Sashe 7
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ba'ita ya ke kallo ba hankalinsama akan laptop d'in gabansa ya ke, ba akanta ba. Hassana muryarta na cracking ta ce, "Ni yar kano ce, mamana da babana duk 'yan jahar kano ne, Babana nada mata biyu. matar Babana tana da fad'a sosai, kuma macece mai son kanta da yawa. Babana tunda ya auri mamana Allah bai bata haihuwa ba, hakan yasa kakata wato Mahaifiyar Babana ta matsama Babana ya k'ara aure. Babana ya auri Umma Rabi ba dad'ewa Allah ya bata ciki ta haifi Aunty jamila, sai da Umma Rabi ta haihu uku sannan Allah ya ba Mamana cikina, tom kuma itama Umma Rabi lokacin tana da ciki, kusan tare sukayi rainon ciki ita da Mamana. Mamana ta haihu da kwana biyu Umma Rabi ma ta haifo yarinyarta mace. Hakan yasa Babana ya ce, sai dai ahad'a sunan mu. Tom Mamana dama tunda ta haifeni bata da isassar lafiya, hakan yasa kwanana biyar aduniya Allah ya yi ma Mamana rasuwa. Babana sosai hankalinsa ya tashi da mutuwar Mamana saboda yafi jin dad'in zama da ita fiye da Umma Rabi. Tom mamana da ma ita ma ita kad'aice awajan Iyayanta kuma Allah ya yi masu rasuwa dad'ewa, hakan yasa Babana badan ya soba sai dan bashi da yarda zai yi ya d'auke ni ya ba Umma Rabi ni, ya ce ta had'amu ta shayar damu tare da 'yarta. Da da farko Umma Rabi ta Nuna ma Babana baza amsheni ba, amma sai Babana ya nuna mata dole ta amsheni, in da bai san Wanda zai kai ma niba. Hakan yasa dole Umma Rabi ta amsheni. Ranar suna Babana ya sa mana Hassana da Usaina ni da yarinyar Umma Rabi. Nasha wahala sosai awajan Umma Rabi dan ko kuka nake sai taga dama ta ke ban nono insha. Kuma koda zan riga Usaina tashi in dai Usaina ta tashi tom Umma Rabi sai ta d'auki Usaina ta lallasheta ta yi shuru sannan koda zata kulani. Ahaka har muka girma. Tunda nafara wayau na fahimci Umma Rabi tafi son Usaina akaina. Babana dawuri ya samu Islamiya, ita Usaina bata cika zuwa ba saini, saboda ni kona ce ba zani ba dole za'a turani. Tun ina 'yar k'arama ta na iya duk wani aikin gida, dan hatta wankinmu Nida Usaina ni ke mana, acewar Umma Rabi ni ce babba. Babana duk lokacin da zaizo gida ya iske ina aiki sai yi ta fad'a ya ce Usaina tazo muyi tare. Wannan abinda da Babana ke yi shiya k'ara jawo min tsana sosai gurin Umma Rabi. Ahaka rayuwa taita tafiya har muka girma , muka shiga secondary school. Tom da akwai wani teacher mu, wanda ya ke kula da duk abinda ya shafemu Nida Usaina, sai dai yana yawan yi min complain, akan wai Usaina ta fi ni tsafta, ni dai ban tab'a fad'amai wani abuba game da gidanmu, shine ya tsinto labari acikin gari. Tunda teacher Kabir ya tsinci labarin halinda nake, ya zamana yake yawan yimin kyautar kud'i. Sosai teacher Kabir ke min hidima hakan yasa har Babana ya sanshi. Muna gama j. S. E. Babana ya ce, bazamu cigaba da karatuba aure zai mana. Tom dama ita Usaina akwai wini dake zuwa gunta harma ya yi ma Babana magana, ni kuma dama teacher Kabir shike Sona shima ya naimi izini gurin Mahaifina ya kuma bashi. Lokacin da Babana ya je ma da teacher Kabir maganar ya turo manyasa gidanmu ai maganar aurena da teacher Kabir . Teacher Kabir rok'on Babana ya yi akan dan Allah ya barni in kamma secondary school sannan. Kasan cewar Babana na son tarayyata sosai da teacher Kabir yasa ya yarda da abinda teacher Kabir ya ce. Koda Babana ya kaima Umma Rabi maganar saina kamma secondary school sannan za ai aurena, cewa ta yi itama Usaina abarsa sai ta kammala sai ayi duka tare. Aiko haka akayi. Muna S. S. S 3 first term, Babana ya sa ranar aure na da Teacher Kabir. Ita kuma Usaina da wani Jamilu d'an layinmu. Umma Rabi bata son tarayyar Jamilu da Usaina ko ka d'an bakamarma da taga teacher Kabir na min hidimaba sosai, ita kuma Usaina babu abinda ke shiga tsakaninta da Jamilu na kyauta. Da akwai wata rana teacher Kabir ya kawo min waya. Wannan kyautar da ya yi min tab'ata ma Umma Rabi rai sosai,hakan yasa tace sai dai in maida mai wai in ya auran ya sai min agidansa. Babana