Sashe 28
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Malam mai biyan buk'ata dole, mik'ama Farida maganin ya y, ya ce, "ki daure ki yi maganin nan yadda ya akace, buk'atarki zata biya 'yan mata". Cikin jin dad'i Farida ta ce, "Allah yasa Malam". Dariya bak'in k'aton wanda aka kira da Malam ya yi, ya ce, "Karki damu buk'atarki zata biya, aikin da mukaga baza mu iyaba bama karb'arsa, ke ko mun hango nasara a tattare da aikinki, nine Malam mai biyan buk'ata dole, buk'atarki zata biya yarinya".
Kud'i masu yawa sosai Hajiya Murja taba shi, sannan su kai mai sallama suka tafi".
Hassana da Hajiya Turai zaune bakin bed d'in Hajiya Turai. Hajiya Turai hannun Hassana ta kamo, ta ce,"Hassana nasan zaki yi mamakin shigo da ke bedroom d'ina da nayi".Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "Hassana Allah ya jarabceni, ya d'orama Habib lallurar da baya son kasan cewa da ni, Hassana zuciyata na ciwo sosai a duk sanda na kalli Habib naga halinda ya ke". Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Hassana anban magani in ba Habib, amma babu dama, taya zan ba Habib magani baya yarda in je inda yake... ". Kuka ne ya kwace ma Hajiya Turai ".
Hassana cikin damuwa da tashin hankali ganin Hajiya Turai na kuka, ta ce, "Hajiya dan Allah ki yi hak'uri, kibar kukan, insha Allah Allah zai ba Oga Habib lafiya".
Hajiya Turai saukowa ta yi daga bakin bed d'in, ta zuk'unnama Hassana ta koma hannun Hassana, ta ce, "Hassana dan Allah ki tai makeni ki auri Habib". Hassana da ke zaune bata san-sanda ta mik'e tsayeba tana kallan Hajiya Turai, cikin yana yin furgita da jin abinda Hajiya Turai ta ce".
Hajiya Turai ma ta shi tayi tsayan tana kallan Hassana ganin yadda furgici da tsoro ya bayyana a idon Hassana. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana dan Allah ki tai makeni ki auri Habib, banda mai ba Habib magani, Hassana ke kad'ai ce Habib ke yarda da ke, in ba ke kika bashi maganin nan ba, bazai shaba, kina ganin ko abinci indai bake ba baya ci". Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta ce, "Hassana dan Allah zaki yardar ki auri Habib? ". Hassana kai ta rik'a girgizama Hajiya Turai , tana zazzare ido kamar wadda tai k'arya asirinta yatonu".
Hajiya Turai itama cikin sanyin murya mai cike da fargaba ta ce, "Hassana dan Allah ki auri Habib, duk abinda kike tunani bahaka bane, idan yau Habib ya ji sauk'i shikenan". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana zaki aurai? ". Still Hassana kai ta girgizama Hajiya Turai "..
Shiru Hajiya Turai ta yi, Sannan ta ce, "Hassana nasan k'ila kina tsoran halin Habib ne shiyasa kika k'i yarda da Auran shi, ni nai miki alk'awari Hassana insha Allah babu abinda zai faru, kamar yadda nace miki daga yaji sauk'i shikenan". Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta kamo hanun Hassana ta ce, "Hassana kin yarda dan Allah? ". Hassana kai ta girgizama Hajiya Turai tana zubda hawaye".
Hajiya Turai hannu tasa tana gogema Hassana hawayanda ke zuba aidonta, ta ce, "Kishiru kinji my daughter, nasan dama maganar zata zo miki wani iri, amma na baki nan da gobe ki yi tunani dan Allah, kinji?, idan har kika yarda da buk'ata ta auran Habib, nai miki alk'awarin baki duk abinda kike so, ki je kiyi tunani kinji My daughter, idan Allah yasa kin yarda da buk'ata ta gobe nake son ayi komai, saboda shan maganin Habib".
Hajiya Turai na sakin hannun Hassana, Hassana ta fita da saurinta".
B'angaran su Farida kuwa tare da Hajiya Murja suka dawo gidan Hajiya Turai. Bayan Hajiya Murja ta yi parking a parking space agidan Hajiya Turai. Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida yanzu taya kike ganin zaki basu wannan maganin na rufe bakinsu da maganar auran nan? ".Farida kamar jira take ta ce, "Wallahi Mommy nima abinda nake tunani kenan, dan bana son asamu kuskure koka d'an". Shiru Hajiya Murja ta yi sannan ta kalli Farida ta ce, "Har yanzu Balaraba kema Hajiya Turai girki? ". "Eh Ita ke yi". Murmushi Hajiya Murja ta yi, ta ce, "Yauwa komai yazo da sauk'i, dan Balaraba nada son kud'i sosai, nasan zata ita yin komai dan kud'i, dan haka da ita za a had'a kai ayi aikin nan". Farida cikin gamsuwa da maganar Mahaifiyarta ta ce, "Wow Mommyna kuma Wallahi haka ne, Balaraba zata iya, amma na Oga Habib d'in fa, dan yanzu yarinyar ta ce bata k'ara shiga kaima Oga Habib abinci ko magani, shinema da lilin da Hajiya ta naimi had'asu aure, shigiya k'ilama tasan Hajiya za tai hakane yasa ta ce haka, tom aiko bata isaba dan ita ba ajin Oga Habib ba ce Wallahi! ".
Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Yanzu ke babu yadda zaki ma yarinyar ta kaima Habib maganin?, ai wayo zaki mata ta kai mai maganin idan ta kai mai, irin minti biyu haka, sai ita kuma kisan yadda zaki bata tasha, idan tasha sai ki tura ta d'akin da niyyar d'akko miki wani abun, ke koma ita bata shaba indai taba Habib d'in yasha shikenan, inda Malam ya ce indai shi yasa ba dole bane ita sai ta sha". Farida cikin jin dad'i ta rungume Hajiya Murja, ta ce, "Sai Mommyna, aikin ki na kyau". Dariya Hajiya Murja ta yi tace, "Tom ba dole in dage ba, daughter zata gudu tabarni ni kad'ai".
Hajiya Murja kallan Farida ta yi ta ce, "Muje Farida mugaisa da Hajiya Turai in tafi gida".
Hajiya Turai na zaune a falonta ta yi nisa acikin tunani su Hajiya Murja suka shigo ita da Farida. Hajiya Turai cikin sanyin murya ta amsa sallamar da sukai.
Hajiya Murja cikin nuna damuwa ta ce, "Hajiya ai ni fushima nake dake, dan bacin hankalina yak'i kwanciya Allah da bazan zo ba, wai yanzu ace lallura ta samu Habib amma bazaki fad'amin ba, sai jiya da Farida ta je nake ji". Hajiya Turai cikin al'ajabi da mamakin furicin Hajiya Murja, ta ce"Ki yi hak'uri rud'ewa nayi, dan abin ya taba k'wak'walwata sosai"."Wallahi nima bikiji yadda naji ba, da Farida ta kaimin labari jiya, dan bacci gagarata ya yi, tom yaza mu yi sai dai fatan Allah ya bashi lafiya". Da ameen Hajiya Turai ta amsa'".
Nan dai Hajiya Murja taita ba Hajiya Turai baki akan kar ta d'ora ma kanta damuwa insha Allah Habib zai ji sauk'i.
Ita dai Hajiya Turai da uhmmm kawai ta ke binta".
Hajiya Murja ganin Hajiya Turai wani iri ba tai tunanin komai ba, dan aganinta ciwan Habib d'in ne yasa ta ke ma ta haka. Hakan yasa ta tashi taima Hajiya Turai sallama tare da addu'a Allah yaba Habib lafiya.
Ita dai Hajiya Turai da ameen ta ke amsa mata".
Farida tashi ta yi zata raka mahaifiyarta. Bayan sun fita daga part d'in Hajiya Turai ne. Hajiya Murja ta kalli Farida ta ce, "Yanzu Farida ina zanga Balaraba? ". "Tana site d'in worker's d'in gidan, bari in kirata".
Farida zuwa kiran Balaraba ta yi, babu dad'ewa sai gata da Balaraban sun dawo tare".
Balaraba cikin girmamawa ta gaida Hajiya Murja. Hajiya Murja kallan Balaraba ta yi, ta ce, "Balaraba wani aiki nake son ki min, zan biyaki kud'i masu yawa, kuma bana son asamu kuskure, zaki iya? ". Balaraba cikin girmamawa ta ce, "Hajiya ai babu abinda zaki sani wanda bazan iyaba, umarninki kawai nake jira". Hajiya Murja muskilin murmushi ta yi, sannan ta ciro kud'i masu yawa taba Balaraba, ta ce, "Gashi wa innan somin tab'ine". Maganin da bokan Hajiya Murja ya basu taba Balaraba, ta ce, "Balaraba a abincin zaki dafa yanzu nake son kisa maganin nan, zaki iya? ". Shiru Balaraba ta yi, sannan ta ce, "Hajiya zan iya, amma tsorona d'aya idan ya kasan ce nakisa ne, saboda bincike zai iya fad'owa kaina". Hajiya Murja cikin b'acin rai ta kalli Balaraba ta ce, "Balaraba kinada hankali kuwa! ,tom bana kisa bane,wani abu na ke nema gun Hajiya Turai". Balaraba cikin yanayin fargaba ta ce, "Hajiya indai bana kisa bane zanyi, amma indai shine bazan iya ba, dan gaskiya ina tsoran tonuwar asiri". Hajiya Murja kallan Balaraba ta yi ta ce, "Balaraba bashi bane, idan kinsan bazaki iyaba kiban abuna, dan Wallahi dan kika b'ata min aiki bazan barki ba". Balaraba jin Hajiya Murja ta kuma jaddada mata bana kisa bane ta ce, "Shikenan Hajiya zan iya wallahi, ya za ai da maganin? ". "A abinci zaki zuba shi".
Hajiya Murja sai da tajama Balaraba kunne sosai akan yin wani kuskure, sannan ta tafi".
B'angaran Hassana ko tun bayan fitowarta daga part d'in Hajiya Turai, ta ke zaune inda ta ke, ta yi ta gumi damuwa duk ta isheta, dan ita gaskiya baza ta iya auran Habib ba, dan shid'in tasan ba ajin auranta bane, Habib mijin first class girl's ne ba itaba, wadda ya kema kallan k'ask'antarta,dan haka cema Hajiya Turai za tai baza ta iya ba, amma ta yadda zata rik'a bashi abincin da maganin harya warke".