← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 78

Sashe 50

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida ko ai ko saurarar Habib ba ta yi ba, ita dai so take kawai ta caka ma Hassana wuk'ar. Habib k'ok'arin kwace wuk'ar ya yi amma ya kasa, aiko cikin haka Allah yaba Farida sa'a ta yanki Hassana a hannu".

Wata uwar k'ara Hassana ta yi, tana cewa, "Wayyo Oga Habib ka rik'eta, zata kasheni Wallahi".

Farida ko yankar da taima Hassana ba tai mata ba so take ta caka mata wuk'ar. Habib ingije Farida ya yi, sannan ya bita ya cigaba da kwad'a mata mari kota ina, yana cewa, "Baki da hankaline, yankar da kikai mata bai miki ba, kasheta kike so ki yi, tom idan kika kasheta kina ganin za a kyaleki ne?, iyye! ".

Habib yin kanshi ya bar marin da ya ke ta aikama Farida shi, sannan ya samu gu zauna, mai da kallan shi ga Hassana ya ji, jin tsantsar ihunda da take tana yarfe hannu, ga jini sai zuba ya ke sosai, dan sosai Farida ta yanki Hassana ".

Habib tashi ya yi ya nufi inda Hassana ta ke tana yarfe hannu tana kuka. Habib na zuwa hannun Hassana ya kamo yana dubawa ganin yadda jini ke zuba".

Habib tsawa ya yi ma Hassana ya ce, "Da Allah can kima mutane shiru, sakarya kawai, mara hankaki".

Hassana k'asa tai da kukanta tana mai ci gaba da yarfe hannunta. Habib waya ya yi da Family doctor su ya ce yazo yanzu da first aid box, an yaki wata yarinya a hannu ".

Aiko cikin minti goma likitan ya iso, wankema Hassana hannun ya yi, ya nad'e inda aka yanka da bandage".

Habib ranshi b'ace ga yunwa da yaje ji, bayan likitan ya tafi ya kalli Hassana, ya ce, "ke wata irin fitinanniya ce, yau da mutum biyu kenan ki kai fad'a, na gaji da ganinki, fitinanniyar yarinya kawai". Hassana da sosai ta ji zafin kalaman Habib, hakan yasa ta ce, "Nima dalili d'aya yasa nake zaune nan, kuma shima naci gaba da zama ne dan rok'on da Mommy tai min kar in tafi da aure kaina, amma Wallahi badan shiba nima nagaji! Nagaji!! Nagaj... ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce yasa ta yi shiru".

Habib tashi ya yi yana nuna Hassana ya ce, "Wallahi! Wallahi!! Wallahi idan har kina hauka tom ki ki yaye, ki rik'a lura da wanda kike magama , naga kina tak'ama da rashin hankali, amma zanyi maganinki!. ".Habib na kaiwa haka ya juya zai fita. Hassana ko shiru ta yi, dan ta tsorata da gargad'in Habib".

Farida ko da k'arfinta ta ce, "Oga Habib baka jiba?". Habib da wowa ya yi yana kallan Farida alamun Ina jinki, ta ce, "cewa ta yi wai ita bata tab'a hauka ba, da zaka kiramata rashin hankali".

Habib wai gowa ya yi yana kallan Hassana. Hassana ko naganin haka, ta juya da gudu ta shige bedroom d'in ta, taja zata rufe Habib ya tura da k'arfi".

Habib na shiga Hassana ta ce, "Oga Habib tsaya kaji dan Allah, Wallahi Allah k'arya take min Wallahi ni bance haka ba, tana jin haushine dan ta sani in dama mata kunu, nace mata yau banda lafiya ta bari sai gobe, Allah ni bance abinda ta ce ba, tana jin haushina ne tai min shairi". Habib shiru ya yi yana kallan Hassana, yana tunanin dama ba Farida ke dama mai kunu ba. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "k'arya kike Ina kika iya dama kunu". "Allah na iya, koma lakacinda Ina zaune part d'inka aini ke damamana". cewar Hassana".

Habib shiru ya yi dan baya son abinda za a tuno mai maganar haukar da aka ce ya yi, abin yana tab'a zuciyar shi sosai".

Habib fita ya yi yabar Hassana, Habib na shiga part d'in shi ya kira Hajiya Turai a waya amma bata d'aga ba, hakan yasa ya tura mata text kamar haka.".

"Mommy ki yi hak'uri ba zan iya zama da yarinyar nan ba, dan haka gobe insha Allah zan sallame ta, kullum cikin fad'a da muta ne ta ke. Nagaji da rabo Mommy ".

Hajiya Turai da ta duba text d'in Habib, tana gani ta kira Habib d'in, aiko kira d'aya ya d'aya Hajiya Turai ta ce, "Habib nima dama nagama duk wani shirina da nake yi, dan haka ka sauraran gobe zan dawo".

Habib cikin jin dad'in albishir d'in Hajiya Turai, ya tashi ya shiga kitchen ya had'a makan shi tea, yasha".

Washe gari Hajiya Turai, jirgin faro ta biyo, dan taji duk abinda ya faru tsakanin Hassana da Farida".

K'arfe sha biyu na rana Hajiya Turai ta iso, Bilya ne ya je ya d'akko ta.
Habib ko dama yau bai fita aiki ba".

Bayan Hajiya Turai ta huta ta , ta kira Habib, da Hassana da Farida, a Falonta, dan acewarta ta gaji yau zata yi ta ta k'are".

