Sashe 14
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
B'angaran friend's d'in Habib, Habib na koma wa Office d'in su kai mai sallah su kace tafiya za su yi. Habib godiya ya yi masu sosai, sannan yasa aka cika masu bayan But d'in su da yoghurt.
B'angaran Hassana ko, Yau ta tashi da niyyar ko ak'asa ne sai ta je aiki dan zaman ya isheta, ga tsoran supervisor d'in su da ta ke yi, dan ana yawan fad'a mata rashin mutuncinta. Hassana da wuri ta shirya kamar yadda ta saba shiryawa ta kama hanya ak'asa ta tafi. Hassana ba ita ta isa sanat yoghurt ba, sai 9:30Am. Ita da ke zuwa tun seven o'clock. Tom dama Billy ta bada sak'o ta ce idan Hassana tazo aiki ace mata tana nai manta a office d'in ta. Hakan ce ta kasan ce, Hassana na zuwa wata daga cikin staff d'in ta sanar da ita sak'on supervisor d'in. Hassana cikin fargaba ta tura Office d'in supervisor ta shiga. Lokacin Billy na zaune tana aikin danna waya. Hassana cikin girmama ta ce, "Barka da aiki supervisor". Da kai Billy ta amsa ma Hassana. Hassana kuma ci gaba da tsayuwa ta yi, tana jiran hukuncinta. Ita ko Billy tama manta da wata Hassana, hakan yasa ta kalleta ta ce, "Lafiya za ki zo ki tsamin akai? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Supervisor dama wata staff ce ta ce kince idan nazo aiki nazo kina kirana". Hassana ta ci gaba da cewa, "Supervisor Wallahi rashin kud'in napep ne ya hanani zuwa aiki, kwana uku da banzo ba, ko yauma ak'asa nazo". Billy bar abinda ta ke yi awaya ta yi, ta d'aga kai tana kallan Hassana, ta ce, "Ki ce mai sharar site d'in da ake yoghurt ko? ". "Eh ni ce". Cewar Hassana. "Billy kallan Hassana ta yi da b'acin rai dan sai abinda Habib ya yi mata yadowo mata farko, hakan yasa cikin d'aga murya ta ce, "Hassana ki ke ko me!?, mun da katar da ke aiki a k'ark'ashin sanat yoghurt Company ". Hassana cikin tsoro da fargaba jin abinda Billy ta ce mata, ta ce, "Supervisor dan Allah ki yi hak'uri insha Allah daga yau haka bazai kuma faruwa ba". Billy ko inda Hassana ta ke bata kalla ba ta ce, "Nariga na gama magana, ki kalli time kigani ko yanzu k'arfe nawa kikazo aiki?, bama aiki da wanda bashi da experience, fitar min daga Office! ". Hassana fita ta yi batare da ta k'ara cewa ko mai ba, Hassana na fita ta nufi Office d'in Manager ".manager na zaune Hassana tai mai nocrking. Izinin shiga manager ya ba Hassana. Hassana shiga ta yi,Hassana cikin girmamawa ta gaida manager. Manager cikin sakin fuska ya amsa ma Hassana, ya ce, "Hassana lafiya dai ko? ". Hassana kamar zata yi kuka ta ce, "Manager supervisor ta dakatar da ni aiki". Manager cikin tsoro ya d'aga kai yana kallan Hassana. Shiru manager ya yi na d'an wani lokaci sannan ya kalli Hassana ya ce, "me kika yi mata? ". Hassana cikin sanyin muryarta, ta ce, "Banzo aiki ba kwana uku, bani da kud'in napep, ko yauwa ak'asa nazo". Shiru manager ya yi, sannan ya ciro kud'i yaba Hassana ya ce, "Hassana amshi kud'innan kinji sai ki amfani da su, ki yi hak'uri kinji naso kiyi aiki anan, tom amma inda haka ya faru sai dai hak'uri ". Hassana amsa ta yi taima manager godiya jin abinda ya ce, ta fita daga Office