← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 78

Sashe 52

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Shafi na 62&63.

Hajiya Turai tana nan tsaye Habib ya tada motar yaja suka tafi.
Sannan Hajiya Turai ta koma cikin gida tana hawayan farinciki.
Kasan cewar bawani shahararran nisa bane tsakanin gidan Hajiya Turai da gidan Habib, hakan yasa cikin mintina kad'an suka isa. Gida ne babba masha Allah, kallo d'aya za kaima gidan kasan ankashe kud'i sosai wajan yinsa. Habib na yin parking bai bi takan Hassana ba ya fita daga motar ya barta nan, tana aikin kuka. Hassana ko jin Habib ya fita, itama fita ta yi tabi bayan shi".

Falon mai ma dai-dai cin girma, wanda ya k'oshi da kayan more rayuwa. Inda akaima falon adon Orange & White, color d'in sai ta kuma fito da madarar kyau na Falon".

Habib na shiga falon ya yi side d'in shi, inda ita kuma Hassana ta baje ko linta a falon, ta zauna kan two seater".

Haka Hassana ta gama kukanta daga k'arshe ta lallashi kanta ta yi hak'uri ta yi shiru. Hassana na nan zaune ta na tunane-tunane a haka bacci ya kwasheta, batare da ta cire kayan jikinta ba, ko ta naimi inda bedroom d'in ta take ba".

Habib ko da ya shiga bedroom d'in shi, toilet ya shiga ya watsa ruwa ko zai ji sanyi a zuciyar shi, shima dai kusan haka ta faru da shi yana fitowa ko mai bai shafaba ya zauna kan lover chair yana tunanin yadda zai yi ma Hajiyarsa idan ta huce Hassana ta koma can da zama ala bashi shi sai ya barmata gidan Hajiyar shi yadawo nan ya ci gaba da zaman shi, Habib na wannan tunanin bacci ya kwasheshi shima anan".

Cikin dare yunwa ta tada Habib, dan tun break fast d'in safe raban shi da yasama cikinshi wani abu,dan tunda Hajiya Turai tai ma Habib maganar ta rewar Hassana ya hana kanshi sukuni. Habib tashi ya yi ya je kitchen ko ruwan zafi ya samu yasa tea, dan sosai ya ke jin yunwa".

Habib mamaki ya yi da yazo yaga Hassana kwance sai baccinta ta ke. Tsaki ya yi ya tab'e baki ya ce, "Wannan yarinyar bata da hankali kwata-kwata. Habib kitchen d'in yaje, ya samu ya dafa ruwan zafi yazo yasha tea".

Hassana tunda ta kwanta ba ita ta farka ba sai 6:00AM, tana tashi, side d'in da ta ke da tabba cin nata ne ta shiga, anan taga kayanta na sawa, Hassana sallah ta farayi, sannan ta cire doguwar rigar jikinta ta samu wata wadda bata kai waccan nauyi ba tasa, ta shiga kitchen ta d'ora ruwan tea, sannan ta soya wainar kwai. Hassana na gamawa ta d'auki na Habib ta kai mai kan derning, ita kuma nata ta shiga bedroom d'in ta dashi. Hassana sai da ta yi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar, inda kayan duk sune, sannan ta zauna ta fara break fast ".

Habib ko bayan ya tashi ya yi sallar asuba, komawa ya yi ya kwanta. Sai 7:52AM, Ya farka da sauri ya shiga wanka, yana fitowa ya yi shirinsa na fita. Habib da bai san Hassana ta yi wani abun break fast da shiba, yana gama shirinsa ya fita abinsa".

Zaune Habib ya iske Bilya acikin mota yana jiran shi, hakan yasa Habib na zuwa, Bilya yaja motar zasu tafi".

Bilya har ya tada Motar Habib ya tsayar da shi ya ce, "tsaya ina zuwa". Bilya da katawa ya yi , Habib ya shiga ciki. Dai-dai nan ma Hassana ta fito itama tana sauri zata tafi dan tasan ta makara sosai".

