← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 78

Sashe 45

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Turai ko shiru ta yi tarasa abinda ke mata dad'i, dan itama sosai maganganun Habib su kai mata zafi, sannan ya kuma daf kawa, wai shi zai tafi dama bada yardar shi akai ba".

Hajiya Turai kallan Hassama ta yi da ke zuk'unne kanta ak'asa. Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, sannan ta ce, "Daughter ki yi hak'uri, nasan kinji duk abinda Habib ya ce". "Babu ko mai Mommy, ai abinda ya fad'a haka ne ba asan asalina ba, ni yanzu Mommy abu d'aya zaki min dan Allah ki datse auran nan, insha Allah gobe zan tafi garinmu". cewar Hassana. Hajiya Turai cikin damuwa ta ke kallan Hassana jin abinda Hassanar ta ce. Sannan Hajiya Turai ta ce, "Daughter tafiya kuma? ".
"Eh Mommy tafiya nake son yi dan Allah karki hanani".
"Shikenan daughter share hawayanki, yau she kike son ki tafi? ". Cewar Hajiya Turai"."gobe". Hassana ta ba Hajiya Turai amsa a dak'ile".

Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta kalli Hassana ta ce, "daughter kije ki yi break fast, Allah ya kaimu goban ".

Hassana cikin sanyi ta tashi ta ta fita".

B'angaran Farida ko, yau ta shirya dan zuwa gidansu Hajiya Turai dan ganin lafiya, dan a yadda tai ma Habib magana akan sakin Hassana ya nuna ya amshi maganar, tom tunjiya taso zuwa, amma Hajiya Murja ta hanata ta ce, ta bari sai nan da kwana biyu tuk'un ta san kafin lokacin Habib ya rabu da Hassanar, Allah bashi sai su san ta yadda zasu b'ullo mai ya auri Farida, hakan yasa Farida yau ta yi shirinta ta na tafita gidandu Habib, in da yau ne Mahaifiyarta ta ce mata ya kamata ta je".

Farida k'arfe sha biyu na rana tazo gidansu Habib. Direct Farida part d'in Hajiya Turai ta nufa".

Hajiya Turai Farida ta iske zaune a falon ita kad'ai, Farida kamar yadda ta saba, haka ta je ta gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai ko ta amsama Farida a dak'ile, babu yabo babu fallasa.
Farida d'an nesa da Hajiya Turai ta zauna, tana Waige-waige ko zata hango Hassana, dan ta k'osa ta ji har yanzu Hassana na gidan. Farida kallan Hajiya Turai ta yi, cikin sanyi ta ce, "Mommy Hassana fa?, banganta ba". "Tana ciki". Hajiya Turai ta kuma ba Farida amsa a da k'ile". Farida shiru ta yi tana tunanin tom Habib ya saki Hassana ne ko ko?".

Farida zama ta yi tana jiran Habib ya dawo ta kuma zuwa ta tunkarai da maganar ta ji abinda zai ce".

B'angaran Habib ko, dan karma ya dawo da wuri ya had'u da Hajita Turai, yauma k'in dawowa ya yi, sai 9:50Pm, kamar jiya. Yana dawowa ya kira Hajiya Turai a waya, bayan sun gaisane ya ke sanadar da ita, ya ce, "Mommy yauma bandawu da wuri ba, shigowata kenan yanzu, sai dafe na shigo". "Allah ya kaimu Hajiya Turai ta ce, ta yi rejecting call d'in ".

Farida ko ganin Habib bai dawo da wuri ba, yasa ta adana kala manta sai washe gari ta yi ma Habib ".

B'angaran Hassana ko yau haka ta wuni duk ba fara'a, dan ko abinci tsakura kawai ta ke. Ko da yaushe ko saurare ta ke, ta ji Hajiya Turai ta ce mata ta warware auranta da Habib, dan sosai ta ji hankalinta ya koma gida, mahaifarta kawai ta ke son tafiya, inda ga abin da barin gida ya jawo mata, har ana ik'irarin ba asan asalinta ba, tabbas bata tab'a, kawo ma ranta wata rana wani zai mata gori da hakan ba, hakan ne ya sa da akai mata ya tada mata hankali , taji gaba d'aya hankalinta ya koma ga mahaifarta.
Adaran dai haka Hassana ta yi bacci duk ba dad'i".

Washe gari. :washe gari bayan Hassana ta idar da sallar asuba gari ya fara aske, kamar yadda ta saba haka ta je gaida Hajiya Turai, sai dai Hassana koda ta tura bedroom d'in Hajiya Turai sai taji kamar ansa key, Hassana cikin mamaki ta juyo, ta koma d'akin ta. Hassana ta zauna babu dad'ewa Maimuna ta yi sallama ".