d'in. Hassana na ta fito daga Office d'in manager ta had'u da staff d'in da ta bata sak'on supervisor na kiranta. Staff d'in cikin tausayama Hassana ta k'araso inda Hassana ta ke, ta ce, ta koreki ko? ". Kai Hassana ta d'aga mata ta ce, " Ta kore ni, na yi ma manager ma magana ma ko zai sa baki, amma ya ce min inyi hak'uri ". staff d'in kallan Hassana ta yi ranta ad'an bace, ta ce, "Ni da nasan zaki gurinsama da na hanaki, ai indai supervisor ta yanke hukunci bai iya yin komai, sai dai ya baka hak'uri bai iya sab'a maganarta". Hassana sallama ta yi ma staff d'in ta tafi dan maganar ma da kyar ta ke yinta. Cikin kud'in da manager ya ba Hassana ta hau napep ta koma gidansu Oga Habib, duk da zuciyarta cike ta je da bargabar komawa gidan, in da yanzu tabar aiki ak'ark'ashin su, haka nan Hassana ta koma inda bata da yadda zata yi.Jimmai cikin mamaki ta ke kallan Hassana ganin Hassana ta dawo gida yanzu.Jimmai k'arasawa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, "Hassana lafiya kuwa naganki kin dawo? ". "Supervisor ta koran aiki". Jimmai ta fe k'irji ta yi tana salati, ta ce, "manager kuma ya sani? ". "Eh ya sani, wai budurwarsa ce ba ya musu da abinda ta ce, inji wata staff". Jimmai shiru ta yi, tana jimamin abinda ya faru. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai tom kina ganin babu damuwa inci gaba da jama gidannan yanzu bana aiki ak'ark'ashin su? ". Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Tom nima dai ban sani ba, amma dai yau Hajiya turai zata dawo ai, shiyasama kikaga ko ina gidan aiki ake, tom ki bari ta dawo mugani".
WACECE HAJIYA TURAI?.
Hajiya turai babbar macece cikakkar 'yar boko. Ita kad'ai ce awajan mijinta wato Alhaji Idris mai kanti. Tun Habib na yaro Mahaifinsa ya rasu, hakan yasa Habib bai san Mahaifinsa ba. Hajiya turai babbar 'yar jarida ce, yanzu haka Hajiya turai a B. B. C, London ta ke aiki, hakan yasa kusan koda yaushe Hajiya turai bata Nigeria.Ji da kai da miskilanci Habib duk a gurin Mahaifiyar shi ya gada. Hajiya turai tun da ta haifi Hassana k'anwar Habib ta tsaida haihuwa, dan ita gani ta ke baza ta iya d'awai niyar yara uku ba. Hassana ta yi girma kusan 18 years sannan Allah ya yi mata rasuwa, sanadiyar wata bak'uwar 'yar aiki da Hajiya turai ta d'auka aiki, ashe had'in kai ne akai da ita aka zuba ma Hassana guba ta ci, wannan ne sanadiyar mutuwar Hassana har lahira. Mutuwar Hassana sosai ta d'agama Habib hankali dan idan ka cire Hajiya turai mahaifiyar Habib, tom babu wanda Habib ya ke zama dashi sunyi hira su ci abinci tare sai Hassana, yana kiranta da sanat, wannan shine dalilin da koda zai bud'e Company yin yoghurt ya sa ma mai suna Sanat yughurt. Tun rasuwar Hassana ya sa Hajiya turai ta bar yadda da kowa yana shigo mata gida barkatai. Wannan shine dalilin da yasa Hajiya turai har 'yan Aiki ta daina d'auka tuma ta ke rik'e wa inda ta ke dasu da mahimmanci bata yadda Habib ya koresu ko sun yi wani abun, duk da ta yi kashedi sosai akan d'aukar wata sabuwar mai aki bata nan, wannan shine dalilin da yasa koda aka kai mata labarin zuwan Hassana taima Habib fad'a. Wannan ke nan".