← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 78

Sashe 77

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da wuri Habib suka yi shirin tafiya Kano, kasan cewar da wuri suka fita hakan yasa k'arfe 1:00Pm suka sauka, inda Hassana ita ke nuna ma Habib hanya har izuwa local government d'in da suke akano".

Hassana wani irin sanyi ta ke jin yana ratsata lokacin da suka iso k'ofar gidansu, sai dai ta wani b'angaran tana daurewa ne kawai kar tai kuka ta tada ma Habib hankali, amma idan ta tuna zata gidan su babu Mahaifinta mai sonta, ji tai kamar tai ihu, dan sai mutuwar Mahaifinta ta dawo mata farko. Duk yadda Hassana ke danne kukanta abin ya ci tura, sai ta ta sa kuka, Habib da ya yi parking a lalataccan gidan da Hassana ta nuna mai ta ce nasu ne, jira ya ke ta ce su sauka, amma sai yaji kukanta, Habib cikin damuwa ya kalli Hassana ya ce, "Sanat ko mai narayuwa d'an hak'uri ne, dan Allah ki yi hak'uri ki goge hawayanki, in ba so ki ke ki sa ni damuwa ba ". Hassana da sauri ta share hawayan ta , ta ce, "Natuna da Mahaifina ne mai sona , mai tausaina, sanadin rashin shi yasa na gudu na bar ma haifata".

Habib lallashin Hassana ya yi sosai sannan ya ce, "ki shiga ciki mana, ko kin manta gidan ne? ". "A'a nan ne". Cewar Hassana ".

Hassana fita ta yi daga Motar ta nufi cikin gidan. Zaune Hassana ta iske Mahaifiyar Usaina 'yar uwarta, da Usaina, Hassana sallama ta yi tana mai k'arasawa inda suke".

Dukan su da kallo suka bi Hassana, dan basu gane ta ba. Hassana ko da fara'arta ta k'arasa inda suke ta ce, "Umma bugu gane ni ba ne, ?, yan zu kema Usaina bi ki gane ni ba? ". Usaina da taji Muryar Hassana zin bur tai ta mik'e tana kallan Hassana, ta ruga ta rungume Hassana ta ce, "Umma Wallahi Hassana ce!, Hassana ce ta dawo gare mu Umma!!! ". Usaina ta fad'i maganar da k'arfi tana fad'awa jikin Hassana".

Hassana ma rungume Usaina ta yi tana kuka, Allah sarki Usaina ma kukan tasa, sai da su kai sukan su sannan su kai shiru, ita dai Umma kallansu kawai ta ke tana share hawayanta ita ma ".

Usaina da katawa ta yi da kukan ta jawo hannun Hassana suka zauna. Umma cikin mamaki ta kuma kallan Hassana ta ce, "Hassana ke ce?, dama kina raye Hassana?, ina kika shiga ke ko?, Hassana kin tafi kin bar mu cikin damuwa ". Umma ta fad'i maganar tana share hawayan ta. Hassana ma goge nata hawayan ta yi, sannan ta ce, "Umma ku yafe min na gudu na barku, dan Allah Umma ki yafe min? ". "Hassana ai dole ki gudu, mun ta kura ma rayuwarki mun rabaki da abin da kike so, bakin cikin haka ya kashe mahaifinku, Hassana dole ki gudu ki bar mu, mu zamu rok'e ki yafiya, ki yafe mana Hassana, amma ke biki mana ko mai ba". Umma kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana inji dai ba karuwanci ki ka je ba? ".

Hassana kuma goge hawanta ta yi sannan ta ce, "Umma banyi karuwanci ba, na bar nan da wata uku nayi aure, yan zu haka muna tare da wanda na aura". Umma bud'e baki ta yi tana kallan Hassana, ta ce, aure Hassana, amma naji dad'i da ba yawan banza ki ka yi ba, je ki shigo dashi, ya zaki bar shi waje ".

Hassana zuwa ta yi suka shigo da Habib. Umma sosai ta cika da al'ajabi da ganin Mijin da Hassana ta aura, lallai wanan shine ake kira da kyakkyawar k'addara".

Dama tun kafin Habib ya shigo an mai shim fid'a, Habib zama ya yi, sannan ya gaida Umma, suka gaisa da Usaina".

Umma kallan Habib ta yi, ta ce, "bawan Allah taya kuka had'u da Hassana? ". Habib zayyane ma Umma ya yi kaf yadda suka had'u da Hassana, da yadda akai auran su da Hassana".

Umma sosai ta yi murna, dan ta yi nadama sosai bayan tafiyar Hassana. Bayan Habib ya gama ba Umma labari ne, Umma ta kalli Habib ta ce, "Na san Hassana ta baka labarin halin da muka sata, wato Hassana bayan auran Kabir da Usaina, ina jin basu zaman wata uku cikakku ba, sai fad'a wulak'ancin yau da ban na gobe da ban. Hassana nayi nadamar rabaki da Kabir, amma kuma na godema Allah da na rabaki da Kabir in da sanadin haka ne yasa kika gudu, har Allah ya had'aki da bawan Allah nan, wato Hassana yan zu haka maganar nan da nake miki Usaina ta dad'e agida, da ta gaji da wulak'an ci da Kabir ya ke mata ta dawo gida, har yan zu ko zuwa bai yi ba, k'arshe ma munji labarin ya yi aure, jiya jiyan nan ya aiko mata da takardar ta". Hassana sosai ta tausayama 'yar'uwarta halin da ta shiga".

