Sashe 54
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari daga Habib har Hassana makara su kai, Habib bayan ya gama shirinsa har zai tafi aiki, sai kuma ya yi wani tunani, fasa tafita ya yi, ya yi nocking d'in k'ofar Hassana".
Hassana ko tunda ta samu ta yi sallah ta koma ta kwanta, dan kanta ciwo ya ke mata sosai, bugun da akema k'ofar ta ne ya tadata, tana mai dafe da kai ta zo ta bud'e k'ofar. Hassana cikin sanyin ta gaida Habib ganin shi tsaye".
Habib bai amsa gaisuwar Hassana ba, sai cewa ya yi, "Karki sake kice zaki kira Hajiya ki fad'a mata abinda ya faru, sannan kuma dama dan Hajiya na nan ne na dakatar da ke zuwa aiki, dan haka ki koma aiki yau". Hassana da sauri ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib banda lafiya, dan Allah sai gobe". Habib tafiyar shi ya yi yabar Hassana nan tsaye ya ce, "kin dai ji abinda nace miki, ki zo aiki yau". Habib na fad'in haka ya bar Hassana nan tsaye shi kuma ya yi tafiyar shi".
Hassana ko tsayawa ta yi tana tunanin ta inda zata fara shiri dan ko a yanzu ta makara. Wanka Hassana ta shiga, tana fitowa ta shiga kitchen da sauri dan samarma kanta abinda zata ci. A falo Hassana ta ci karo da ledar kaya, tsayawa ta yi tana dubawa, atamfofi ne masu kyau sosai sun samu style masu kyau, sai dogayan ri guna na shadda guda hud'u dukan su duk gizina ne sai shampoo ,ka yan sosai suka burge Hassana, ko wanne da gyalan shi ahaka ta ka wo mata su. Hassana sosai ta ji dad'in ganin kayan. Cikin sauri Hassana ta had'a tea ta sha, sannan ta shiga wanka. Wata atamfa blue and brown color tasa, sai ta ya fa gyalan atamfar. Masha Allah sosai Hassana tai kyau. Tana fitowa ta samu Napep ta kaita har sanat yoghurt, lokacin 9:50Am. Ita da lokacin zuwanta ya ke 7:00Am".
Hassana koda ta je bata iske wani aiki ba, dan duk wani gu da take sweeping and mopping ta je ta iske duk anyi, hakan yasa ta je wajan su Amina tana taya su nasu aikin".
Amina kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana kina jin dad'in ki kinganki kuwa yadda ki kai kyau, sannan sai kinga dama kike zuwa aiki". Hassana Kallan Amina ta yi, ta ce, "Amina Wallahi ba laifina bane". "Tom kaifin waye? ". Cewar Amina".
Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Ke dai kawai awuce maganar". Dariya Amina ta yi, ta ce, "Anwuce".shiru Amina ta yi, sannan ta ce, "An d'auki wata aiki anan, ita ma dai daga ganinta irin supervisor ce, amma abinda ke ban mamaki tun ranar da ta fara zuwa aiki ta ke tambayarki, wai kinzo, kullum tazo sai ta tambaye ki". Hassana shiru ta yi, tana tunanin tom ita wayasanta, can dai tace, "Kila bani ta ke nufi ba". Zuwan Supervisor ne yasa Amina ta yi shiru ta ci gaba da aikinta. Supervisor ko tsaye ta yi tana kallan Hassana sannan ta ce, "Ke !, wannan dama shine aikinki? ". Hassana kallan Supervisor ta yi, ta ce, "A'a da yake banzo da wuri bane, lokacinda nazo kuma angama duk aikinda yake amazaunin nau". Billy sosai ranta ya b'ace da maganar Hassana, wato ita sai ta ga dama take zuwa aiki, sannan idan tazo sai aikin da taga gama ta ke yi".
Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ok, ki wanke duk wani toilet da ke wajannan". Hassana kallan Supervisor ta yi, ta ce, "kiban wani abun, amma bazan iya wankin toilet ba, saboda inada kyankyami ". Wani uban ashara Billy ta yi, sannan ta bar gun, direct Office d'in Maganar Billy ta je, tana zuwa ta kalli manager ta ce, "Manager ba fa zai yuwu ba, yarinyar nan sai ta ga dama take zuwa aiki, sannan idan tazo sai taga dama take aiki, aikinma in za tai sai ta zab'a, dan haka Wallahi yau dole ta yi abinda nasa ta".
Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Karki damu bari in mata magana da kaina zata yi".
Manager da kanshi yasa mu Hassana ya yi mata magana akan ta wanke toilet d'in da Billy ta sata. Hassana, "tom"tace ma manager saboda bata iya yi mai musu, haka Hassana ta wanke duka toilet d'in gun. Sosai ta gaji ga kanta da ke mata ciwo".
Yau Farida bata zo Sanat yughurt ba, koda su Habu suka jema Farida da labarin masu samu d'akko Hassana ba saboda harin da aka kawo musu, dan haka sai dai ta yi hak'uri, idan su kai aiki basu yi nasara ba basa kuma k'ara jarabawa, saboda gudin matsala".
Habib ko bayan ya tashi aiki police station ya biya akan maganar b'arin da suka shigar mai jiya, tare da amsar police biyu ya kai su gidan shi dan gadi, gudun matsala".
Bilya ne yaje ya d'akko Hassana bayan ya kai Habib. Hassana zaune ta iske Habib a falon yana cin abinci, azuciyarta ta ce daga gani dai nasiye ne".
Hassana tsayawa ta yi kamar ta wuce, sai kuma ta ga kamar hakan bai da ce ba, ta ce, "Barka da dawowa Oga Habib ". Habib d'ago kai ya yi kawai ya kalli Hassana ya koma yaci gaba da cin abincin shi".
