Sashe 31
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farida ko cikin k'osawa da Hassana ta bata amsa, ta bugama Hassana tsawa ta ce,"Ke bada ke nake ba!, zaki tsaya kallona, nace lafiya naji kinyi k'ara ? ". Sana cikin son taka ma Farida ta ce, "Auntu Farida k'ara kuma?, anya kuwa ni ce". Gaban Farida ne ya fad'i, amma sai ta daure ta ce, "Ke bansan shirme,angaya miki banji bane, me yasa me ki kikai k'ara alokacin?, ko Oga Habib ne ya yi miki wani abun? ". Hassana kallan Farida ta yi, sannan ta ce, "Eh Aunty Farida na tuna, Oga Habib ya yi min wani abu". Farida cikin sauri da k'osawa, ta ce, "Me ya yi miki? ". "Aunty Farida glass Cup ya bugamin a kai". Farida cikin jin haushin abinda Hassana ta ce, ta ce, "Sannu, bayan nan fa be miki komai ba, danni naji k'ararki sosai, kina kiran Mommy da Bilya, dan haka fad'amin gaskiya ". Hassana cikin danne mamakin Farida da ta ke yi, ta ce, "Aunty Farida Allah bai min komai ba, k'arar da kikaji nayi zafin Cup d'in ne yasani k'ara, amma babu wani abu". Shiru Farida ta yi tana nazarin maganganun Hassana azuciyarta, sannan ta ce, "Na bani kaddai ace Oga Habib bai kusanci yarinyar nan ba! ".
Farida cikin rud'ewa ta kalli Hassana ta ce, "Ke kinko ba Oga Habib maganin da nace miki Mommy ta ce abashi? ".
"Eh Aunty Farida na bashi". "Kinfa bashi kika ce? ". Farida ta tambayi Hassana. "Eh Wallahi Aunty Farida na bashi".Farida cikin rashinsanin me ta ce, ta ce, "Amma kuma kika ce Oga Habib me biki komai ba". Hassana cikin mamakin Farida, da al'ajabin dama da akwai abinda ta k'ula kenan, ta ce, "Aunty Farida na ce miki ya buga min Cup mana". Wata irin tsawa Farida ta bugama Hassana, ta ce, "Dan Uwarki abinda na tambayeki kenan!, tom nufina Oga Habib bai kusanceki ba? ". Hassana cikin tashin hankali da al'ajabi ta ke kallan Farida, sannan ta ce, "Subhalallah Aunty Farida wannan kuma wata irin magana ce? ". Shiru Farida ta yi dan sai alokacin ta dawo hayyacinta ta tuna da irin tab'argazar maganar da tayi. Hakan yasa Farida cikin kame-kame, ta ce, "Eh dama da naji kinyi k'arane nayi tunanin haka, amma dai ai ba haka bane, bai kusance kiba ko? ". Hassana kamar zata yi kuka ta kalli Farida ta ce, "Eh hakane". Hassana na bata amsa ta juya zata tafi, dan sosai Farida ta b'ata mata rai, wato dama burinta kenan Oga Habib ya lallatamin tarbiya".
Farida ko cikin zafi ta jawo Hassana ta ce, "K'arya kike munafuka bakiba shi maganin ba, kuma Wallahi bazaki barnan ba sai naji dalilin da yasa baki bashi maganin ba yasha! ". Hassana da mamaki ta ke kallam Farida, sannan cikin sanyin muryarta, ta ce, "Aunty Farida ta ya kika san ban shi maganin ba, bacin na tabbatar miki da naba shi? ". Farida shiru ta yi sannan ta saki Hassana, gudin kar Hassana ta zargi wani abu".
Hassana harta tafi Farida ta kuma kiranta,ta ce, "Me kikaje yi part d'in Mommy ". "Maganin Oga Habib ta tambayan yasha". Hassana ta fad'ama Farida hakane, dan ita bata son Farida ta ji auranta da Oga Habib inda ance mata Farida na son shi".
