Sashe 23
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka Baba Lami tai ta nuna ma Bilya hanya har ya kaisu gidan malam Ishu.
Bilya na yin parking ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Tom Hajiya ina jiranku". Hajiya Turai kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba Lami muje". Baba Lami da Hajiya Turai sallama suka yi suka shiga gidan malam Ishu. Lokacinda da suka shiga lokacin malam Ishu baya gida.
Malam Ishu fitattan malami ne mai almajirai, duk wata lallura da ke damunka in dai kaje gun shi insha Allah zaka sami sauk'i da yardar Allah. Inda malam Ishu ke sauke bak'in shi aka kai su Hajiya Turai. Su Hajiya Turai na nan zaune Malam Ishu ya dawo".
Cikin girmama juna Hajiya Turai suka gaisa da Malam Ishu, bayan sun gama gaisawa ne. Hajiya Turai ta kalli Malam Ishu ta ce, "Malam dan Allah nazo ne katai makamin akan yarona d'aya shikenan min". Malam Ishu kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "Hajiya meke damun shi? ". Hajiya Turai cikin natsuwa ta fara yima malam Ishu bayani".
"Malam ciwanne kamar hauka-hauka, inda yanzu haka bacikin hayyacin shi ya ke komai ba".
Malam Ishu da katar da Hajiya Turai ya yi tahanyar ce mata, "Hajiya ko ke baya ganewa? ". Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, "Malam yanzu haka ko shiga d'akin shi nayi sai dai akwaceni hannun shi, bawai duka ya ke ba, amma idan yarik'e mutum yana shan wuya gun shi sosai, dan wujijjiga mutum ya ke, sosai".
Shiru Malam Ishu ya yi sannan ya ce, "Babu damuwa insha Allahu zai warke, da akwai rubutun da zamu rik'a mai duk sati insha Allahu kodama iskace ta shafe zata kauce, idan ma sihirine zai karye, ke kodama ace da aljani aka had'ashi ya mai da shi haka insha Allah ayar Allah zata karya duk wani abinda ke jikinshi".
Malam Ishu kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Hajiya ina zuwa".
Malam Ishu fita yayi daga d'akin, ya kai kamar minti sha biyar da fita sai gashi ya dawo da gallon k'anana guda biyu a hannun shi. Malam Ishu mik'ama Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Hajiya ga wannan arik'a bashi wannan na farar jarkar sha biyun rana d'aya da kuma sha biyun dare, wannan kuma safe , rana, dare, insha Allah kome ke damunsa Allah zai mai maganin shi, duk sati zaku rik'a zuwa kuna amsar mai, yanzu idan ya shanye wannan sai muga yadda jikin nashi zai yi, sannan insha Allah za'ai mai saukar alk'ur'ani mai girma".
Godiya sosai Hajiya Turai tai ma Malam Ishu, sannan ta bashi kud'i masu yawa sosai, sannan sukai mai sallama suka tafi".
Su Hajiya Turai suna a mota suna tafiya, Hajiya Turai ta kalli Baba Lami, ta ce, "Baba Lami nikam ina tunanin yadda Habib zai sha maganin nan, Kinga dai yadda akeyi da shi, sannan wa zai rik'a tashi yana ba Habib magani sha biyun dare?, ni kuma Baba Lami kinga yadda ya ke min, Wallahi duk hankalinama ya tashi narasa yadda zanyi gaba d'aya ". Hajiya Turai ta idasa maganar tana share hawayan da ke zibo mata".
Shiru Baba Lami tayi, dan itama tun d'azu tunanin da take yi kenan. Ahaka dai suka isa gida batare da Baba Lami ta ce komai ba".
Bayan Bilya ya yi parking sun fiffita a motar ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, "Na bani Bilya namanta tun d'azu na tura Hassana kema Habib abin break fast, Wallahi ina zuci-zucin ince ma mubari ya gama ku fitar da Hassana sannan mu tafi, amma Wallahi na manta sham, da nazo na shiga mota kawai muka tafi, dan Allah muje mugani ko yabarta ta fita".
Wajan window Habib Hajiya Turai ta tsaya ta lek'a, zaune ta iske Hassana kamar jiya, Habib kuma na rik'e da hannunta. Hajiya Turai cikin damuwa ta kalli Bilya ta ce, "Bilya ka gani ko, ashe har yanzu yarinyar nan na nan yak'i barinta ta fita! ". "Tom Hajiya ni kaina Wallahi abun shiru kawai nake yi, amma ita kanta Hassana yanzu ta fara ban tausai, dan ita ke jinyar Oga Habib kusan".
Shiru Hajiya Turai ta yi, Sannan ta ce, "Bilya kira Musa dan Allah ku fito da ita, nasan k'ila ko abinci basu ciba su duka, inda babu wanda zai yi hausar kai musu".
Bilya kiran Musa ya yi shuka shiga d'akin Habib don fito da Hassana. Habib ko na ganin su ya tashi da saurinsa ya yo kansu.
Bilya da Musa rik'e Habib suke ita kuma Hassana ta tashi ta fita da saurinta, sannan suma suka saki Habib d'in suka gudu".
Hassana sauran kad'an tabige Hajiya Turai, dan bata san da ita ba, saboda fitowar da tayi da gudu. Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, ta ce, "Sannu ko Hassana Allah ya yi miki albarka". Da Ameen Hassana ta amsa. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Bakici abincin rana ba ko? ". kai Hassana ta d'agama Hajiya Turai. Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Hassana ya sha kunun da kika kaime? ". "Eh Hajiya yasha sosai dan duka ya shanye shima". Hajiya Turai hannun Hassana ta kama tace, "Sannu da k'okari, muje falona kici abinci kema".
