Sashe 64
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Billy kallan manager ta yi, ta ce, "ka tabbata dearie? ".murmushin magana ya yi, sannan ya d'aga ma Billy kai, Billy cikin jin dad'i ta tashi ta fita".
B'angaran Habib ko yana zaune a Office d'in shi Hassana ta shigo da fara'arta tana zuwa ta idasa inda Habib ya ke zau ne. Babu zato babu tsammani sai dai Habib ya ji Hassana ta rungume shi, ta ce, "Oga Habib nagode, naji dad'in matsayina da ka bayyana agaban staff's, nagode dear.. ". Hassana saurin rufe bakinta ta yi, ta saki Habib zata gudu, dan sukubutar bakin da ta yi".
Habib jawo Hassana ya yi, ta dawo ya rik'e ta ya ce, "Mai-mai ta abinda kika ce". Habib ya fad'i maganar yana kallan Hassana. Hassana hannu tasa ta rufe idanta, ta ce, "Nifa babu abinda nace".Habib hannu Hassana ya rik'e yana burzawa. Hassana ihu ta fara, tana cewa , "Wayyo Oga Habib da zafi Allah! ". "Tom mai-mai ta abinda kika ce". Cewar Habib ".
"Tom naji sakar ni in mai-mai ta". Habib sakin Hassana ya yi, aiko yana sakin ta ta ta gudu".
Habib jin kina ya yi da chair d'in da ya ke zaune kanta, idon shi rufe, ya na mai-mata abinda Hassana ta ce,ya yi murmushi, sannan ya ci gaba da abinda ya ke".
Hassana tana fita Office d'in Habib ta wuce wajan koyan girkinta, ba ita ta dawo ba sai la'asar, tana dawowa ta je kan rubber chair ta sauna tana kallan staff's d'in sai aikin su suke, Hassana na nan zaune taga fitowar Farida daga Office d'in Billy. Farida ta zo dai-dai inda Hassana ta ke zata wuce, Hassana ta ce, "Farida me ya shigar da ke Office d'in ca muna tsakiyar aiki? ". Farida da mamaki ta kalli Hassana, sai tai murmushi ta ce, "Zan shiga duk inda nake so a Company nan a duk lokacin da naso, gargad'i na k'arshe kar ki kuma shiga safgata, idan ba haka ba, zan b'atar da ke da ta rihinki, acikin Company'nan". Hassana ta shi tai tsaye, tana kallan Farida dan ta bar shakkarta, ta ce, "Ni kuma ina miki albishirin zanyi amfani da da mata na koreki a Sanat company, ko kin san dan ke na amshi matsayin nan, ba zan tab'a barin Sanat ba sai naga bayanki, mu zuba ni da ke! ".Farida dariya ta yi, jin abinda Hassana ta ce, ta ce, "Aiko in dai danni kika amshi matsayin nan, ina mai tabbatar miki kinyi aikin banza, dama kin tsaya a share-sharanki da wankin toilet da yafi miki, dan ni Farida nafi k'arfin ko ruwa a gurin mutum k'askantaciya irinki, wadda bata da asali!, ni ba Sanat kad'ai zan kore ki ba, har gidan Oga Habib sai nayi amfani da basira na koreki". Sakarya mai aiki a titi babu Office! ". Farida na fad'in haka, ta bar gun kafin taji abinda Hassana zata kuma cewa".
Hassana ko zama tai agun tana mai-mai ta maganganun Farida azuciyarta, tabbas sai nayi amfani da matsayina agun nan na mataimakiyar manager Farida na koreki gurin nan. Hassana ta dad'e zaune agun, sannan ta ta shi ta shiga office d'in manager ".
Magan-ganun da Hassana ta ji anayi ne a Office d'in manager ya hana ta shiga, manager ne taji yana cewa, "Farida naji duk abinda kika ce, wato ta amshi matsayi ne dan ta kore ki aiki a Company, kar ku damu ku dai ku ban nan da lokaci kad'an, sai tabar Sanat yughurt da k'afafunta, na san yadda zan mata.... ". Hassana ji tai baza ta iya jure sauraro ba kawai ta banka Office d'in ta shiga. Hassana tsayawa ta yi tana kallan su d'aya bayan d'aya, sannan ta kalli manager ta ce, "Manager ada ina maka kallan adali, amma kuma a yau ina maka wani rin kkallo wanda ban san ya zan kira shi ba, sai dai ina mai mu ku albishir daga kai har su buku isa kusa in bar Sanat ba, sai dai ni in barta alokacin da naso". Hassana shiru ta yi, sannan ta ce, "Manager nazo ne ka ban Office ". "M, d bai fad'i a baki Office ba alokacin da ya baki matsayi". Cewar manager ".
Hassana juya wa tai zata tafi, Farida ta rik'o hannun ta ta ce, "Ji mana, kina tunanin zaki iya karawa da mutum uku ko?, Yaro man kaza bai san wuta ba sai ya taka tabbas haka abin yake, zaki iya tafiya". Farida ta idasa maganar tana sakin hannu Hassana da k'arfi, Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Manager idan har haka zaka ci gaba da tafiyar da aikin ka, tom ba wai su ba, hatta kai zaka iya barin Sanat cikin k'ank'anin lokaci, kabar ta k'amar kana da power agun Oga Habib, ni zan rugaza power taka". Hassana na fad'in haka taja Office d'in da k'arfi ta fita".
