← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 78

Sashe 17

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilya ko yadawo bakin aiki, saboda Hajiya Turai na dawowa tasa Habib ya dawo da shi. Habib da sauri ya fito domin tafiya gida baya son magriba ta sa mai anan. Bilya ko dama yana ganin time d'in tafiya gidan Habib ya yi, ya shiga motar yana jiran fitowar Habib. Hakan yasa Habib na shiga Bilya jaya motar suka kama hanya. Bilya tsaye ya hanki Hassana can gefan titi daga gani abin hawa ta ke jira. Bilya Kallan Habib ya yi, ya ce, "Oga Habib dan Allah ga Hassana can ko zamu rage mata hanya? ".Habib banza ya yi da Bilya. Bilya ko jin Habib ya yi banza dashi yi tunanin ko be ji abinda ya ce bane, hakan yasa ya k'ara cewa, "Oga Habib ga Hassana can na ce, dan Allah ko murage mata hanya? ". Habib tsaki ya ja alamun Bilya ya da mai, Bilya ko najin haka ya kama bakinsa yayi shiru. Bilya yana ji yana gani suka wuce Hassana tsaye badan yaso ba, sai dan bashi da yadda zai yi. Habib sai da ya yi Sallar magriba sannan ya shiga site d'in Mommynsa. Habib na shiga ji yayi kamar ya juya ya koma, sai dai bashida yadda zai yi tariga ta ganshi, hakan yasa Habib ya kuma tamke fuska ya shiga falon.Farida da saurinta ta tashi zata yi welcoming d'in Habib. Habib hannu ya d'aga ma Farida. Farida ja tai tatsaya tana Kallan Habib kamar za tai Kuka, ta ce, "Broz Habib kana nufin bakai murnar ganinaba? ". "Yess ". Cewar Habib. "Farida bana murnar ganinki saboda shirman da kike min". Farida Kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Mommy kinji fa abinda Broz Habib ya ce, wai baya murnar ga nina". Farida ta fad'i maganar kamar zata yi kuka. Hajiya Turai hannun Farida ta kamo tana murmushi ta ce, Farida rabu da Habib shi bai san wacece Farida bane"., Habib ko ji yayi ba zai iya jure zama ba afalon Hajiya Turai hakan yasa Habib Kallan Momynsa ya ce, "Mommy zan shiga ciki ki bada tea akawomin". Hajiya Turai Kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib gobe zan wuce, jirgin safe zan hau". Habib Kallan Hajiya Turai ya yi , cikin damuwa ya ce, " Kai Mommy wannan karan kin koma da wuri".murmushi Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Habib kamar kana da damuwa Allah kalli face d'in ka ? ". "Babu abinda ke damuna Mommy". Habib na fad'in haka ya wuce. Habib falon shi ya je yana jin wani iri acikin jikin shi, amma yarasa gane shikan shi me ke damunsa. Habib na nan kwance Farida ta shigo rik'e da tea a glass cup. Habib bai cika cin abinci ba da daddare sai dai yasha tea. Farida har inda Habib ya ke , ta k'araso, tea d'in hannunta ta mik'ama Habib ta ce, "Broz Habib gashi in ji Mommy ta ce kasha dan Allah badan ni ba".Farida ta yi hakane saboda tasan da wuya Habib ya sha tea d'in. Habib amsa ya yi ita kuma Farida ta fita dan bataga fuskar zama ba. Habib haka ya ke jin shi wani iri ahaka ya samu sha tea d'in. Yana gama sha ya tashi ya yi Sallar issha'i sannan ya kwanta, dan sosai ya ke jin jikin shi ba dad'i, bakamar brain d'in shi ba tana mai ciwo sosai, haka dai Habib ya samu wani wahalallan bacci ya kwasheshi.
Washe gari tun asuba, Hajiya Turai taima Habib magana, ya shirya dan seven o'clock Am, ta ke son tafiya. Habib tashi ya yi badan wai yaji sauk'in yadda ya ke ji ba, wanka ya yi, ya yi shirinsa Cikin wata dark blue suit. Habib mota ya zauna yana jiran fitowar Hajiyarsa. Hajiya Turai da Farida suka fito Farida na rik'e da jakar Hajiya Turai. Hajiya Turai amsar jakarta ta yi hannun Farida ta ce, Farida ki koma gida. Farida ba Hajiya Turai ta yi saboda bata so tana mata musu. Bayan Hajiya Turai ta shiga motar, kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ko dai zuwan Farida ne yasa naganka haka so silent". Habib kallan Mahaifiyarsa ya yi, ya ce, "Mommyna bashi bane, nima haka na ke jin jikina duk babu dad'i, ga jiya nayi wani mafarki da yaban tsoro sosai, amma karki damu nayi addu'a, kuma yanzu normal na ke jina". Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Shikenan Habib, amma dan Allah kaje Hospital ka yi check up, dan Allah Habib na sanka da shiririta". Habib ganin Hajiya Turai ta damu, yasa ya kalleta yana murmushi, ya ce, "Mommyna normally fa nake jina yanzu, karki damu yanzu daga na kaiki airport zan je ganin likita". Habib action ya rik'ayi kamar mai lafiya, dan yasan in ya nuna ma mommysa ba ya jin dad'in jikinsa tom bazafa tatafi ba. Koda Habib ya kai Hajiya Turai airport. Hajiya Turai rak'on Habib ta yi sosai akan ya je Hospital aduba shi, nan dai Habib ya yi mata sallama ya nufi sanat yoghurt Company".