Hassana tsayawa ta yi ganin Habib, kuma kamar gunta yazo, Hasssana baki ta bud'e ta gaida Habib, Habib ya katseta da cewa, "Karki sake kizo aiki yau, sai Hajiya ta koma". Habib na fad'in haka ya juya ya tafi, dan yasan indai Hajiya Turai tasan Hassana na zuwa Sanat yughurt aiki, yasan zata hana, shi kuma baya son hakan ".

Hassana ko cikin jin dad'i ta koma ciki, dama ba son zuwan take ba, dan tun abinda Billy tai mata taji ta tsani Sanat Company gaba d'aya.
Hassana komawa ta yi tana mai jin dad'in hakan".

Wajan misalin 12:15PM, Hajiya Turai da Hajiya Murja mahaifiyar Farida suka zo gidan, lokacin Hassana na zaune a falon tana game awayarta da Hajiya Turai ta bata".

Hassana cikin nuna jin dad'in ganin Hajiya Turai ta tarbe su, inda Hajiya Murja sai tab'a baki take, dan acewarta gidan da Farida ya dace ba da Hassana ba".

Hassana ruwa ta kawoma su Hajiya cikin fresh, sannan ta gaida su cikin girmamawa, sun d'an jima da zuwa Kafin suka tafi. Dan ita Hajiya Turai bata so zuwan ba ma, Hajiya Murja ce ta matsa mata, ita kuma gulma ta kawota, dan ganin yadda gidan yake".

B'angaran Farida ko kamar yadda su kai da Hajiya Zaliha haka akayi, da wuri ta shirya, ta nufi Sanat yughurt nai man aikin".

Koda Farida ta isa direct Office d'in Habib ta naimi izinin shiga. Lokacin Habib nata aiki a laptop, Bilya ya shiga Office d'in, ya ce, "Oga Habib Farida ce ke son ganinka, zata iya shigowa? ". Habib shiru ya yi yana tunanin lafiya Farida ke son ganin shi,kai ya d'aga ma Bilya, alamun zata iya shigowa ".

Farida shiga ta yi. Bayan ta zauna ne, ta gaida Habib kamar yadda ta saba, sai kuma taja bakinta ta yi shiru. Habib da katawa ya yi da abinda ya ke yi ya yi, ya kalli Farida ya ce, "Lafiya dai ko? ".

Farida sosa kai ta yi, sannan ta ce, "Uhm, Oga Habib dama nagaji da zamane haka nan, shine na yanke shawarar inzo nan ko zan samu aiki". Habib kallan Farida ya yi, ya ce, "Gurin manager zaki, bani ke d'aukar aiki ba". Shiru Farida ta yi, sannan ta ce, "Oga Habib ba lallene manager ya d'aukan ba, saboda wata friend d'ina ta tab'a zuwa nai man aiki anan manager yace mata sun b'ar d'aukar aiki suna da wadatattun ma'aikata". "Kije ki ce mai nina turoki, zai d'aukeki". Cewar Habib yana mai ci gaba da abinda ya ke yi".

Farida badan ta soba ta tashi ta fita daga office d'in Habib. Office d'in manager Farida ta shiga. Cikin girmamawa da mutunta juna Farida suka gaisa da manager, inda manager yasan Farida sosai a gidansu Habib. Bayan sun gama gaisawa ne, manager ya tambayi Farida lafiya".

Farida cikin hikima ta fara magana kamar haka, "Wallahi manager nagaji da zaman gida ne, shine nace bari inzo nan in rik'a ta ya ku aiki".Dariya manager ya yi, ya ce, "Tom ai shikenan, wani b'angare kike so? ". Farida shiru ta yi dan in son samu ne, b'angaran da Hassana ta ke ta ke so, tom amma kuma bata san b'angaran da Hassana ta ke ba, hakan yasa Farida ta ce, "Manager ni ko ina da ruwana". "Ok, tom shikenan, hakanma ya yi ai". Cewar Manager. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Manager zan iya fara aiki yau? ". "Sosai ma kuwa, zaki iya farawa".

