← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 78

Sashe 3

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta kirani, yanzu , akan in zo ta far.......... ". Habib cikin tsawa ya katse, Bilya ya ce, " Bilya kana ko da full sense, awannan lokacin zaka kirani kana min wannan maganar!?, Yarinya kuma da ka ke magana,duk yadda kaga dama kayi da ita bai shafan ba, karka kuskura ka sake min magana akanta!. ". Wata zufa mai zafi ce ta fara karyoma Bilya. Ko tunanin mafita Bilya bai fara yi ba, kira ya kuma shigowa wayar shi. Bilya koda ya duba yaga Number likitar nan ce, Bilya cikin rashin sanin abinda zai ce mata ya yi picking d'in call d'in. Tun kafin ta yi magana, Bilya ya rigata da cewa, " Ki yi hak'uri kinga yanzu dare ya yi ba damar in zo Kano, amma zuwa gobe zaki ganni". Likitar jin abinda Bilya ce yasa ta kashe wayarta. Bilya sosai abinda Habib ya yi mai ya b'ata mai rai, taya zai ta kuramai ya d'auki ya rinyar, yanzu kuma yazo yana nai man lik'amai bala'i. Bilya shiru ya yi, ya na nazari, ya ce, Tom ni yanzu ko ma kano nace zan je in d'akko ta ina zan kaita. Bilya da sauri ya ba kanshi amsa da cewa, Wallahi sai dai in barma likitar ita, idan ma ta sake kirana bazan d'agaba. Bilya blocking number likitar ta ya yi. Cikin jin dad'in shawarar da yankema kanshi bacci ya kwasheshi. Washe gari misalin k'arfe goma na safe, kamar yadda Habib ya saba sai ya je office sannan ake kai mai abin break fast , haka aka yi. Bilya ko dama so ya ke ya yi magana da Oga Habib , amma bai samu dama ba, dan tunda ya d'akko shi da safe ya ke waya har suka isa company bai dai na ba. Wanan shine ya hana Bilya yi ma Oga Habib maganar Yarinyar. Ga shi kuma tunda safe likitar ta da mai da kira, dan tana ganin ya yi blocking Number ta ta kira shi da wata Number. Hakan yasa Bilya ya ke son ganin Ogan nashi sosai. Gashi in dai Habib ya shiga office d'in shi ganin shi na da wuya sosai, sai dai in Allah yasa ya fito. Bilya na nan tsaye yana nai man hanyar da zai bi yaga Oga Habib , Sai ga masu kawo mai break fast sun iso, tattawan mata ne guda biyu, amma ba wai sun tsufa bane sosai. Bilya na ganinsu cikin da bara, ya yi gurin su, ya ce, "Baba lami sannunku da k'ok'arin kula da Ogan mu ". Tsofaffin cikin girmamawa su ka amsa ma Bilya. Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, "Baba abin k'arin Ogan mu ne ko? ". "Eh Bilya shi ne". Suka bashi amsa. "Baba ku kawo dan Allah in kai mai dama ina son magana da Oga Habib Wallahi amma narasa yadda zan yi". Wadda ya kira da Baba lami, wayayyar tsohuwa, murmushi ta yi, ta ce, "Tom Bilya ka dai son ko mai,ka san babu wanda Hajiya turai ta yadda ya ba Oga Habib abinci hannu da hannu sai mu, tom kuma dai kasan Oga Habib yadda ya ke abu kad'an za kai mai babu ruwansa da bashi ya d'auki mu aiki ba, yanzu sai ya da katar da Mutum aiki ba ruwansa, dan haka kayi hak'uri, amma idan nashiga zan gwada mai magana kana son ganinsa k'ila idan akaci sa'a yabari ka