Habib na zuwa Office d'in shi ya shiga, Habib na shiga ya kira Bilya awaya, ya ce, "Hello, Bilya ina sanat yoghurt, ka biya restaurant d'in kusa damu ka tahomin da abin break fast". Habib na fad'in haka ya katse kiran.
Bilya ko lokacin da Habib ya kira shi tashinshi a bacci kenan, hakan yasa Cikin sauri Bilya ya shirya yaja motar shi yafita. Da safe da kuma dare Habib tea kawai ya ke iya sha, sai wainar k'wai. Bilya na shiga Sanat yughurt , ana sauke Hassana ita kuma a napep. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce "Yauwa Hassana dan Allah amshi break fast d'in nan ki kai Office d'in Oga Habib. Hassana tsayawa ta yi tana kallan Bilya ta ce, "Oga Bilya dan Allah ka kaimai da kanka Allah bana son shiga office d'in Oga Habib. Bilya mik'ama Hassana ya yi, ya ce, "Hassana haka nan zakiyi Hak'uri ki amsa, tun d'azu Farida ke kirana in zo in kawota Sanat yughurt, Wallahi na manta sham sai yanzu na tuna, tom shine ke so inje in d'akkota, yanzu idan na shiga office d'in Oga Habib zai iya sani wani abun, ba zai barni in fito yanzu ba, dan Allah ki amsa ki kai mai". Hassana amsa ta yi ta ce, "Haba Oga Bilya, ai Umarni zaka bani na aikata ba sai ka rok'eniba". Dariya Bilya ya yi ya ce, "Bakomai Hassana girmanki ne, bari in je in dawo dama Wallahi ina son wata magana mai mahimmanci da ke". Hassana itama murmushin ta yi tace, "Tom Oga Bilya sai kadawo". Bilya tafiya ya yi Hassana kuma tana rik'e da break fast d'in Habib ta nufi office d'in shi".

Hassana nocking ta yi. Tad'an dad'e atsaye tana nocking sannan Habib ya bata izinin shiga. Hassana na zuwa Cikin girmama ta ce, "Barka da safiya Oga Habib ga shi inji Oga Bilya, ya ce yanzu zai dawo". Habib batare da ya amsa gaisuwar Hassana ba, dan zuwa yanzu sosai ya ke jin ciwo acikin jikin shi. Habib kallan Hassana ya yi, sai zuwa can ya tashi kamar zai amshi jug d'in hannun Hassana, sai kuma ya fasa, ya dafe kanshi da hannun shi guda d'aya ya mik'ama Hassana d'ayan hannun nashi, yana rin tse ido, ya ce da k'arfi dan har wanda ke waje sai da yaji. "Ahhhh rik'e min hannunaaaa!!? Habib ya fad'i maganar da k'arfi yana mik'ama Hassana hannun shi. Hassana sosai ta tsorata, Hakan yasa ta saki jug d'in hannunta ta bud'e k'ofar Office d'in zata fita. Sai dai ina ta makara kafin ta bud'e kofar sai dai taji anjawo hannunta da k'arfi.....................

A'A, WAI ME KE FARUWA NE?, NI FA BANGANEBA.

NASAN WASINKU DA DAMA ZASU CE HAKA.

KARKU DAMU ZAKU GANE.

LABARIN YANZUN YAFARA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

BANDA LAFIYA DAN ALLAH INA BUK'ATAR ADDU'ARKU.

COMMENT
&
SHERE
PLEASE 🙏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI ( Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
🍃 Ibnul-Qayyim (Allah Yayi masa Rahama) yana cewa: *"Lalle damuwa, baƙin ciki da qunci suna faruwa ne ta dalilai guda biyu: _Daya daga cikinsu shine son duniya da nemanta (ta kowace hanya), na biyu kuma rashin aikata ayyukan kwarai da (kyautata) ibada"_*
📒 [Iddatus-Saabireen - P. 265].
Allah kasa mu dace.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 18&19.

Hassana sosai ta tsorata, hakan yasa ta saki jug d'in hannunta ta bud'e k'ofar Office d'in zata fita, sai dai ina ta makara kafin ta bud'e k'ofar sai dai taji anjawo hannunta da k'arfi, an dawo da ita baya. Hassana cikin tsoro ta d'aga kai tana kallan Habib".

Habib ko rik'e hannun Hassana ya yi da k'arfi da d'ayan hannunsa, d'ayan hannun kuma ya dafe kan shi da shi.
Hassana da Habib kusan atare suka yi k'ara wadda duk kusan wanda ke cikin Sanat Company babu wanda bai ji k'ararnan ba".
Chapter 17 · 0% Book details