Hassana tana tafiya tana mamakin dalilin Farida na ba Habib magani ya kusanceta, tom meyasa za tai haka?, inda dai ita son shi take, ai yakamata ace tana kishinshi, kai gaskiya k'ila dai tana da mugunnufi ne akaina, tom amma kuma shi Oga Habib d'in fa?, kuma ni mai nai mata?". Nan dai Hassana ta yi shiru dan babu mai amsa mata tambayoyinta".
B'angaran Hajiya Turai ko, Hassana na fita ta kira Bilya awaya. Bilya cikin mintina kad'an yazo".
Hajiya Turai kallan Bilya ta yi da murnarta ta ce, "Bilya dama yarinyar nan ce da kanta tazo ta ce min ta amince da maganar had'ata aure da Habib da Mukayi, tun shine dama nakiraka dan yau nake son d'aura auran idan kunfito sallar azahar ". Bilya kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Hajiya aure kuma, Yaushe akai maganar, ni dai gaskiya bansan da wata magana ba". Hajiya Turai da mamaki ta kalli Bilya ta ce, "Bilya maganar da mukayi jiya-jiyan nan amma kace min baka san da magana ba, bari in kira Baba Lami ta tunama". Hajiya Turai Baba Lami ta kira".
Bayan Baba Lami ta zo ne, Hajiya Turai ta kalli Baba Lami ta ce, "Baba dama maganar da muka yi da ku jiya na had'a Hassana da Habib aure, tom shine yanzu nakira Bilya Ina mai maganar dan yau nake son ad'aura auran shine ya ke cemin wai shi bai sanda maganar ba, shine nakiraki ki tunamai".
Baba Lami ma kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Hajiya ban fahimci maganarki ba, aure kuma,bangane ba, kimin bayani dama zaki had'a Oga Habib aure ne da.. .".
Hajiya Turai cikin b'acin rai ta ce, "Baba Lami bana son shirme, taya munyi magana daku yanzu kozo ku nuna min basu san magana ba, bacin ke cema kika kawo shawarar amma yau zaki nuna min baki sanda maganar ba, idan kuna ganin kamar cutar yarinyar mutane zanyi ai gara kufad'amin bawai ku nunamin baku san da magana ba".
Baba Lami kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Wallahi Hajiya da gaske nake bansan da maganar nan ba, sai dai ko Bilya k'ila da shi kuka yi". Bilya bud'e baki ya yi zai magana Hajiya Turai ta d'aga mai hannu ta ce, "Naji ya isa, ku tashi kufita kuban guri! ". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin fad'a, dan ita aganinta wannan raini ne, taya zasu yi magana, yanzu sununa mata basu san anyiba".
Bayan su Bilya sun fita Hajiya Turai tunani ta fara, "Tom ko dai su Bilya basa san aurane yasa suka had'a kai da Baba Lami su kai min haka, tom ni dai Allah kasani, banda yadda zanyi, banda wanda zai kulamin da Habib, inda baya yarda da kowa, dan haka Wallahi in da har yarinyar nan ta furta da bakinta ta amince, Manager zan kira in mai magana yashigarmin gaba ad'aura auran, yau-yau d'innan.
Hajiya Turai kiran manager ta yi awaya ta ce tana nai manshi dan Allah yazo yanzu".
To abinda ya faru, tunda Habib ya fara ciwo tashin hankali yasa Hajiya Turai bata iya cin abinci, sai dai abu mai ruwa-ruwa, shiyasa ko abincin da Balaraba ta girka mai magani Hajiya Turai bata ciba, tea ta sha,shiyasa abin ita bai yi aiki akanta ba. Wannan kenan ".
B'angaran Farida kuwa, Hassana na tafiya,waya ta d'akko ta kira Mahaifiyarta. Hajiya Murja na d'auka,Farida ta fasa kuka, ta ce, "Mommy nashiga uku, yarinyar nan bata bashi maganin ba, dan Wallahi Mommy be kusanceta ba". Daga b'angaran Hajiya Murja, shiru ta yi sannan ta ce, "Tom maganar auran fa, kinji sun k'ara magana". "A'a banji ba". "Tom shikenan ki zo yanzu sai mu koma gurin Malam, muji ya Akai haka ta faru, amma dan Allah Farida kibar kuka, wai bani nai miki alk'awarin auran nan baza ayi shiba, kumama kince baki ji sunsake tada maganar ba, tom duk da hakama babarin maganar zamuyiba, kizo yanzu ki saman mu tafi gurin Malam".
