Sashe 49
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hassana ko tsabar ta kai ci, cikin kuka ta fara magana kamar haka, "Oga Habib kamar yadda nace ma ni ban mata komai ba haka ne , hasalima ita ce tai min, dan haka ni bazan iya bata hak'uri ba". Habib da mamaki ya tsaya yana kallan Hassana. Sannan ya ce, "Ok, ke baza ki iya bata hak'uri ba!, ko?".
Hassana banza tai da Habib ta ci gaba da kukanta, sai dai ta yi alk'awarin duk abinda Habib zai mata sai dai ya yi mata, amma baza ta tab'a ba Billy hak'uri ba, inda ba tai mata komai ba".
Billy ko cikin jin dad'in ganin Hassana na kuka, da kuma yadda Habib ya kafe mata sai ta bata hak'uri, cikin yaudararrar murya, ta ce, " Oga Habib dan Allah ka rabu da ita, ai dama ta ce, duk factory nan babu wanda ya isa yasata abinda ba tai niyya ba, ni na yafe mata". Habib ko da zigar Billy ta shige, bai san sanda ya jawo Hassana da hannu d'aya ba, ya wurgarda ita kefe guda yana huci, ya ce, " Zaki bata hak'uri ko bazaki bata ba, saina yagalgalaki anan gurin!? ". Hassana ko da taji zafin wurgin da ya yi da ita, dan sosai kanta ya bugu, kwanciya tai ak'asan malemale tana kuka iya k'arfinta, tana cewa, "Wayyo Allah Mommy kaina, Wayyo Mommy dan Allah ki dawo na gaji, Wayyo Mommy zasu taru su kasheni".
Daga Habib har Billy kallan Hassana kawai suke, Habib kallan Billy ya yi ranshi a d'an b'ace ya ce, "zaki iya tafiya ". Billy kamar karta futa taji, dan bata ji dad'in fita ita kad'ai ba ba Hassana, amma ko ba ko mai taji dad'in yadda Habib ya yi ma Hassana, dan ko a haka ai ya fifitata akan Hassana".
Bayan Billy ta fita Habib zama ya yi yaci gaba da abinda ya ke yi, Hassana ta yi k'asa sosai da kukan sai shashshek'a da ta ke yi".
Bilya ne yashiga Office d'in Habib kawo mai lunch. Bilya da mamaki ya bi Hassana da kallo da ke kwance ak'asa . Sai dai yanzu tabar kukan sai shashshek'ar kuka , itama kad'an-kad'an ta ke yi. Bilya kallan Habib ya yi, ya ce, "Oga Habib wannan fa lafiya? ". Bilya ya fad'i maganar ad'an rud'e.
Habib ko kallan Bilya bai yi ba, balle Bilya ya sa ran zai bashi amsa".
Bilya ganin haka, Kiran sunan Hassana ya yi ahankali, ya ce, "Amaryar Ogan m.... ". Da sauri Bilya ya ja bakin shi ya rufe, saka makon kallan da Habib ya yi mai, dama kuma sub'utar baki da yaso ya yi. Bilya cikin sosa kai, ya ce, "Madam". Dan ba zai iya Kiran sunan Hassana kai tsaye ba".
Hasssana kuma da wani sanyayyan bacci ya fara d'aukarta, d'ago kai ta yi tana kallan Bilya, Bilya ya ce, "Ki tashi mana akwai sanyi ak'asa kar ya yi miki illah". Hassana cikin k'asa da murya sosai kamar za tai kuka, ta ce, " Oga Bilya bazan iya tashi ba, kaina". Bilya shiru ya yi in da ba damar ya rik'e ta ta tashi , Bilya ganin haka maida kallan shiga Habib ya yi, ya ce".
"Oga Habib ga abincinka nan ". Habib sosai yaji haushin Bilya, wato sai da ya gama abinda ya yi niyya sannan zai bashi abincin, hakan yasa Habib ya yi banza da Bilya. Bilya ya ya gaji da tsayuwa k'arshe ya aje abincin ya fita , dan ya lura ya b'atama Oganna shi rai".