Hajiya Turai tana rik'e da hannun Hassana har suka isa falon ta. Hajiya Turai d'aya daga cikin masu aikinta ta sa ta had'ama Hassana abinci, sannan tasa suka kai mata kan derning space . Hassana ko daya ke yunwa ta ke ji dan ko karyawa bata yi ba Hajiya Turai tasa ta kaima Habib abin k'arinshi. Sosai Hassana ta ci abincinta".
Hajiya Turai ko tunaninta taya zata kuma rok'on Hassana ta kaima Habib shima.Hajiya Turai so take ta rok'i Hassana amma sai ta kasa dan tana tsoran kar Hassana tai mata kallan mai son kanta da yawa. Haka Hassana ta gama cin abincinta ta tashi ta yima Hajiya Turai godiya ta tafi. Hajiya Turai nason yima Hassana magana ta rok'eta ta kaima Habib abinci, amma ta kasa, haka nan ta yi hak'uri badan taso ba tana gani Hassana ta tafi".
Hajiya Turai bayan ta yi Sallah ne, ta aika aka kira mata Baba Lami. Bayan Baba Lami ta zo ne, Hajiya Turai kallanta ta yi tace, "Baba Lami nace taya kike gani Habib zai sha maganin nan? ". Shiru Baba Lami ta yi, sannan ta ce, "Hajiya ni gani nake kamar yadda kike sa Bilya da Musa su kwace Hassana daga hannun Oga Habib, haka zaki sasu su d'ura mai maganin nan". "Tom Baba Lami idan hakan ta yuwu na daran fa? ". Shiru Baba Lami ta yi, dan itama shi tafi tunani, sannan zuwa can ta ce, "Hajiya ni gani nake kima Bilya da Musa magana su rik'a tsayawa wajan Habib har lokacin shan maganin, alabashi idan sun bashi magani sai su koma inda suke kwanciya su kwanta, alabashi sai ki biyasu, bare kuma nasan daga Bilya har Musa sunada kirkin yi miki haka". Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta ce, "Baba Lami kina ganin ba damuwa zasu yi ko? ". "Sosai ma kuwa, Hajiya ai Bilya da Musa dukansu 'yan gidan Oga Habib ne, ina da tabbaci zasu yi".
Hajiya Turai kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba kiramin Bilya sai muyi magana da shi, inji ta bakinshi".
Baba Lami fita tayi sai gata da Bilya sun dawa. Baba Lami kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Hajiya ga Bilyan nan naki rashi"., Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, "Bilya dan Allah tai mako zakai min?, magani akaba Habib ya rik'asha sha biyun rana da na dare , shine dan Allah nake nai man alfarmarka kai da Musa kurik'a bashi, zan biyaku dan Allah Bilya ku yi min wannan tai makon". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin rok'o".
Shiru Bilya ya yi sannan ya ce, "Hajiya Oga Habib matsayin shi agunmu ya wuce haka zamu iyamai abinda yafi hakama, amma matsalar guda d'aya ce, na farko dai kinsan baya yarda da kowa yashiga inda yake, na biyu kuma Hajiya kina gani jiya da aka kaima abinci yadda aka kaishi haka aka d'akko shi, amma idan kina da wata shawarar sai mubi". Shiru Hajiya Turai ta yi bata ce komai ba".
Baba Lami ce ta ce, "Bilya ni dama shawarata sai inga d'ura mai za kuyi, amma dama indai ta lallimice ai ba zai shaba".
Bilya gudin kar Hajiya Turai taga kamar yak'ine yasa ya ce, "Shikenan ,Yaune za'afara bashi magani? ". Baba Lami ce ta amsa mai ta hanyar cewa"Eh".
Hajiya Turai rubutun ta d'akko ta mik'ama Bilya ta ce, "Bilya wannan shine zai sha yanzu, wannan kuma shine na sha biyun daran,wannan kuma sai gobe zai fara shashi, dan Allah sai kai ma Musa bayani yanzu sai ku bashi". Bilya amsar rubutun ya yi batare da yace komai ba yafita".
Bayan fitar Bilya ne,Hajiya Turai ta kalli Baba Lami ta ce, "Baba ni ko duk yau banga Farida ba? ". "Nima kam yanzu nagama zancan azuciyarta". Cewar Baba Lami".
Farida ko tun safe tabar gidan, tana ganin fitar su Hajiya Turai itama ta fita, dama yaune sukai da Mahaifiyarta Hajiya Murja zata je. Bayan Farida ta isa gida ne, Hqjiya Murja kallanta tayi tace, "Farida sanin kankine bamu da wani wada tattan lokaci amma shine kikak'i zuwa da wuri, tun shekaran jiya da naima Malam magana aiki ya lallace ya ce kizo da wuri dan asan ta inda za ab'ulloma lamarin amma kikak'i sai yau! ". Farida cikin shagwab'a kamar zata yi kuka ta ce, "Mommy kefa kika ce min bakya so Hajiyar Oga Habib tasan zanzo, tom yaune suka tai zaria naimanma Oga Habib magani, shine fa suna tafiya nasamu nafito". Shiru Hajiya Murja ta yi, sannan ta ce, "Shikenan tashi muje gidan malam". Farida tashi ta yi suka tafi a motar Hajiya Murja".