da shi batare da sanina ba, yanzu jeki watsa ruwa ajikinki, sai in kira doctor ya dubaki ".

Hajiya Turai Family doctor su ta kira ya duba Hassana. Magunguna kawai na kuzarin jiki ya bata, dan kafin yazo abinda ta ke ji ta ji sauk'in shi sakamakon ruwan da ta watsa. Hassana na fitowa Hajiya Turai ta bata wata abayarya ta saka, duk da ta yi ma Hassana yawa. Hassana na gama shiryawa ta tada sallar la'asar, tana idarwa a kan sallayar bacci ya kwasheta. Hassana ba ita ta farkaba sai gab da magriba ta tashi, tana tashi ta shiga toilet tai alwallar magriba. Hassana ta idar da sallar tana nan zaune kan sallayar Hajiya Turai ta shigo".

Hajiya Turai cikin damuwa ta kalli Hassana ta ce, "Daughter anya ko lafiyar Habib k'alau kuwa? , saboda tun d'azu fa bai tashi daga inda ya ke kwance ba". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin damuwa".

Hassana ma cikin sauri ta tashi daga kan sallayare tana mai nufar hanyar falon ta ce, "Mommy muje in gani?". Hajiya Turai bayan Hassana ta bi".

Hassana na zuwa ta durk'usa inda Habib d'in ya ke kwance, Hassana a hankali ta rik'a kiran sunan shi, tana cewa, "Oga Habib! Oga Habib!! Oga Habib!!! ". amma shiru.Hajiya Turai da tafa rasa na tsuwarta kuka ta fara yi".

Hassana ganin Habib ko motsi bai yiba, ya sa itama hankalinta ya fara tashi, hakan yasa ta sa hannu tana bugun bayan Habib d'in da d'an k'arfi, tana cewa, "Oga Habib dan Allah katashi mana". Hassana d'ago kan Habib d'in ta yi da ya ke ak'asa ta d'ora a kan cinyarta, tana mai cigaba da girgiza shi hankalinta a tashe".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter kawo min ruwa cikin fresh". Hassana tashi zata yi da niyyar d'akko ma Hajiya Turai ruwan, Habib ya rik'e Hassana ".

Daga Hassana har Hajiya Turai mamaki su kai . Hassana kallan Habib ta yi ta ga idonshi rufe ya ke, hakan yasa ta kira sunan shi, ta ce, "Oga Habib! ". Still idon Habib a rufe idan ka saurara zaka ji yana nishi kad'an-kad'an".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ko dai maganin nan ya yi mai 'illa ne? ". Shiru Hassana ta yi tana kallan Habib d'in da ke juya kan shi akan cinyarta da takwantar da kanshi. Hannu Hassana ta kai da niyyar ta garama Habib d'in kwanciya ajikinta, amma sai ta ji kanshi zafi rau. Hassana kallan Hajiya Turai ta yi da alamun damuwa ta ce, "Mommy Oga Habib baida Lafiya , ki tab'a jikinshi kiji zafi". Hajiya Turai tab'a jikin Habib ta yi taji zafi sosai, dan ko tab'a Habib d'in da ta yi kawai ya barta ta san ba lafiya, dan inda da da lafiyar shi ba kamar yau ba, ba ta isaba ta tab'a shi".

Hajiya Turai likitan da takira ya duba Hassana shi ta kira ya duba Habib. Yana zuwa ya yi ma Habib duk aune-aunan da suka kamata, amma shiru Habib bai hana ba, dai dai ya kallesu da ido sai ya koma ya kwanta. Likitan ko Magunguna ya je ya kawoma Habib d'in na zazzab'i da na ciwan kai. Babu yadda likitan bai yiba dan su d'auki Habib su mai dashi ciki amma yak'i, dan acewar likitan sanyin k'asan zai kara mai zazzab'in".

Bayan likitan yaba da Magungunan da za a ba Habib d'in ya tafi. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter tom ya zamuyi mai da kwanciyar k'asan nan? ". Hassana cirema Habib kan shi ta yi da ke kan jikinta. Tom dama da yake jikin k'ofar bedroom d'in Hajiya Turai suke ta yi sauri ta shige bedroom d'in Hajiya Turai".

Habib haka ya tashi yana layi kamar d'an k'waya ya bi Hassana. Hassana gudin kar Habib ya fad'o mata ta yi sauri ta kwanta kan gadon Hajiya Turai, dan tasan in ba haka ba, zai iya cewa zai kwanta kanta".

Allah sarki Habib bayan Hassana yabi ya kwanta, yana mai rik'e ta da d'ayan hannun shi. Hajiya Turai bayan su tabiyo".

Hassana ko naganin Hajiya Turai ta yi sauri ta yunk'ura ta tashi zaune, dan sai taji kunya sosai yadda Hajiya Turai ta ganta kwance kusa Habib ga shi duk ya wani kananna d'eta. Hajiya Turai maganin ta mik'ama Hassana ta ce, "Daughter ga maganin shi ki bashi, bari inje site d'in shi in d'akko mai rubutunshi ki bashi, yau dai banda na safe duk bai ma shaba". Hajiya Turai fita ta yi ta nufi site d'in Habib ta d'akko mai rubutun shi".
Chapter 37 · 0% Book details