Hajiya Turai , shiru ta yi, tana nazarin maganar da ta ke son fad'a, sannan zuwa can, ta ce......... ✍️

Nifa bangane ba?, wai me hajiya Turai ki shirin cewa ne? 🥺🥺🥺.

Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Shafi na 60&61.

Hajiya Turai shiru ta yi, tana nazarin maganar da ta ke son fad'a, sannan zuwa can, Hajiya Turai ta kalli Farida ta ce, "Farida me ya had'aku keda Daughter wanda zai sa ai fad'a harda wuk'a? ". Farida kamar wadda ke jira Hajiya Turai ta tambayeta ta fara zubo zance kamar haka, "Mommy tunda kika tafi nike damama Oga Habib kunu, tom jiya banda lafiya, gashi kuma Oga Habib har yazo da kanshi ya yi min maganar dama kunun, tom shinefa sai nai ma wannan yarinyar magana". Farida ta nuna Hassana da hannu. "Na ce mata dan Allah zan nuna mata yadda akeyi ta damama Oga Habib kunun, shikenan fa Mommy daga magana wai ai ita ba baiwarshi bace, ta yi bauta da shi alokacin da ya ke hauka , yanzu koma ba zata iya yi ba , kuma duk abinda tai abanza wai keda Oga Habib baku gani". D'an numfasawa Farida ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Mommy wannan maganar da ta fad'a akan Oga Habib ita ce ta tafasamin zuciya ,nai mata magana, karta kuma kirama Oga Habib hauk.... ".

Tsawar da Habib ya yi ma Farida ce tasa ta yi shiru, zuciyarshi har wani zul-zul ta ke idan ana maganar ya yi hauka. Hajiyar Turai sosai ranta ya b'ace da kalaman Farida, bakamar da ta juya ta kalli Habib ba, taga yadda idonshi ya kad'a ya yi jawur, kuma tasan ya yadda da kalaman Farida".

Hajiya Turai mai da kallanta ga Hassana ta yi, yadda ta yi tsuru, daga gani dai itama cikin tashin hankalin k'aryar da Farida tai mata take".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter me ya had'aki da Farida? ". Hassana cikin natsuwa da sanyin muryarta, ta fara ma Hajiya Turai bayani kamar haka, "Mommy kullum idan Oga Habib yasa Aunty Farida ta dama mai kunu, ni Aunty Farida ke sawa in dama, ban tab'a yima Aunty Farida musu ba sai jiya, shima saboda banda lafiya ne, nace mata bazan iya damawa ba, Aunty Farida tai ta zagina ta uwa ta uba, wai dole sai na dama shi, sai banji dad'in zagin da ta ke ma Babana ba kodan ya mutu, sai nai mata magana, ta kuma zagin shi, ni kuma nace inda haka ne bazan dama kunun ba, shine fa ta kama jana wai sai na dama shi, tana kuma zagina, ni kuma na tureta, daga nan muka kama fad'a ta d'akko wuk'a wai sai ta kasheni, Allah bai bata sa'a ba shine ta yankan, wannan yankar da kika gani Mommy ". Hassana ta fad'i maganar tana nuna ma Hajiya Turai yankar hannunta".

Hajiya Turai shiru ta yi, dan dama ita ko bata ji ta bakin Hassana ba, tasan Farida ce bata da gaskiya".

Hajiya Turai kallan Farida ta yi, ta ce, "Shikenan Farida ta shi ki shiga ciki, Hassana kuma insha Allahu daga yau zamanta yak'are a cikin gidan nan". Farida cikin farincikin da ta kasa b'oyewa ta d'ago kai tana kallan Hajiya Turai ta ce, "Nagode Mommy ". Sannan Farida ta tashi ta yi kamar ta shiga side d'in ta, ta lab'e dan jin abinda Hajiya Turai za taima Hassana ".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ki yi hak'uri kinji, nasan ban kyauta miki ba, na yi miki alk'awari ban cika miki ba, na tafi, tom a gaskiya na tafi ne alokacin saboda bazan iya raba auranki da Habib ba, kuma banyi niyyar dawowa yanzu ba, amma jin labarin fad'an da kukai da Farida jiya yasa nadawo, saboda nasan hakan na iya k'aramiki tsanar zaman gidan. Wato jiya da nadawo na dawo ne dan in cika miki alk'awarin da nai miki daughter, amma da na zauna nayi tunani sai naga shi kanshi auranki da Habib Allah ne ya k'ulla shi bani ba, me yasa Habib da yafara ciwo bai yadda da kowa ba sai ke, wato kenan Allah ya tsara aure a tsakaninku ne shi yasa k'addarar ta fad'a kanki". Shiru Hajiya Turai ta yi, na d'an wani lokaci, sannan ta kalli Habib, da yake zaune babu alamun fara'a a fuskar shi, kai daga kaganshi kasan bayajin dad'in yanayin".

Hajiya Turai sunan Habib ta kira, ta ce, "Habib! ". Habib kallan Hajiya Turai ya yi gaban shi na fad'uwa, dan shi abinda ya k'osa ya ji, ya ji Hajiya Turai ta ce ta da tse auran shi da Hassana".

Hajiya Turai, ta kuma cewa, "Habib, ada nayi niyyar raba auranka da daughter, amma ayanzu na fasa saboda wasu da lilaina, sannan auranka da ita wani rubutancan al'amarine, dan haka na soke maganar raba auranku, Ina fatan da ga kai har Hassana zaku min biyyya akan k'udirina? ". Habib shiru ya yi bai tan kama Hajiya Turai ba, sai zuwa can, ya fara magana cikin wata irin murya ".
Chapter 50 · 0% Book details