Manager da su Billy kallan juna sukai, manager ya ce, "kar ku ji komai zuwa gobe aikin zai fara, ai yarinyar nan sai ta bar gurin nan cikin satin nan, zan yi amfani da barinta gurinnan da ta ke yi, kullum ai ko yau sai da taje inda zata ta dawo taci gaba da aiki, dan haka karku ji komai, cikin satin nan nan komai zai zo k'arshe". Su Farida cikin jin dad'i suka kashe da juna ita da Billy ".
Hassana ko gu d'aya ta samu ita ma ta zauna tana tunanin ta ina zata fara b'illo musu, wani tunani yazo ma Hassana ya sa ta tashi ta nufi Office d'in Habib".
Hassana zama ta yi tana kallan Habib, sannan ta ce, "Oga Habib ina da tambaya? ". Habib d'agowa ya yi yana kallan Hassana, sanna ya ce ina ji? ". "Oga Habib atsa rin masana'antar nan manager zai iya hakana wasu aiki kawai su keb'e suna hira? ".Habib kai ya girgiza ma Hassana. Hassana kuma ta ci gaba da cewa, " Ni zan iya tsawatarwa akan abinda naga anayi ba dai-dai ba? ". Kai Habib ya kuma d'aga ma Hassana".
Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "shikenan Oga Habib ni zan wuce gida, akwai abinda zanyi". "Ki bari mu wuce tare". Cewar Habib ".
Hassana hak'ura ta yi har lokacin da Habib ya tashi suka wuce tare".
Washe gari Hassana ta gama shirinta na fiya aiki Habib ya ce mata yau ba zata ba, Hajiya na kiranta. Habib da kan shi ya d'au ki Hassana ya kai ta gidansu".
Yau sati d'aya kenan raban Hassana da zuwa Sanat saboda kullum gidan Hajiya Turai ta ke wuni. Can b'angaran su Manager ko acewar shi sun samu damar dakatar da Hassana aiki, in da bata sanar ba. Aiko haka akayi yau Hassana tazo aiki saboda Hajiya Turai yau taje unguwa bata gida. Hassana na zuwa ta samu gu ta zauna inda ta ke zama, Hassana na nan zaune manager yazo da ta wata takarda ya mik'a ma Hassana ya ce, " mun baki suspection na sati d'aya, saka ma kon rashin zuwa ki na sati d'aya da biki ba, kuma ba bu wata sanarwa ko dalilin hakan".
Hassana amsar ta kardar ta yi, ta kalli manager ta ce, "Zan tafi ne kawai dan uzirin kaina, Hassana na kaiwa nan ta tashi ta tafi. kamar yadda manager ya ce mata".
Tun daga wannan rana Hassana ta fara zuwa koyan girkinta kullum har na tsawan sati d'aya kamar yadda manager ya bata. Habib ko koda ya tambayi Hassana lafiya ta bar zuwa aiki , fad'a mai ta yi manager ne ya bata suspection, Habib bai cema Hassana ko mai ba. Ahaka dai har Hassana ta yi sati d'aya".
Zaman Hassana da Habib ko masha Allah, dan ahanki ahankali shak'uwa keta k'ara shiga tsakanin Hassana da Habib sosai".
Yau Hassana da wuri ta tashi tai shirin zuwa aiki, tana zuwa ta samugu inda ta saba zama ta zauna".
Billy ko da ke cikin karanta ba babbaka k'arfe biyu tazo aiki. Abin sosai ya yi ma Hassana da d'i, ganin Billy yanzu tazo aiki. Hassana tashi ta yi tana kallan Billy ta ce, " 'Yan matan manager ki ce yadda kika ga dama kike zuwa aiki, tom ki koma gida sai nan da sati biyu ki dawo! ". Billy dariya ta yi, ta ce, "Banda lokacin ki amma ga manager nan bari yazo ya baki amsa. Manager k'arasowa gun ya yi yana kallan Billy irin lafiya? ". Murmushi Billy ta yi, sannan ta ce, " dearie wai ta ban Suspection na two week's ". "Muje ". Manager ya cema Farida". Hassana kuma kallan manager ta yi, ta ce, "Ai wallahi sai ta yi zaman gida na sati biyun da na anbata". Billy kallan manager ta yi, ta ce, " dearie muje ka rabu da karyar". Hassana ranta b'ace ta ce, "Shine kare, shida ke binki kamar. ..... ". Marinda manager ya yi ma Hassana ne yasa bata k'arasa fad'in abinda tai niyya ba, manager hannu yasa zai kuma wanka ma Hassana mari... ".
Yaji an ce, "Managereeeeeeeee..... ✍️
Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝
Share
&
Comment please 🙏
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://www.facebook.com/groups/301023561618950/