Sashe 16
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hassana cikin tsoran Billy ta shiga cikin Sanat yughurt. Hassana direct inda ta ke sharewa ta nufa ta kama aikinta. Duk staff d'in da tazo da mamaki ta ke kallan Hassana, dan su asaninsu duk wadda Billy ta dakatar ta tafi kenan, hakan yasa suke bin Hassana da kallon mamaki. Hassana ta gama share gun tana morpping Billy ta shigo site d'in. Billy tun daga nesa ta ke kallan Hassana, dan tabbas idan idonta ba gizo ya ke mata ba, yarinyar da ta kora aiki jiya ce ta dawo yau. Hakan yasa Billy ta k'arasa inda Hassana ta ke.Billy kallan Hassana ta yi da kyau sannan ta ce, "Ke ba ke bace jiya na dakatar da ke aiki a Company nan? "? Hassana d'agowa ta yi tana kallan Billy sannan ta ce, "Ni ce". Wani kallo Billy taima Hassana sannan ta ce, "Ok, biki ji bane sai na kuma maimai tawa ko me!? ".Hassana kallan Billy ta yi, ta ce, "supervisor Oga Habib ne yace in dawo in cigaba da aiki". Billy kallan mamaki tai ma Hassana, dan tana da tabba cin k'arya tai ma Oga Habib. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, "Ke kafin insa ad'aukeke afitar dake daga nan, ki sauri ki bargunnan stupid kawai". Hassana kallan Billy ta yi ta ce, "Supervisor Wallahi Oga Habib ne ya ce in dawo". Shiru Billy ta yi tana tunanin tom ina Hassana zata ga Oga Habib, dan ko ita sai da dalili mai k'arfi ta ke shiga office d'in Oga Habib bare kuma Hassana, cewarta acikin zuciyarta. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, ki bar aikin kisaman office d'in manager". Billy na fad'in haka ta juya ta tafi office d'in manager. Hassana bayan Billy ta fi, ta sameta office d'in manager kamar yadda Billy ta buk'ata. Billy ko na shiga office d'in, manager ta kalli Manager tana nuna mai Hassana ta ce, "manager waya dawo da yarinyar nan aiki? ". Manager shima da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "Hassana waya dawo da ke aiki, bacin Supervisor ta dakatar da ke? ". Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Oga Habib ne ya ce indawo in cigaba da aiki". Billy ranta b'ace jin abinda Hassana ta kuma cewa ta ce, dan ita yanzu tafi tunanin manager ne yadawo da Hassana ya ce tace Oga Habib ne yadawo da ita. Inda ita a tunaninta Hassana ina zata ga Oga Habib, in ma taganshi tasan bata isa ba ta kai mai k'arar andakatar da ita aiki. Hakan yasa Billy ranta b'ace ta kalli manager ta ce, "Manager yau d'in nan zan aje aiki, Inda ni ban'isa in yanke hukunciba, in dai yarinyar nan bazatabar aiki anan ba, tom sai dai ni in aje aiki! ". Manager cikin damuwa ya kalli Hassana ya ce, "Hassana taya M, D, ya san ankoreki aiki? ". Hassana kallan manager ta yi ganin yadda ya damu jin Billy ta ce zata bar aiki. Manager dakama Hassana tsawa ya yi ganin Yana tambayarta ita kuma tunanin ta ke, ya ce, "Ke bakya jine?, nace taya M. D, yasan andakatar da ke aiki!? ". Hassana kallan manager ta yi ta ce, "Jiya Hajiyar Oga Habib ta dawo, tom bacin naje gaidata ne, ta ke tambar waya d'aukeni aiki, tom shine bayan nasanar da ita, nake fad'a mata amma andakatar dani aikin, tom da yake Oga Habib na gurin zaune, shine ya ke tambayata waya dakatar dani shine nace mai supervisor ce, shine yace yau in dawo aiki".manager kallan Billy ya yi yace tom kinji yadda akai". Billy itama kallan manager ta yi ta ce, "Wai bangane ba, idan nagane kana nufin yarinyar nan causing d'in Oga Habib ce ko me?, naji tana maganar gidansu ta ke ne kome ?". Manager kallan Hassana ya yi ya ce," je ki cigaba da aikinki". Hassana fita office d'in ta yi tabar manager da Billy".
