← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 78

Sashe 22

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Turai ko bayan fitar Bilya Kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba barka da zuwa, ya hanya, ki yi hak'uri Baba zaki ce ban ne mekiba lokacinda Habib ya koreki sai yau da buk'atata ta tashi, Baba dan Allah taimako zaki min kamar yadda ki kaimin kafin mutuwar Mahaifin Habib? ". Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi, dan duk bata gane takan zancan ba ta ce, "Hajiya ina ji, wana irin tai mako zan baki? ". Shiru Hajiya Turai ta yi, tana tunanin ta inda zata fara yima Baba Lami bayani, sannan zuwa can ta ce, "Baba Habib ne baida lafiya, kuma ciwannashi kamar hauka, dan Baba Lami yanzu ko ni ban isa inje d'akin Habib ba, sai yarinya d'aya agidannan dan yauma ita akaba abin break fast d'in shi ta kai me, amma cikin ikon Allah ita Bai mata komai". Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Hajiya to aiko idan haka ne akwai alamar tambaya ajikin yarinyar nan, wata yarinyar ce? ". Hajiya Turai Kallan Baba Lami ta yi ta ce, "Yarinyar da ya koreki keda Bilya akanta". Shiru Baba Lami ta yi, Sannan ta ce, "Hajiya wai meye musabbabin ciwanne?, koko sai dai kuka wayi gari kuka ganshi ahaka?". "Eh Tom Baba Lami, maganar ce nada mamaki da kuma d'aure kai, wato Baba Lami naje d'akin Farida sai naji tana waya da Hajiya Murja tana cewa ita yanzu abinda ke damunta yarinyar da ciwan ya riski Habib da tana wajan yanzu da ita zai rik'a yarda ba ita ba, ita abinda ke damunta kenan, tom da yake a speaker wayar ta ke, sai naji ita Hajiya Murja na cewa, Farida kuma kin tabbata kin bashi tea d'in ya sha, Farida ta bata amsa da Eh, tom shine fa ta ce wai ta binciko mata sunan yarinyar da ciwan yamu Habib agabanta". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "tom Baba Lami kinjin abinda ke faruwa, dan Allah ki taimakamin kamar yadda ki kaimin lokacinda Mahaifin Habib na da rai! "? "Karki damu Hajiya insha Allah, mu bari sai gobe inda yanzu yamma ta yi". "Tom Allah ya kaimu goban Lafiya". Cewar Hajiya Turai ".
B'angaran Hassana ko yanzu haka kwance ta ke tana mamakin da Oga Habib Bai yadda da kowa ya shiga inda ya ke sai ita, abinda ya k'ara d'aurema Hassana kai har Mahaifiyar shi ma taga bata isaba tashiga inda ya ke ba, nan dai Hassana ta na tunane-tunananta ta bacci ya kwasheta inda dama ba sallah zata yi ba".

Bilya bashi ya k'ara shiga part d'in Hajiya Turai ba sai da ya yi Sallar magriba sannan. Zaune Bilya ya isketa kan sallaya ta yi ta gumi. Hajiya Turai na ganin Bilya ta ce, yauwa Bilya dama maganarka na keyi azuci yanzu haka,kamar kasan san ganinka nake yi. D'azu da nace ma kabimin bayan Farida, ya akayi? ". "Hajiya kamar yadda ki kayi tunani Sanat yughurt taje, tana zuwa suka had'u da supervisor gun, bayan sun gaisane da yake sunsan juna tom shine Farida ke tambayar supervisor sunan wadda Habib ya rik'ema hannu lokacin da lallurar ta sameta, dan acewarta ga supervisor ke kika aikota wai kina zargin Hassana, tom nan dai ta fad'a mata sunan Hassana". Shiru Hajiya Turai ta yi Sannan ta ce, "Bilya dan Allah ka mik'ama Habib abinci kota window ne, dan ni Wallahi tsabar rud'ewa na manta kona rana ban bashi ba".

Bilya amsar abinci ya yi ya je ya jira ma Habib shi ta window kamar yadda Hajiya Turai ta ce.
Sai dai abinda basu saniba Habib ko Kallan abinci bai yiba".

Washe gari Hajiya Turai da Baba Lami da wuri suka yi sammakon zuwa zaria, inda Bilya ne zai kaisu.
Bayan sun fitone Hajiya Turai ta lek'a ta window tana kallan Habib zaune yake inda yasaba zama. Hajiya Turai ganin abinci jiya ta yi yadda aka kaishi yana nan ahaka. Hajiya Turai Bilya ta kira ta nunamawa ta ce, "Bilya kaga abincin jiya ko Habib bai ciba? ". "Eh Wallahi Hajiya nima haka nagani". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta kalli Bilya ta ce, "Bilya ku jirani amota kaida Baba Lami ina zuwa".

