Sashe 59
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Habib bayan yadan dara, kallan Hassana ya yi, ya ce, "kin ban dariya, me zaki da matsayin manager?". "Tom ai ni matsayin nake so, kuma ai kai kai min alk'awari kace duk abinda nake so, dan haka ni babu abinda nakeso wanda ya wuce, haka". Cewar Hassana tana turo d'an mitsitsin bakinta". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Kizab'i wani abun zan miki, amma banda wani abu a Sanat yughurt". "Ni dai acan nake so". Hassana ta fad'i maganar cikin shagwab'a".
Habib tashi ya yi, ya ce, "Shikenan kin rasa, ni kam bazan miki wannan ba". Habib na fad'in haka ya tashi ya nufi bedroom d'in shi".
Hassana da sauri ta tashi itama, tabi Habib tana rik'o hannun shi, ta ce, "Dan Allah Oga Habib kai fa kai min alk'awari!,". Hassana tana rik'e da hanun Habib tana mai magiya har suka shiga bedroom d'in shi. Habib zama ya yi, bakin gadon Shi, Hassana ma ta zauna tana mai k'ara cewa, "Oga Habib dan Allah kaban". Habib gaba d'aya baya jin dad'in yadda Hassana ke mai, shiya ya koma bedroom d'in shi, ya zaci bazata bishi ba. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Ki je ki kwanta, gobe sai muyi magana". "Wayyo Allah na Oga Habib, Allah ni bazan iya bacci ba, dan Allah kafad'amin yanzu". Habib kwanciya ya yi, ya rufe ido kamar mai bacci, dan bai san me kuma zai kuma cema Hassana ba". Hassana ma kwanciya ta yi, gefan Habib tana kallan shi, ta ce, "Oga Habib bacci kake? ". Habib juyawa ya yi batare da ya tankama Hassana ba, ya juya mata baya".
Hassana ma juyawa ta yi side d'in da Habib ya juya, ta ce, "Oga Habib dan Allah". Hassana ta fad'i maganar tana mai kara shigema Habib". Habib bud'e ido ya yi yana kallan Hassana, ya ce, "Banda lafiya ki je ki kwanta gobe zamu yi magana". Habib ya fad'i maganar da sanyi sosai".
"Ayyah sannu Oga Habib, Allah yabaka lafiya, tom kace Eh kawai dan Allah sai in tafi". Habib tashi zaune ya yi, ya na kallan Hassana , sannan ya ce, "Shikenan ki zama ma taimakiyar manager". Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "da shida Supervisor wane ya fi? ". "Naki yafi". Habib ya ba Hassana amsa". Wayyo Hassana dad'i kasheta. Rungume Habib ta yi tana mai jin dad'in matsayin da Habib ya bata. Ta ce, "Wayyo Oga Habib Nagodeee". Hassana sakin Habib ta yi, ta tashi ta fita daga d'akin".
Habib ko runtse ido ya yi, jin shi cikin wani bak'on yana yi. Yana mai jin sanyi cikin k'ofofin ji kinshi. Habib na nan yadda Hassana ta bar shi, Hassana ta shiga rik'e da jug d'in kunun Habib. Hassana cikin sanyi ganin Habib d'in kamar bai da lafiya da gaske kamar yadda ya ce, dan taga kamar yana ciccije baki, ta ce, "Oga Habib ga kunun ka, ka tashi kasha". Habib banza ya yi da Hassana sai da ta sake maimai tawa, sannan ya ce, "ki aje, kije ki kwanta idan na tashi zan sha". Hassana aje cup d'in kunin ta yi, sannan ta hau gadon, ta ce, "Oga Habib baka da lafiya ne? ". Habib cikin fad'a ya ce, "Ban sani ba, tun d'azu bikiji abinda nace bane, ki tashi kije ki kwanta! ". Hassana da sauri ta tashi tun Kafin ta idasa k'ure shi, dan tunnuni ma ta zaci zai mata haka".
Habib ko bayan fitar Hassana tashi ya yi ya je ya watsa ruwa, ko zai ji shi ya dawo yadda ya ke da. Bayan ya fito kunun da Hassana ta kawo mai ya samu yasha sannan ya kwanta yana ta juyi shi ka d'ai, ahaka dai Allah ya tai ma kai bacci ya kwashe shi".
Washe gari Hassana duk yadda taso ta tashi da wuri sai da ta makara, hakan yasa ta hak'ura da yin abin break fast, ta yi wankanta kawai tashirya. Hassana ta fito zata tafi Habib ma ya fito, Hassana cikin jin dad'in ganin Habib d'in ya ji sauk'i, ta gaida shi, tare da cewa, "Oga Habib kaji sauk'i kenan? ". Habib banza ya yi da Hassana, Hassana kuma kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib kura gemin hanya mana dan Allah ". "Akan me?, kije ki hau abinda kike hawa ya kai ki". "Ayyah Oga Habib kaga fa gidanmu d'aya dan Allah ". Habib banza ya yi da Hassana dama sunzo dai-dai motar shi, ya shige, Bilya ya ja zasu tafi, Habib ya ce yana zuwa ya yi mantuwa. Habib gida ya koma ya d'ako abinda ya manta. Sannan ya dawo suka tafi, tsaye suka iske Hassana tana jiran Napep. "Tsaya" Habib ya ce ma Bilya, bilya tsayawa ya yi,Habib kallan Bilya ya yi, ya ce, "Yi mata magana, tazo mu tafi".
Bilya sauka ya yi ya nufi inda Hassana ta ke tsaye. Ita kuma Hassana dama koda tai ma Habib magana akan yarage mata hanya ta yi mai ne, saboda idan shine tasan za tafi zuwa da wuri, kuma yau tana son taje da wurine dan ta fara cika aikinta yau, tana kuma addu'ar Allah yasa ta riga Farida zuwa, wannan ne da lilin da yasa Hassana ta rok'i Habib ya rage mata hanya".