Bayan Hassana ta fita ne, Billy ta kalli manager ta ce, "Manager ni fa gaskiya banyarda da dawowar aikin yarinyar nan ba". Manager cikin taushin murya ya ce, "Tom Billy yanzu ya ki ke so ayi, aidai kinji daga m, d, ne dawowar ta". "Eh naji daga Oga Habib ne, amma ai yanzu idan kaje kasamu Oga Habib ka ce mai kai ka dakatar da ita, nasan zai yarda, idan kuma bahakaba ni zan bar aiki anan, dan sai ta d'auka ita sa'atace, shiyasa ni na koreta aka dawo da ita". Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Billy Yarinyar nan da kike gani m, d, da Bilya driver m, d, ne suka tsinceta, tom bata da Inda zata zauna shine dalilin ma da yasa M, D, barinta gidansu, nina rok'anmata, yanzu idan ya koreta ina zata?, ki yi hak'uri daga yau zata gyara ". "Shikenan badamuwa amma ta kiyaye ta rik'a zuwa aiki da wuri". cewar Billy, sannan ta fita daga Office d'in manager".
Hassana ko komawa ta yi taci gaba da aikinta, Hassana na tsaka da aiki ne, wata staff ta kalli Hassana ta ce, "Ke ce Hassana? ". "Eh ni ce". "Tom Supervisor ta ce idan kin gama morpping d'in ki je tana kiranki". Hassana da tom ta amsa. Aiko Hassana na gama wa ta je office d'in supervisor ta ce, "Supervisor ance kina kirana". Billy sai da tagama abinda ta ke yi, sannan ta ba Hassana wani Cup ta ce taje ta wanke mata. Hassana amsa ta yi ta je ta wanke mata ta kawo mata. Bayan Hassana ta dawo ne, Billy ta kalli Hassana ta ce, "Hassana ki ke kome, dama kunne zanja miki, sannan kinsan ya zama dole a hukuntaki abisaga laifin da ki kai, na fashin da ki kai baki zoba, daga yau sai 10 o'clock zaki rik'a close". Hassana kallanta Billy ta yi ta ce, "Supervisor dan Allah ki yi hak'uri,Oga Habib ya ce kar in wuce magriba ban dawo ba".Billy Cikin d'aga murya ta ce, "Oh!, kina nufin duk da laifin da ki kai har wani ragin lokaci kika samu, tom wannan kuma ke ya shafa ni dai kinji abinda na ce miki, idan kuma kink'iji zamu rage a salary d'inki". Shiru Billy ta yi sannan ta nuna ma Hassana hanyar fita, ta ce, "fitar min daga office. Hassana fita ta yi tana mamakin yadda Billy ke nuna mata tsana k'iri-k'iri".
Hassana magriba na yi, kamar yadda Habib ya ce mata ta koma gida, magriba na yi Hassana ta shirta ta koma.
Tun daga wannan rana ya zamana kullum Hassana ta je aiki Billy ta dinka sata aiki kenan, daga yi min wancan sai yi min wancan, har wankin toilet d'in gun Billy Hassana ta ke sawa, acewarta abakacin tashin da wurin da ta ke yi. Ita kuma Hassana ta yi ma kanta alk'awarin duk abinda Billy ta sata zatayi baza tai mata musuba, hakan ya sa Hassana ta kuma ramewa sosai.
BAYAN SATI D'AYA.
Hassana sosai ta dage sai goge-goge ta ke yi so ta ke tagama tai ma manager magana ta tafi gida, saboda ciwan da kanta ya ke mata. Hassana na Cikin aiki wata staff ta ce, Hassana kije Office d'in manager ana kiranki". Hassana sauri ta yi tak'arasa abinda ta ke yi, sannan ta je office d'in manager. Hassanan da mamaki ta ke kallan shi ta ce, "Oga Bilya kaine, yau she kadawo? ". Bilya murmushi ya yi ma Hassana sannan ya ce, "Hassana tun jiya na dawo,ya kike ya aiki? ". "Lafiya klau, barka da dawowa Oga Bilya". Bilya kallan Hassana ya yi yace, " Yauwa Hassana, zaki iya ko mawa ki ci gaba da aikinki, dama nakiraki ne mugaisa. Hassana kallan manager ta yi tace, "Manager bani da lafiya, dan Allah ina son zuwa gida yau da wuri in samu magani insha". Manager kallan Hassana ya yi, sannan ya ce, " ki fad'ama supervisor ". Hassana shiru ta yi dan tasan in dai ita ce ma babarinta za tai ba, amma ance mai naima baya fushi, hakan yasa ta fita Office d'in manager ta shiga na supervisor. Hassana na zuwa ta kalli supervisor ta ce, "Supervisor bani da lafiya, ina son zuwa gida dan Allah, zan sha magani". ko inda Hassana ta ke Supervisor bata kallaba, ta ce, " Idan kin je karki dawo". Hassana najin haka tafita office d'in supervisor dama tasan ba barinta za tai ba. Hassana haka ta koma guri d'aya ta zauna dan bata iya komai tsabar ciwan kan da kanta ke mata. Hassana ba ita ta tashi ba sai magriba kamar yadda ta saba tashi. Hassana tafiya ta rik'ayi a k'asa kafin tasamu napep ga wani irin ciwo da kanta ke mata".