Hajiya Turai site d'in worker's d'in gidanta ta je, wata daga cikin masu yima Hajiya Turai aiki, Hajiya Turai ta aika takiramata Hassana.
Hassana ko lokacin tana kwance tana baccin safe,Binta ta shigo ta tada Hassanan, ta ce, "Hassana ki tashi Hajiyar Oga Habib na waje tana jiranki! ". Binta na fad'in haka ta juya ta tafi badare da ta tsaya taji amsar Hassana ba".

Hassana ko tashi ta yi ta tafita tana mai addu'ar Allah yasa Hajiya Turai ba abinci zata kuma cewa ta kaima Habib ba. Hassana na wannan tunanin ta isa inda Hajiya Turai ke tsaye tana jiran fitowar Hassana".

Hassana har k'asa ta juk'unna ta gaida Hajiya Turai tare da tambayarta ya mai jiki.
Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, "Lafiya klau, Hassana dan Allah taimako zaki min na k'arshe? ". Hassana cikin girmamawa ta ce, "InajI Hajiya". "Hassana dan Allah abinci zaki taimakamin ki kaima Habib, tun abincin jiya da kika kai mai haryanzu baici komai ba, jiya da nasa aka kaime nadare Yanzu haka abincin nacan baiciba, dan Allah Hassana ga abin break fast d'in shi can, dan Allah kije ki kai mai". Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Tom Hajiya". Hassana tashi ta yi tanufi site d'in Hajiya Turai d'akko break fast d'in Habib. Hajiya Turai amota ta samu su Bilya suka kama hanyar zaria".

Hassana na tafiya zuwa b'angaran Habib tana tambayar kanta, "Wai meyasa ni Oga Habib baya dukana? , dan ayadda na lura kowama duka ya ke, kuma meye dalilin shina hanani fita da yake yi?". Hassana shiru ta yi dan bata san mai amsa mata tambayoyinta ba. Hassana ta window ta fara lek'a Habib.
Kwance ta hango shi kan caution d'in falon, ya yi kwanciyar rubda ciki. Hassana kallan yadda Habib ya ke ta yi sai taga kamar yaji sauki, dan ayarda ta ganshi babu yadda za ai kace wai wani abu nadamun shi. Bud'e k'ofar d'akin Hassana ta yi tashiga".

Habib na jin alamun shigowar mutum ya tashi da sauri yayo kan Hassana. Dan sai da Hassana ta ji tsoro ganin yadda ya yo kanta, amma kuma yana zuwa inda ta ke sai ya kamo hannunta ya ida shigoda ita falon".

Hassana bayan ta zauna kallan Habib ta yi ta ce, "Oga Habib ga abin break fast d'in ka ". Hassana ta fad'i maganar tana mik'ama Habib kunun gyad'a".

Habib amsar kukun ya yi, kafin kace me ya shanye shi tass. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib in k'arama? ". Habib Kallan Hassana kawai ya ke, amma ba bakin magana. Hassana ganin ba magana zai mata ba, yasa ta kuma k'ara mai kunun ta mik'a mai.
Habib amsar Cup d'in ya yi ya kuma d'agawa ya shanye tass, ya mik'a mata Hassana cup d'in. Hassana amsa ta yi tana mai tsananin jin tausan Habib. Mutumin da komai nashi anatse ya ke yi wai ace yau shike irin wannan shan kunun. Hassana k'ara ma Habib kunun ta yi, nanma ya d'aga kai ya shanye shi tass lokaci guda ya aje cup d'in. Bayan Habib ya gama shan kunun ne, Hassana ta tashi da niyyarta ta tafi. Amma Habib ya rik'eta ya hanata tafiya kamar jiya. Hassana cikin sanyi murya kamar ance mata Habib d'in jinta ya ke ta ce. "Oga Habib dan Allah kabarni in tafi zanyi wanki ne, innagama zan dawo ". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi. Bubu irin wayan da dubarar da Hassana batai ma Habib ba dan yabarta ta tafi amma yak'i yana mai irik'e da hannunta. Dole Hassana ta yi hak'uri ta zauna tana mai addu'ar Allah yasa Hajiya Turai ta dawo da wuri".

B'angaran su Hajiya Turai ko, sun isa zaria. Hajiya Turai ce ta kalli Baba Lami ta ce, "Baba Lami zadai ki gane gidan ko? ". Murmushi Baba Lami ta yi sannan ta ce, "zan gane mana Hajiya".

Haka Baba Lami taita nuna ma Bilya hanya har ya kaisu gidan malam Ishu...........

Idan kin karanta ki daure ki yi Comment sister 🤝

SHERE
&
Comment
PLEASE 👏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group:
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
🍁 Ibnul-Jawzī (rahimahulLah) yana cewa: *“Ka kiyayi roqon Allah game da wani lamari ba tare da ka rokeshi alherin dake cikin abin ba. Haƙiƙa, wani abinda zaku roqa game da rayuwar duniya na iya zama sanadin halakarku."*

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 24&25.
Chapter 22 · 0% Book details