Habib lokacin da sallar azahar ya yi, ya tashi zai ta fi sallah, kwata-kwata ya manta da Hassana da ke kwance a k'asa, ya tashi da sauri dan ya makara, ya take ta da takalmin shi".
Wata uwar k'ara Hassana ta yi, wadda sai da taba Habib tsoro, dan sosai ya ta ke ta. Habib juyowa ya yi da sauri yana kallan Hassana, dan ya manta da ita agun. Habib tsaki ya yi zaja k'ofar ya fita".
kasan cewar Hassana ba sallah za tai ba, cikaba da kwanciyarta ta yi tana yarfe hannun dan yadda ta ke ji ta yi tarkad'e a hannun. Haka Hassana dai ta ci gaba da kwanciya tana jinyar hannunta, zuwa yanzu kan ya d'an lafa mata, amma hannunfa sosai ya ke mata zugi".
Habib sosai ya yi mamaki da ya dawo ya iske Hassana kwance gun, dan ya yi tunanin zata tashi kafin ya dawo. Tsallaketa Habib ya yi, ya je ya zauna".
Abin mamaki Hassana har dare tana kwance a Office d'in Habib. Bilya ko da ya zo dan ganin Habib ko ya shirya su tafi, cikin mamaki ya ke kallan Hassana, Bilya kamar ya juya ya tafi, ganin Habib d'in ya shirya, tsayawa ya yi, ya kira sunan Hassana ya ce, "Madam lokaci fa ya yi, ki tashi".
Hassana tashi ta yi ta ta fita daga office d'in, daga Bilya har Habib da kallo suka bita".
Bayan Bilya ya kai Habib gida kamar yadda ya saba ya dawo ya d'auki Hassana ma".
Amota ne Bilya ke tambayar Hassana me ya had'ata da Oga Habib. Hassana cikin jin zafin abinda Habib ya yi mata, ta ce, "Oga Bilya, da muka Shiga Office d'in Oga Habib, nida Supervisor, kamata ya yi ya tambayi kowannan mu abinda ya faru, amma sai ita kad'ai ya tambaya, ta fad'i mai kaf abinda ba ai ba, shi kuma ya hau ya zauna, wai sai na bata hak'uri, ni kuma nak'i bata, shine ya wurgar da ni a inda ka ganni, da zai tai sallah kuma ya take min hannu, kaga hannun". Hassana ta nuna ma Bilya hannunta da ya kunbura".
Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "Wai ni ko meye had'inki da Supervisor ne? ". "Wallahi Oga Bilya haka nan ta tsanan ban mata komai ba". Cewar Hassana".
Dariya Bilya ya yi ya ce, 'aiko kin mata komai, ba ke bace kika aurar mata miji, kin san ita a haukarta so take Oga Habib ya aureta ". Hassana da mamaki ta kalli Bilya ta ce, "Tom amma taya ta san hakan? ". "Wai auranki da Habib?, tom ai Manager shi Hajiya ta sa akan komai a d'aurin Auran, inajin shi zai fad'a mata".
Haka dai su Hassana suka isa suna fira da Bilya".
Hassana zaune ta iske Farida a falo kamar yadda ta saba, ta ci kwalliya tana jiran dawowar Hassana tai ma Habib kunu, ita kuma ta kai mai, dan yau Habib na da wowa ya shiga falon ya ce ma Farida ta yi mai kunun yanzu. Hakan yasa Farida ta k'osa sosai Hassana ta shigo".
Hassanan kuma na shigowa ta nufi bedroom d'in ta. Farida kallanta ta yi, ta ce, "Ke kin manta da kunun Oga Habib ne? ". "Yau bazan samu yi ba, banda lafiya". Cewar Hassana na nai man shigewa ciki".