shiga". Godiya Bilya ya yi ma Baba lami. Sannan suka shiga. Su Baba lami sun dad'e atsaye suna jiran Comment. Amma shiru. Habib sai da ya gama abinda ya ke sannan ya basu izin shigowa. Bayan sun Baba lami sun kaima Habib abin break fast ne. Har za su fita, Baba lami ta yi k'arfin halin bada sautin Bilya. Baba Lami cikin girmamawa kamar yadda ta saba ba Habib d'in, ta ce, ", Oga Habib, dama yaran nan ne, driver ka, Bilya ya ke Son magana da kai wai". Habib batare da ya kalli Baba Lami ba, ya ce, "Ba yanzu ba". Baba Lami fita ta yi, tana alawadai da dukiyar da zata sa Mutum ya d'auki kan shi haka, kamar yadda Habib ya d'auki kan shi. wata zuciyar ta ce mata tom kodai kyan shine yasa ya ke yin haka ne.Nan dai su Baba Lami suka fito suna mai Allah wa dai da ji da kai da tak'ama irinta Habib. Bayan su Baba Lami sun fito ne. Bilya ya k'arasa in da suke da saurinsa ya ce, "Yauwa Baba ya ce in shiga ko? ". Baba Lami cikin nuna rashin jin dad'in ta, ta ce, "ka yi hak'uri Bilya kasan yaron nan dama ba wai mutunci gare shiba, bai ganin kowa da Mutun ci, Wallahi ya hana. Sai dai ka yi hak'uri idan ya fito, ko in za ka kaishi wani gun". Bilya cikin d'an bacin rai ya ce, "Wallahi Baba Oga Habib na mulkamu yadda ya ke so, amma babu da muwa, ko mai nada lokaci, akwai lokaci". Baba Lami ta fiya su kayi bayan sun ba Bilya Hak'uri. Bilya ko yana nan tsaye yana ganin fitowar Habib amma shiru, har akai Sallar azahar. Bilya na nan tsaye kira yak'a shigowa wayar shi tai ringing, Bilya na dubawa yaga Number likitar ce, sosai gabansa ya fad'i dan k'aryarsa ta k'are. Biya na d'auka ya ce, "Ki yi hak'uri dan Allah nima banso haka ta faruba, ko ba komai na k'arya alk'awarin da nai miki, amma Wallahi duk abinda kika ga ya faru ba laifina ba ne laifin Ogana ne, amma bari yanzu in turomiki Number sa, dan Allah ko kinkira bai d'aga ba karki gaji ki ta kira zai d'aga". Bilya na kashe kiran ya tura mata Number Habib. aiko tana ganin Number ta danna mata kira, dan bata son yau ta sake kwana mata agida. Habib ko na zaune a Office d'in shi yana aiki a laptop, kira ya shigowar shi. Habib ko duba Number bai tsayiba ya ci gaba da aikinsa. Ita ko da yake taji abinda Bilya ya ce mata, hakan yasa taita kira. Habib cikin jan tsaki ya d'aga kiran ya sa akunne, yana sauraran mai magana. Ita ko likitar tana jin and'aga kiran ta ce, "Ranka shi dad'e dan Allah, kuzo ku amshi amanar da kuka ban dan Allah ". Habib cikin rashin fahimtar maganar, ya ce,"Wrong Number ". Yana fad'in haka ya katse kiran. Likitar ko bata gaji ba k'ara kira ta yi, cikin b'acin rai ta ce, "Oh wai kunyi satar Yarinyar ne kuke tsoran asirinku ya tuni, koko ku 'yan kidnappin...... ". Habib cikin daka tsawa ya tsayar da ita, yana kunfar baka. Magana ya ke son yi ya kasa, kawai sai ya kashe wayar shi baki d'aya, dan shi harga Allah ya manta wata yarinya da suka kai hospital. Bilya ko tunanin ko anda ce ne, yasa yakira, likitar dan ya ji yadda su kai da Habib. Likitar