Hassana na tsaye tana jan tsakin burinta ba zai cikaba, taji maganar Bilya, yana cewa, "Amaryar Ogan mu, ya ce, aimiki magana kizo mu tafi". Hassana hararar Bilya tafi sannan ta bishi suka tafi".
Hassana kusa da Habib ta zauna, tana kallan shi, ganin ya d'auke idon shi ya yi kamar bai san da ita ba, yasa itama ta yi banza da shi. Ahaka suka isa babu wanda ya yi ma kowa magana. Hassana na sauka da sauri ta yi ciki dan tana so taje ta gani Ko su Billy sun rigata zuwa".
Habib da mamaki ya bi Hassana da kallo yana mamakin saurin da take yi. Hassana ko na zuwa ta iske Billy ta zo, a wayance Hassana ta duba, ta ga Farida bata zo ba".
Hassana tafi hours biyu da zuwa sannan Farida ta zo. Hassana da ke zaune tana jiran zuwan Farida, Farida na zuwa Hassana ta tashi ta isa gunta, wani kallo Hassana tai mata, sannan ta ce, "dama wannan lokacinne ake zuwa Aiki? , tom ko mai Sanat yughurt tun d'azu yazo Aiki, dan haka bazamu laminci haka ba, mun baki suspection na One week, dan haka zaki iya komawa gida, nan gaba idan kika k'ara aikata haka, korarki za muyi". Farida tsabar al'ajabi ne ya hanata magana, kallan Hassana kawai ta ke, tunani Farida ta fara, tom ko anba Hassana wani matsayine, wata zuciyar ta ce mata, tsabar rainaki ne da tayi, ta yi ma Supervisor mana. Farida a zuciyarta ta ce, "Tabbas yau zakici ubanki, yau zaki tabbatar ni ba sa'arki bace"., Farida juyawa ta yi zata shiga ciki, "Hassana ta ce, "Zaki iya jama wadda kika shiga gurinta itama". Farida bangaje Hassana ta yi tashige ciki".
Farida Office d'in Supervisor ta shiga,Farida cikin damuwa ta ce, "Supervisor anba yarinyar nan wani matsayi ne? ".Supervisor kallan Farida ta yi, ta ce, "Wata yarinyar kuma? ". "Wata yarinya fa in ba Hassana ba! ". Cewar Farida ".
"Ai idan za aba wani matsayi a Company nan sai anyi meeting, da an bata da ke ma kin sani ai, ". Cewar Billy. Shiru Farida ta yi, sannan ta ce, " ke dai kikira manager muji, dan baki ga yadda tai min magana ba, wai ta dakatar dani na sati d'aya, kuma idan na k'ara ai kata haka korata za tai". Billy cikin masifa, kamar ita Hassana ta ce ma haka, ta ce, "Bari mu kira Manager awaya, yau dama ya ce min ba zaizo da wuri ba, amma inda ko karya take Wallahi yau sai ta san ita k'aramar mara kunya ce".
Billy kiran manager awaya ta yi, manager na d'agawa, bayan Billy ta gaida shi, ta ce, "Dama dearie naki raka ne in tambayeka, na ce anba Hassana matsayine agunnan, naga sai zuba iskancinta ta ke son rai". Manager ko tsabar dad'in dearie din da Billy ta kira shi da shi, ya sa ya ce, "Ki bar wannan yarinyar kawai zanyi maganinta, duk dan akwai auran M. D, kanta ne ta ke wannan iskancin, kuma shi bai d'auketa komai ba, danma shi mai biyayya ne ga Mahaifiyar shi, ki barni da ita zanyi maganinta".
Billy cikin jin dad'i ta kashe kiran, dama a speaker ta sa wayar Farida ta ji duk abinda manager ya ce. Billy kallan Farida ta yi, ta ce, "Muje mu sami shegiyar, Kafin manager yazo muci uban 'yar iska, haba ni dama nasan jin kan Oga Habib ne zai kula wannan, sai dai biyayyar kamar yadda Manager ya ce".
Hassana na zaune kan wata rubber chair, Farida da Billy suka zo suka sa meta, Farida kallan Hassana ta yi,ta nuna ta da hannu, ta ce, "Ke kikiyayi kanki dani, nifi k'arfinki nafi k'arfin iskan cinki, dan na girmi shekarunki, ni sa'arkice da zaki fad'amin abinda kika ce min d'azu? ". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "Tom da ke da wadda ta rakoki duk na dakatar da ku sai nan da sati d'aya, dan itama ba Aiki ta ke ba, akwai wasa a aikin nata, sannan kuma dama na fad'a miki".
Billy wani gigitattan mari ta wanka ma Hassana sannan, ta ce, "Shi wanda kike ta k'ama da auran shi, shi yaban matsayin da nake kai, shakarya mai tak'ama da abinda bata ita yake ba. Hassana tashi ta yi daga zau nan da take tana dafe da kuncinta, ta ce, "Masha Allah garani ko bata ni yake ba, da akwai abinda zanyi ta k'ama da shi, dan nasan hakan ma girma ne, akirani da matar Oga Habib, Allah sarki ku kuma dukkanku da kuke hauka akan shi, ko 'yan matan shi baza akiraku ba". Hassana na fad'in haka ta sa hannu ta wanke Billy da mari, ta rama marinda tai mata, sannan ta ce, "Ki ki ya yi kanki da harshanki Wallahi! ".Hassana bata rufe baki ba, Billy da Farida suka rufe ta da kuka kota ina, suna bugunta tana ramawa , amma ina hauswa sun ce sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, hakan yasa su Billy suka ci nasarar Hassana".