Farida saurin rik'o hannun Hassana ta yi, ta ce, "Aiko biki isa ba, ubanki zai ci idan baki da mamai kunun ba! ".
Hassana ranta ad'an b'ace ta ce, "Aunty Farida dan Allah idan muna abu dake kibar zagin ubana, saboda ya mutu baya raye, bana jin dad'in zagin Ubana d'in da kike yi". Farida kallan Hassana ta yi ta ce, "Tom k'arya na yi?, Idan baki dama mai ba Ubanki zai sha? ". Hassana cikin jin haushin zagin ubanta d'in da Farida ta kuma yi, ta ce, "Shikenan Aunty Farida, ni kuma bazan dama kunun ba, sai ya sha abinda zai sha".
Hassana ta juya zata shiga ciki. Farida ta fincikota ta ce, "Wallahi sai kin dama shi, biki isa ba dan Uwarki! ".
Hassana ko fincikewa ta yi daga rik'on da Farida ta yi mata, ta ce, "Aunty Farida dan Allah ki sakan, inajin kunyarki". Hassana ta fad'i maganar cikin sanyin murya".
Farida wujijjiga Hassana ta yi, ta ce, "Wuce muje kitchen ki damame kunun, dan Ubanki so kike ki tona min asiri yasan bani ke dama kunun ba, tom Wallahi biki isa ba! ".
Hassana tun k'arfinta ta kwace daga rik'on da Farida tai mata, sannan ta ce, "Haba Aunty Farida tunda nace miki bazan iya ba ai ya kamata ki yi hak'uri, inda kullum ni ke damame, tom yau banda lafiya bazan iya ba". "K'arya kike munafuka, kina jin haushin baya kula kine, ni yake kulawa shiyasa, kunu kuma Wallahi sai kin dama shi". Cewar Farida".
Wani k'ayataccan murmushi ne ya sub'ukucema Hassana, ta ce, "Haba Aunty Farida dan me zanji haushi dan Oga Habib ya sakin mai kunu, abinda kowa da matsa yinsa a gunsa". Farida d'aure fuska ta yi, ta ce, "ke muje ki dama kunu". "Wallahi bazan dama ba". Cewar Hassana".
Farida ko jawo Hassana ta yi. Hassana ta turota da k'arfinta, Farida ta bige da caution. Aiko tana tashi ta kama Hassana da bugu".
Farida na bugun Hassana, Hassana na ramawa, nan fa dambe sosai ya b'arke tsakanin Hassana da Farida".
B'angaran Habib ko, jin Farida shiru, tashi ya yi ya zo ya amsa da kanshi, dan yunwa yake ji sosai, inda raban shi da abinci tun break fast d'in da ya yi, Bilya ya b'ata mai rai d'azu , bai ci abincin da ya kawo mai ba".
Habib tun kan ya shigo falon ya ke jin hayaniya sosai. Hassana ko Allah ne ya bata sa'a ta samu ta had'a kan Farida da bango, Farida sosai taji azaba haka yasa ta shiga kitchen ta d'akko wuk'a ta bi Hassana da ita. Hassana sosai ta rud'e tana za gaye falon tana ihun nai man d'auki, dan tabbas a yadda taga Farida babu abinda zai hana ta kasheta".
Hassana na cikin za gayan nai man d'auki, taji shigowar mutum, da gudu ta ruga ta cimimiye Habib tana "Wayyo Allah Oga Habib tai makanni zata kasheni".
Farida ko duk da Hassana ta rik'e Habib bata fasa abinda tai niyya ba, dan ita gani take wannan ma ai dama ce Allah ya bata, dan tasan kota kashe Hassana ta kashe banza, wama yasan Iyayanta, idan ansansu ma basu da abinda zasu yi k'ararsu".
Hassana ganin Farida ta kuma yo kanta, bayan Habib ta b'oye, tana ihu. Habib shi kanshi ganin Farida da gaske ta ke, tsawa ya da kamata, cewa, "Ke baki da hankaline, kasheta zaki yi! ".