Farida cikin jin dad'i ta fita Office d'in manager, haka Farida tai ta aikin duba ko ina ko zata ga Hassana amma bata ganta ba, ahaka dai har lokacin tashi ya yi, Farida bata ga Hassana ba, hakan ya tabbatar mata da Hassana bata zo Aiki yau ba".

Washe gari ma haka Farida tazo aiki ,Haka Farida ta wuni bata ga Hassana ba, gaban Farida fad'uwa ya farayi, tana jin tsoran ko dai Hassana ta bar aikine. Yauma dai haka Farida ta tashi batare da taga Hassana ba, gashi bataga wata hanyar da zata samu shiga Office d'in Habib ba, dan sai ya san da zuwanka kake shiga".

Hassana ko jita ke kamar kar Hajiya Turai ta tafi dan bata son k'ara zuwa Sanat yughurt, gashi bata iya kai k'arar Habib wajan Hajiya Turai, akan zuwanta aikin".

Yau kwanan Hassana shida kenan agidan Habib, kuma har yanzu babu wata magana da tak'ara shiga tsakanin Habib da Hassana, Hassana ganin Habib ko tayi abin breakfast da shi ba sha yake ba, yasa ta daina yin komai da shi, iya cikinta ta ke yin komai. Kafin ta fito da safe Habib ya tafi, da daddare kuma Kafin ya dawo ta koma bedroom d'inta, Habib ko ganin batare da Mahaifiyarsa ya ke ba, yanzu sai kusan 10:00PM ya ke dawowa gida, hakan yasa basa had'uwa da Hassana ".

Farida ko yau kwananta biyar kenan da fara zuwa aiki, amma har yanzu bata ga Hassana ba, hakan ya tabbatar mata Hassana ta bar aiki. Hakan yasa Farida yau da kuka ta isa gidan Mahaifiyarta. Bayadda Hajiya Murja ba ta yi da Farid ba ta yi shiru, amma Farida tak'i. Daga k'arshe ma tashi ta yi, ta had'o kayanta ta ce, ita tafiya za tai ta gaji, Hassanar ma tak'i zuwa Sanat yughurt d'in, wama yasani ko Oga Habib ya hak'ura yana sonta yanzu, in da mai yasa tabar zuwa aiki". Hajiya Murja waya ta d'akko tai waya, ita dai Farida duk tana kallanta, Hajiya Murja ta ce, "Hello Habu dan Allah kuzo yanzu aiki za ku yi min adaran yau d'in nan".
Farida kallan mahaifiyarta ta yi, ta ce, "Aikin me za su yi miki?, nifa bana son kina tarayya da su habu". Murmushi Hajiya Murja ta yi, ta ce, "karki damu Farida wannan shine aikin k'arshe da zanyi da su".

Hajiya Murja na nan zaune ita da Farida su Habu suka shigo gidan su Uku. Babban cikinsu d'in kallan Hajiya Murja ya yi, ya ce, "Hajiya wana aiki za muyi miki? ". "Wata yarinya nake son ku d'auke ku yi nisa da ita sosai sannan ku yi mata gargad'i in ta koma tom kasheta za kuyi". Cewar Hajiya Murja ".

Dariya Habu ya yi, sannan ya ce, "Bamu address d'in gidan". Hajiya Murja wata takarda ta mik'ama Habu, mai d'auke da address d'in gidan da kuma photon Hassana".

Hajiya Murja kallan Habu ta yi, ta ce, "Na san kun iya aiki, bana son kuskure zan baku dubu d'ari biyu, ya yi muku? ". "Ba komai Hajiya ai ana tare". Cewar habu".
Chapter 52 · 0% Book details