Hassana amsawa ta yi, sannan ta fito tana tambayr Maiamuna lafiya. Takardar da ke hannun maimuna ta mik'ama Hassana, ta ce, "Dama Hajiya ce ta ban ta ce in baki". Hassana amsa ta yi tana bin letter da Maimuna ta bata da kallo, sannan ta mai da kallanta gun Maimuna ta ce, "Ina Mommy fa?". "Hajiya ta yi sammakon tafiya". cewar Maimuna. Hasssana ba ta k'ara bin takan zancan Maimuna ba, ta bud'e letter tana karantawa kamar haka. :Assalamu akaikum. Da farko dai ina baki hak'uri daughter na sab'a alk'awarin da nai miki, hak'ik'a naso in raba auranki da Habib kamar yadda nai miki alk'awari, sai dai kash !, na kasa hakan. Daughter ba zan b'oye miki ba bazan iya raba auranki da Habib ba, sai dai idan Allah ya yi babu rabon zaman aure a tsakanin ku. ki yi hak'uri da rashin sallamr da ban miki ba. Daughter bana iya had'a ido da ke ne, dan ina jin kunyar abinda Habib ya yi miki. Dan Allah daughter ki lura yanzu akwai aure kanki, dan Allah ina rok'onki karki ce zaki tafi da aure kanki. Ki yi hak'uri insha Allah komai zai dai-dai ta tsakaninki da Habib.,ki yafemin daughter, bissalam ".

Hassana ko da ta kama karanta letter da Hajiya Turai ta bada a ba ta, gun ta zauna tana kuka. Cikin kukan tana cewa, "Haba Mommy biki ji abinda Oga Habib ya ce bane, koda ace ni 'yar asali ce, tom baya sona kwata-kwata azuciyar shi. me yasa zaki min haka!! ".

Haka Hassana tasha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru".

Farida ko da kukan Hassana ya ta data, ta window ta lek'o tana kallan Hassana. Hassana ko nan ta tashi ta bar letter da Hajiya Turai ta bata agun".

Farida ko na ganin Hassana ta tashi ta zo da saurinta ta d'au letter tana karantawa ".

Farida ko da ta kagama karanta letter, kuka itama tasa, dan ta yi tunanin Hassana nakukan Habib ya saketa ne. Farida share hawanta ta yi sannan ta d'akko tan figigin mayafinta ta yafa, ta nufi gidan Mahaifiyarta, da letter a hannunta".

B'angaran Habib ko bayan ya gama shirinsa ya fito, ya nufi part d'in Hajiya Turai. Bilya ne ya yi saurin da katar da shi ta hanyar cewa, "Barka da safiya Oga Habib, ga shi inji Hajiya ta ce in baka".

Habib amsar letter da Bilya ya mik'a mai ya yi yana mamakin ta me ye. Habib bud'e letter ya yi ya fara karantawa kamar haka. :Habib raina b'ace na kema magana, hak'ika na ji zafin maganganunka na jiya akan Hassana, kuma ina son ya zama farko da k'arshe da zaka k'ara furta mata wata kallama mai muni irin haka. Habib na koma wajan aiki, hak'ika idan na kalli fuskarka ayanzu tana tuna min ne da kalmomin da ka fad'ama Hassana marasa dad'in ji. Daga k'arshe idan har ka saki Hassana koda ko ita ce ta naimi hakan Allah ya isa ban yafema ba Habib!!! ".

Wata irin zufa ce ke keto ma Habib lokacin da yagama karanta letter. Sosai ranshi ya b'ace da furicin Mahaifiyarshi akan shi, akan me za tai mai haka, koko ana zaman aure ba so ne, tom idan ma anayi gaskiya shi ba zai iya haka ba. Habib wayar shi ya ciro ya kira Hajita Turai, amma har ta gama ringing bata d'aga ba".

Habib ranshi b'ace ya kalli Bilya ya ce, "Bilya kiramin waccan yarinyar ". Bilya ko tunda yaga haka ya yi tunanin babu lafiya, dan lokaci guda idon Habib ya kad'a ya yi ja sosai".

Bilya kallan Habib ya yi, ya ce, "Oga Habib wata yarinyar? ". "Bansani ba Bilya!, ai kasan yarinyar da nake nufi".

Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan yaga Hassana ahalinda ya ke yanzu , ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai............ ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.

Idan naga Comment da yawa gobe insha Allah zaku ga Update da wuri Allah.

Idan na raina comment tom zafa kuji shiru🤐🤐🤐.

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Shafi na 54&55.

Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan Habib yaga Hassana a halinda ya ke yanzu ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai. Sai dai ko da ya shiga ba kowa Falon, sallama Bilya ya yi da k'arfi, amma shiru. Bilya fita ya yi yana mai jin dad'in rashin ganin Hassana da bai ba , dan shi dama ba son isar da sak'on ya ke ba, aganin shi hakan bai kamata ba ".

Habib na tsaye inda Bilya ya barshi, Bilya ya dawo. Bilya kallan Habib ya yi ya ce, "Oga Habib inajin bata side d'in Hajiya, dan na yi magana naji shiru, babu alamun mutum".

Habib batare da ya tankama Bilya ba ya shiga mota. Bilya ma ya shigaya yaja motar suka tafi".
Chapter 45 · 0% Book details