koda yazo yaji abinda Umma Rabi ta ce hanawa ya yi in maida ma teacher Kabir wayar shi". Hassana shiru ta yi, tana goge hawayanta saboda wani kuka da ke son k'wace mata, saboda tunowar rabuwarta da teacher Kabir ta k'arshe da ta yi. Hassana cikin murya mai kama da ta kuka taci gaba da magana kamar haka, "Ranar da bazan mantataba arayuwata, ita ce ranar wata laraba, Iyayan teacher Kabir suka zo gidan mu wai d'ansu Kabir ya janye maganar auran shi dani ya mai da ta kan Usaina. Bani ba har Babana ya girgiza da jin haka, mamaki da al'ajabi suka cika shi, saboda shi kanshi asanin kanshi Kabir bama sa wani jutuwa da Usaina, sai yau rana tsaka wai ace Kabir ya janye maganar auran shi da Hassana ya maida kan Usaina. Babana cema Iyayan teacher Kabir ya yi tom su bari zaiji daga bakin Kabir d'in sannan. Aiko haka akayi Babana kiran teacher Kabir ya yi ya tambayai ya akan maganar da Iyayanshi suka zo da ita". Bud'ar bakin teacher Kabir sai cewa ya yi, "Eh hakane shi Usaina ya ke so". Wannan maganar sosai ta d'aga hankalin Babana. Washe gari da safe Babana ranshi b'ace ya je d'akin Umma Rabi. Babana nazuwa ya kalli Umma Rabi, ya ce, "Rabi ina son kisan wani abu duk k'ula-k'ular da kika yi, ki ka maida auran Hassana ya koma kan 'yarki tom tun wurima ki warware shi, dan ni bazan tab'a aura auran Usaina da Kabir ba, garama kisani tun wuri. Haka Babana ya gama fad'anshi Baba Rabi bata tanka mai ba. Abu kamar wasa yazo ya zamana gaske, dan teacher Kabir idan yazo gidanmu sai inga Usaina taje suna hira, ni ko ko gaisuwata baya amsawa. Abin ya daman Sosai, hakan yasa na kaima Babana k'arar teacher Kabir. Babana kallona ya yi cikin alamun tausaya min, dan ya lura ina son teacher Kabir sosai. Hakan yasa Babana cikin lallashi, ya ce, "Hassana kinsan dai wani baya aurar matar wani ko?, haka kuma wata bata auran mijin wani, inji hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Tom Hassana dan Allah karki tambayan dalili dan nima ban sani ba, amma ina so ki hak'ura da Kabir ". Wannan magana da Babana ya fad'a ji nai kamar ya lumamin wuk'a azuciya, dan Allah ya sani ina son teacher Kabir sosai, kodan shine saurayina na farko. Kuka na fashema Babana da shi jin abinda ya ce. Babana duk wata magana mai dad'i da zai fad'amin wadda zata sa in yi shiru ya fad'amin, amma ina na kasa. Sosai kukana ya d'agama Babana hankali. Ni ko kafin kace me sai ciwan kai tsabar kukan da nayi haka kaina ya yi ta min ciwo. Aranar dai da ciwan kai na kwana. Iyayan Kabir ko sun yi ake kamar me akan Babana ya maida auran Hassana da Kabir kan Usaina ya k'i. Umma Rabi ko ganin Babana yak'i amsar maganar Usaina da Kabir, yasa taturasu wajan k'aninta. Tom da ya ke shima k'anin nata gashi ga irin shi. Hakan yasa batare da binciken komai ba, ya amshi maganar, nan dai ya yi jagoranci aka tsaida ranar auran Usaina da Kabir, wata biyu masu zuwa. Wannan ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Wannan kukan da nayi sosai ya tadama Babana hankali. Kafin kace me hawan jinin Babana ya tashi. Washe gari da safe shiri-shiru Babana be ne meniba. Hakan yasa na lallab'a na tashi dan kaina sosai ya ke min ciwo. Ina tashi d'akin Babana natura nashiga. Ganin Babana kwance kuma harna tura d'akin bai tashi ba, yasa na k'arasa gun shi ad'an tsorace. kiran sunan Babana nayi ina bubbuga k'afarshi amma shiru. Kuka na fasha dan duk da ban san Mutuwa ba jikina ya bani kamar babu rai ajikinsa. Babana ya tafi yabarni yatafi in da bazan sake ganinsa ba. Haka akai zana'izar Babana. Nayi kuka sosai dan Babana shine abokin shawara, shine abokin firata idan yana gida, shine wanda abu in yasaman nake fad'amawa sai ko teacher Kabir, tom shima anrabani da shi. Bayan wata d'aya da rasuwar Babama, abubuwa sun cakud'e min, ga aiki na gidan duk ni ke yi, wanke-wanke, shara, girki, wankin kayan mu. Ana gobe d'aurin auran teacher Kabir da Usaina na gudu saboda zuciyata bazata iya jure ganin auran teacher Kabir da wata ba, ba ni ba............