Hassana kuma aje gyalanta ta yi ta shiga kitchen ta dafa indomie ta fito, har yanzu Habib na nan zaune, ya dai gama cin abincin. Hassana nesa sosai da Habib ta zauna. Tana cin indomie ta, tana satar kallan Habib da hankalinshi gaba d'aya ya ke akan waya. Can dai Habib ya tashi ya nufi side d'in shi. Hassana shiru ta yi tana tunanin yadda za ta iya kwana ita kad'ai, dan gani take daga ta kwanta b'arayin zasu k'ara zuwa. Sai da bacci ya fara kama Hassana , sannan ta daure ta nufi bedroom d'in ta ta kwanta. Haka Hassana ta samu bacci ya d'auketa tana cikin masifar tsoro. Can cikin dare Hassana taji k'arar bindiga cikin tashin hankali ta diru daga gadon ta fita d'akin da gudu, tana zuwa Allah ya bata sa'a k'ofar Habib a bud'e ta ke bai kulle ba. Hassana cikin tsoro ta haukan gadon Habib ta kwanta bayan shi".
Habib sai baccin shi ya ke kwata-kwata baiji shigowar Hassana ba".
Hassana ko ta dad'e cikin tsoro sai ta kai hannu zata tada Habib ta ce mai b'arayi sun dawo, sai ta tuna daga ta tada shi zai koreta d'akinta, hakan yasa Hassana ta bar Habib bata tada shi ba".
Habib ko bashi ya farka ba, sai asuba. Jin d'imin mutum bayanshi yasa ya juya. Habib da mamaki ya ke kallan Hassana dake baccinta abinta abayan shi, tunani ya farayi tom yaushema ta shigo d'akin, ya akai tazo bai ji zuwanta ba. Habib sauka ya yi daga gadon ya nufi toilet ya yi alwallah yazo ya tada sallah. Habib har ya idar da Sallah yana zaune kan dadduma Hassana bata tashi ba. Habib ta tashi ya yi cikin fad'a-fad'a ya ce, "Ke ". Hassana da sauri ta tashi zaune tana sosa kai tana kallan Habib, ta ce, "Uhm Wallahi Oga Habib b'arayi ne suka k'ara dawowa". Habib kallan Hassana ya yi, ya girgiza kai kawai , sannan ya nuna ma Hassana hanyar fita da hannun shi".
Hassana sakowa ta yi tafita. Habib kuma wanka ya shiga ya yi shirin aiki".
Hassana ma b'angaran ta ta gama shirinta tsab, Compound d'in gidan taje, dan tana son ganin Bilya. Aiko zaune Hassana ta iske shi cikin mota, yana jiran Habib".
Hassana lek'awa ta yi da kai ta ce, "Oga Bilya dan Allah ina son magana da kai". Bilya fitowa ya yi daga motar, ya ce, "Inajinki". "Oga Bilya dan Allah so nake kaima manager magana aban kud'in aikina, tunda na fara zuwa ba'a tab'a biyana ba, kuma yanzu amfani nake so inyi da kud'in ". Cewar Hassana ".
"Shikenan badamuwa zanma manager magana, zan amsa in baki". Habib tun daga nesa ya ke kallan Hassana da Bilya". Bilya kuma yana ganin Habib ya ce ma Hassana, "shikenan sai kin zo ga Oga Habib nan ya fito zamu wuce".
Bilya bayan ya kai Habib Office d'in manager ya shiga, ya yi mai maganar kud'in Hassana. Manager batare da gaddama ba ya d'akko kud'in wata hud'u yaba Bilya ya ce, gashi ka bata".
Hassana yau da wuri tai k'okarin zuwa aiki, tana sauka Napep Farida ma na sauka. Farida cikin jin dad'i tace shegiya ashe kin fara zuwa, ta yi maganar a zuciyarta".
Hassana da mamaki ta kalli Farida,sai ta d'auke kanta tashi ge ciki abinta.Farida ko da mamaki ta bi Hassana da kallo wata bazata gaida ni ba, zaki ci ubanki a gunnan yau".
Hassana na zuwa ta sweeping and mopping na gun baki d'aya kamar yadda ta saba. Tana gamawa ta samu gu tana hutawa, niyyarta inta gama hutawa ta je ta amshi kud'in da Bilya ya ce mata manager ya bata, ta yi amfanin da take son yi dasu".
Hassana na zaune tana hutawa sai ga Bilya da Farida sun nufo inda ta ke, suna nufota suna tattaunawa".
Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "me yasa nashiga toilet na gansu da datti baki wanke ba? ". Hassana batare da ta kalli Billy ba, ta ce, "Nayi aikin da yake ma zaunin nau, amma wankin toilet bashi cikin aikina". Farida ce ta amshe zancan da cewa, "Ke 'yar matsiyata zaki je ki wanke ne koko sai jikinki ya gaya miki? ". Hassana da mamaki ta furta, "duka kuma". "Eh ko bazaki bugu bane? ". Cewar Farida".
Dariya Hassana ta yi, sannan ta ce, "ko shi mai Sanat yughurt, wanda kuke aiki ak'ark'ashin nafi k'arfin duka agunsa, bare ku da kuke a k'ark'ashin shi... ". Marinda Farida tai ma Hassana ne yasa tai shiru".
Hannu Hassana ta d'aga da niyyar ramawa Billy ta rik'e hannun. Haka Farida da Billy suka taru sai bugun Hassana suke. Har hankalin staff ya kai kansu, ga manager baya nan. Da gudu d'aya daga cikin ma'aikatan ya ruga Office d'in Habib ya sanar da shi, ana fad'a".
Habib da dama tun d'azu yake jin hayaniya, tashi ya yi dan yasan manager baya nan, ya nufi inda ake fad'an".