Farida mayafinta kawai ta d'akkko takama hanyar tafiya wajan Mahaifiyarta.
Kasan cewar banisa tsakaninsu sosai, hakan yasa cikin lokaci Farida ta isa.Dama Hajiya Murja ta shirya Farida kawai ta ke jira, hakan yasa Farida nazuwa, suka tafi".
Hajiya Murja da Farida zaune a gaban Malam mai biyan buk'ata dole. Hajiya Murja bayan ta gaida Malam boka, cikin girmamawa ta ce, "Tom Malam mai biyan buk'ata dole, yarinyar nan fa, munajin haryanzu tak'i ba yaron maganin, ga guri sai k'ara k'urewa ya ke, dan Allah nidai atai makan, ayi wani abu malam". Hajiya Murja ta idasa maganar cikin rok'o".
Malam mai biyan buk'ata dole, wani k'ok'o ya d'akko, sannan ya kalli Hajiya Murja ya ce, "zoki gani da idonki Hajiya". Hajiya Murja da Farida da sauri suka kango kansu dan ganin abinda ya ke nuna masu".
Cikin al'ajabi Farida da Hajiya Murja suke kallan k'ok'an. Hassana ce rik'e da maganin da ta ba Habib. Ata kaice dai haka su Farida sukaga abinda ya faru tsakanin Hassana da Habib bayan ta bashi maganin, haka suka kallah kamar, T, V, ".
Farida cikin takaici, ta ce, "Shegiya wato toilet dama ta shiga ta b'oye, amma yanzu malam ya za ai, kuma ya maganar auran da suke so su had'a?, dan munriga mun basu maganin sunci, dan wanda mukaba maganin ta zuba ta tabbatarmin ta zuba". K'ok'an da ya nuna masu abinda ya faru tsakanin Hassana da Habib, shi ya k'ara d'akkowa, ya ce, "Zuku gani da idonku abinda ya faru". Farida da Hajiya Murja lek'a k'ok'annan suka k'arayi, sai ga foton Balaraba ya bayyana lokacinda ta ke zuba maganin a abincin. Daga nan kuma sai lokacinda ta rarraba abincin ta kaima Baba Lami da Bilya, sai kuma ga wani ta d'akko ta nufi site d'in Hajiya Turai. Balaraba na zuwa cikin girmamawa ta ajema Hajiya Turai abincinta. Balaraba har ta juya zata tafi Hajiya Turai ta kirata ta ce, "Balaraba zoki d'auki abincin nan bana iya cin komai yanzu, garama abu mai ruwa, nakan iya daurewa insha".sai ga Balaraba annuno ta d'auki abincin ta fita da shi. Daga nan Malam mai biyan buk'ata dole ya kauda k'ok'an. Kallan Farida ya yi, ya ce, "Tom kinji abinda ya faru, ita Wanda ke da ruwa da tsaki a maganar bataci maganin ba. Yanzu su wa'inda sukaci maganin kuzo ku gani". K'ok'an ya k'ara kanga musu. Sai ga Hajiya Turai da Bilya lokacinda ta ke mai maganar auran Hassana da Habib , ya nuna shi kwata-kwata bai sanda maganar ba, suna ganin lokacinda Hajiya Turai ta tashi ranta b'ace ta kira Baba Lami, tana mai-mai ta mata maganar auran, nan itama ta nuna ma ta bata san da maganar ba. Daga nan Malam mai biyan buk'ata dole, ya kauda k'ok'an, ya ce, "Tom Hajiya kunga abinda ya faru, wato ita Uwar yaron da kusan dan ita akai, bataci abincin ba, kuma yanzu haka ta kira wanda zai shigar mata gaba ad'aura auran".