cikin b'acin rai ta ce,ma Bilya "Karka rainamin hankali malam, yarinya kuma ku kuka sani, amma daga yau na gama kwana da ita". Bilya hak'uri ya ba likitar sosai sannan ya ce, mata,"Wallahi ba maganar wasa gobe zai yi samma kon zuwa kano d'in ". Ai ko haka akayi Bilya tun da daddare ya nemi permission gurin Ogan shi, akan tafiya kano. Washe gari da wuri Bilya ya tafi kano, hakan yasa 12:00pm a kano tai mai. Bilya bacin ya biya likitar hak'uri Sosai ya ba ta.Sannan ya zauna yana jiran fitowar 'yar tsuntuwar tasu, shiga Ogan shi, wanda shi ya ma manta da batunta. Bilya na nan zaune 'Yar tsuntuwar su ta fito sanye ta ke da wata doguwar riga ta atamfa wadda likitar ce ta bata dan ganin bata da kaya, yasa likitar ta bata a tamfar. Bilya kallanta ya yi, sannan ya ce, " 'Yan mata ke 'Yar wana gari ce, yanzu in kaiki gidan ku, dan mu ahanyar mu ta zuwa kano muka tsince ki". Matashiyar budurwar da bazata haurama shekara goma sha bakwai ba. Cikin siririyar muryarta ta ce, "Ni marainiya ce, bani da kowa, dan Allah ka tai ma ke ni". Bilya da tausayi ya ke kallanta, dan shi aganinshi tabbas marainiyarce. Bilya shiru ya yi, dan yasan bai da in da zai kaita. Ito ko Yarinyar ganin Bilya ya yi shiru alamar ba zai tai maka mata ba, ya sa, ta ce, "Dan Allah katai makan Allah banda kowa". Bilya cikin tausaya mata ya ce, "zan tai make ki ki, amma tai makon ba mai tsawo bane, zan tai make ki ne kafin Hajiya turai ta dawo,kuma ni ba nan nake ba Abuja nake kin yarda zaki bini?, Sannan kuma duk sanda Hajiya turai ta dawo zaki kama gabanki , kin yarda? ". Da sauri ta ce, "Eh na yarda na godee. Bilya tashi ya yi Yarinyar na binshi aba suka je in da ya yi parking d'in motarsa da Ogan sa Habib ya yi masa kyautarta, suka tafi. Suka kama hanyar Abuja . Kasan cewar Bilya yana gudu sosai da mota, hakan ya sa, ana Sallar magriba suka shiga gida. Allah ko ya tai maki Bilya sosai dan lokacinda suka shiga ba kowa, duk 'yan aikin gidan sun shi cikin gida, hakan yasa tana fitowa daga mota Bilya yaja hannunta da sauri ya kaita d'akin shi. Dan yasan gidan cike ya ke da magulmata. Bilya dama tun kafin ya iso ya kira Baba lami ya yi mata bayanin ko mai, hakan yasa Bilya na isowa ya kira Baba Lami ya sanar da ita sun iso. Baba lami na shiga d'akin Bilya. Bilya ya kalleta ya ce, "Tom Baba kin san dai yadda gidan nan ya ke, Baba lami ga Yarinyar nan, dan Allah ta zauna gunki kafin Hajiya turai ta dawo". Baba lami batare da taima Bilya magana ba, gudun matsala dan ba wani lokaci sosai,Baba Lami taja hannun 'Yar tsuntuwar ta yi d'akinta da ita da sauri. Bayan sun shiga d'akine Baba Lami ta kalli Matashiyar budurwar ta ce, " 'Yan mata ya sunan ki? ". Cikin sanyin murya ta ce, "Sunana Hassana". "Yauwa Hassana dan Allah ki yi zamanki nan, karkisake ki fita waje, muta nan gidan nan magulmata ne, dan Allah ki kula, kafin Bilya ya samarmiki gurin zama". Sosai Baba Lami ke k'ok'arin b'oye Hassana. Sai dai
Chapter 3 · 0% Book details