Sun dad'e suna hira sannan Habib ya ne mi Masallaci ya tafi yin sallah. Bayan Habib ya fita ne, Umma ta kalli Hassana ta ce, "Hassana kinga gidan ko girki ba muyi ba, me zaku ci Usaina ta tashi ta siyo miku? ". "A'a Umma Allah bana jin yunwa sai da muka ci abin ci a hanya ".

Habib na dawowa ya d'auki Hassana ya suka nufi dan gin mamarta da babanta, duk inda suka je ba wani dad'ewa suke ba, dama kuma ba wani damuwa da Hassanar su kai ba, garama yan zu da suka ga waye mijinta tom sun nuna damuwar su da ita".

Da daddare Habib cikin gari ya shiga ya siyo abin da zasu ci. D'akin Mahaifinsu Hassana aka gyarama Habib ya kwanta, ya so ya nemi hotel ya kwana Hassana ta hana shi".

Washe gari :
Duk in da ya kamata Hassana su je, sun je, k'arfe 10:00Am Habib ya kalli Hassana ya ce, "Sanat ki shirya yan zu zamu wuce? ". Hassana dafa Habib ta yi kamar za tai kuka ta ce, "Dan Allah Oga Habib ka bari sai gobe mana". Habib da sosai ya daurema ya yi kwana d'a yan da ya yi, kallan Hassana ya yi, ya ce, " Dama nayi tunanin mu tafi da su Umma ne da Usaina suga in da kike, Allah basshi sai su zauna wajan Mommy har uzuwa lokacin da zaki haihu". Hassana da itama ta yi tunanin hakan, amma kuma ta kasa fad'ama Habib, Hassana cikin jin dad'i ta rungume Habib ta ce, "Sweetheart kamar ka shiga zuciyata nima nayi tunanin haka". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "tom muje asanar da su sai su shirya mu tai da wuri".

Habib zaune gaban Umma, ya ce, "Umma dama cewa nayi keda Usaina ko zaku shirya mu tafi tare kuga inda Hassana ta ke". Allah sarki itama dama ta yi tunanin hakan, hakan yasa batare da ja ba tace, "Tom ai shikenan sai mu shirya ".

Cikin k'ank'anin lokaci su Umma suka shirya, in da Hassana ta hana Usaina d'aukar kayan sawa ko d'aya ta ce ta bari ta rik'a sa nata, haka ko akai Usaina ban da kayan jikinta bata d'au ko d'aya ba".

K'arfe Biyar na yamma suka sauka. Wato su Umma mutuwar tsaye su kayi lokacin da suka ga gidan da Habib ya shigar da su".

Haka suka shiga Falon Hassana,Habib kuma ya shige ciki. Usaina da ta kasa daurewa kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana dama a irin gidan nan kike rayuwa?, gaskiya Hassana kin ji dad'i, kin ga ni son zuciya ya ja min na zama k'aramar bazawara". "Kibar tuna abin da ya wuce Usaina haka Allah ya k'addara". Cewar Hassana".

Habib hajiyar sa ya kira ya ce ta turomai Maimuna tai masu girki dan Hassana bata iyawa ta gaji. Aiko haka akai Maimuna ce ta zo tai masu girki. Suna nan zaune suna hira Maimuna ta zo ta Sanar da Hassana ta gama. Hassana kallan Umma ta yi, ta ce, "Umma muje muci abinci".

Haka suka ci abincin su suka gama. Koda lokacin kwanciya ya yi Hassana side d'in ta ta bar masu ta tafi wajan Habib ta kwana".

Yau kwana nan su Umma uku kenan da zuwa. Habib ya zo zai gaida Umma, bayan sun gama gaisawa Umma ta kallai ta ce, "Yau she zamu tafi ne? ". Habib cikin girmama Umma dan shi ya na mata Kallan mahaifiyar Hassana ne, inda ita ta shayar da Hassana, ya ce, "Umma dama yau Mahaifiyata zata dawo, idan ta dawo zaki koma wajan ta da zama ne, idan Hassana ta haihu sai ku tafi".
Umma k'in yarda da haka tai da kyar dai Habib ya samu ta yarda, dama Umma tana ma Hassana kallan kamar mai ciki, ashe ko haka ne".

Hajiya Turai na dawowa Habib ya d'auki Umma da su Hassana ma baki d'aya suka je. Wajan dawowa ne suka dawo suka bar Umma, inda suka dawo da Usaina, dan Hassana ta ce bata yarda ba sai dai Usaina ta dawo wajanta".

Billy ko tare da Manager suka zo har gidan Habib kawo ma Hassana invitation na biki. Hassana sosai ta yi mamakin ganin Billy amma kuma sai ta wuske, bayan manager ya ba Hassana Invitation card d'in, ya ce, "Madam dan Allah karfa kik'i zuwa". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "insha Allah zan zo ".Billy kuma cikin kunya ta ce, "Dan Allah amaryar Oga Habib duk abin da ya faru ki yi hak'uri ki yafe min, Wallahi har da zigar Farida abubuwa da dama da nai miki". Hassana cikin nuna ba komai ta ce, "laa ni har nama manta karki ji koma Babu komai Wallahi".
Billy Sallama su kaima Hassana suka tafi".

Akwana atashi babu wuya awajan Allah cikin Hassana ya shiga watan haihu, amma cikin babu wani girman kirki. Yau tunda Hassana ta tashi ta ke jin ciwo ka d'an -kad'an tun tana daurewa har tasa Usaina ta kira mata Hajiya Turai".

Hajiya Turai ko najin kira wai Hassana bata da lafiya, suka tafi ita da Umma in sa suka biya ta wata private hospital suka tafi da wata nursing".
Chapter 77 · 0% Book details