← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 78

Sashe 73

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habib gaf da magriba ya tashi aiki ya koma gida. Side d'in shi ya shiga sai da ya watsa ruwa ya yi sallah sannan ya nufi b'angaran Hajiya Turai. Habib Hajiya Turai kad'ai ya iske a Falon, zama Habib ya yi gefan Hajiyarsa ya gaida ta. Shiru-shiru Habib bai ga Hassana ba, Habib Hajiya Turai ya kallah ya ce, "Mommy ina yarinyar nan? ". Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Wata yarinyar? ". Kai Habib ya sosa ya ce, "Mommy Sanat fa nake nufi". "Ok, tana ciki... ". Hajiya Turai bata rufe baki ba Hassana ta fito, Hassana gefan Hajiya Turai ta zau na. Hassana na zama Hajiya Murja na yin sallah ma ta shigo, Hajiya Murja na zuwa ta je ta rik'e k'afafun Hajiya Turai tana kuka, ta ce, "Hajiya dan Allah ki bar Habib ya rufa min asiri ya ceto rayuwar yarinyar nan ya aure ta, Wallahi yan zu haka Hajiya Turai na barota sai aman jini take,Habib dan Allah ku tai maka". Habib da tausan Hajiya Murja ya kama shi, gyaran murya ya yi, ya ce, "Mommy ki yi hak'uri ni nai miki alk'awari kuma zan cika miki insha Allah". Habib mai da kallan shi ga Hajiya Turai ya yi ya ce, "Mommy ku yi hak'uri dan Allah ke da Sanat zan auri Farida ne ba dan soyayya ba, zan aure ta ne dan ceto rayuwarta, dan Allah Mommy ku yi hak'uri ". Hajiya Murja kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib in dai ka yarda zaka ceto rayuwar Farida tom kazo mu je yan zu ga waliyin Farida nan cikin mota, kai kuma sai ka samu naka, yan zu ad'aura auran idan an idar da Sallar issha'i ". Habib kallan Hajiyarsa ya yi da fata furta koma ba, ya mai da kallan shi ga Hassana da ita ma shi ta ke kallo, Habib jin du kan su babu wanda ya yi magana, kallan Hajiya Murja ya yi, ya ce, "ki je gida kawai zan nai mi wanda kika ce kuna tare yan zu mu yi magana". Hajiya Murja godiya ta yi ma Habib sannan ta tashi ta tafi, Hajiya Murja ta tafi bai fi da minti goma ba Habib ma ya tashi jin kiran Sallah zai tafi. Hassana ko da ta san Habib daga wajan Sallar za'a d'aura auran shi da Farida, Hassana ta shi ta yi da sauri ta rik'o hannun Habib, Hassana cikin kuka ta ce, "Wallahi Oga Habib Allah baza ka fita ba sai ka sakan ai tun jiya haka mu kai da kai, ka sakan sai kaje ka aure ta in da tausan ta ka ke ji! "Habib tsayawa ka wai ya yi yana kallan Hassana yama rasa me zai ce mata, Hassana kuma ta kama Habib kata kam ta rik'e ta k'i saki. Hajiya Turai ko da ita kanta bata san mai zata cema ba,tashi tai ta ba su gu".

Habib kallan Hassana ya yi cikin sanyin murya ya ce, "Haba Sanat wai ke biki san abin da kike fad'a babu kyau ba, dan Allah me yasa kike yin haka ne, ki zauna in je Sallah in dawo sai mu yi magana". "Ai ina ji kace idan kaje sallah za'a d'aura auran acan, ni dai kawai ka ban sannan ka tafi, amma ni bazan tab'a zama da Farida ba!". Duk maganar da Hassana ta ke yi cikin kuka ta ke yin ta".

Habib hannun Hassana ya kama suka zauna, hannu Habib ya sa ya goge ma Hassana hawayan ta, ya ce, "Sanat ki yi shiru tom muyi magana". Hassana shiru ta yi tana kallan Habib alamun ina jinka. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Yan zu me ye damuwar ki da auran Faridar? ". "Ni ban iya zama da ita ba ne". Hassana ta ba Habib amsa. Magana Habib zai k'ara yi ringing d'in wayar shi ya hana. Habib d'aga wa ya yi, daga can b'angaran Hajiya Murja ta ce, "Habib dan Allah naji shiru ga waliyin Farida ya kirani wai yaji ka shiru"."Ok, gani nan zuwa". Habib ya ba Hajiya Murja amsa".

Habib tashi ya yi zai tafi, Hassana ta rik'e Habib tai tana kuka, tana cewa, "Dan Allah Oga Habib karka je, dan Allah, Allah in ka aure ta ba zan ji dad'i ba, dan Allah ". Haka Hassana ta rik'e Habib tana kuka tana rok'an shi. Dan tai mai ma kurarin sakin amma bai ji ba".

Habib jikin shi sosai ya yi sanyi da yadda yaga Hassana tana kuka, ga Hajiya Murja na jiran shi. Habib rasa yadda zai yi ya yi, komawa ya yi ya zauna dan Hassana ta k'udin-dine shi ta hana shi fita, ga kukanta na da mun shi sosai, dan ya lura in dai tai kuka bata da wuyar ciwan kai".

Habib rungume Hassana ya yi yana lallashin ta, ya ce, "Shikenan na fasa, tom ki share hawayan ki". "Ai jiya ma haka kace min"
Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Kina son in fasa auran Farida? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib".

Habib kallan Hassana ya yi, yana na zari, dama yana son Hassana ta koma gidan shi da zama tom yasan Mommy ba zata bari ba, ba kamar yan zu ba da yasan ya k'ara b'ata ma ta rai ba, hakan yasa Habib cema Hassana, "Sanat na fasa auran Farida, amma in dai kin yarda sai dai yau ki koma gidanki ki bar gidan Mommy, kuma karki bari Mommy ta sani, tom in dai kin yarda da haka ni kuma na fasa auran ta". Hassana ba tare da tunanin ko mai ba, ta ce, "Eh na yarda". Habib cikin jin dad'in abin da Hassana ta ce, ya tashi ya ce, "Tom tashi mu tafi kafin Mommy ta fito ".

Hassana ta shi ta yi tana kama hannun Habib suka bar falon Hajiya Turai, suna zuwa Habib ya hangi wanda Hajiya Murja ta ce yana jiranta acikin mota. Shi ko mai jiran Habib ya na ganin Habib ya yo inda ya ke da sauri, hannu ya ba Habib suka gaisa, sannan ya ce, "Tun d'azu nake jiranka, gashi har nai ma limamin magana, yan zu haka kai suke jira". Habib kallan shi ya yi, ya ce, "sai zuwa gobe ma yi magana". Habib na fad'in haka ya shiga motar shi ya ja suka tafi suka bar Waliyin Farida tsaye".

Habib na isa gida direct falon shi ya yi da Hassana suna zuwa Habib ya shiga wanka, ya yi alwallah. Habib bayan ya fito sanye da farar jallahbiya aji kin shi, kwance Habib ya iske Hassana, Habib hannun ya mik'a ma Hassana ya ce"Sanat zo in cud'aki". Hassana dariya ta yi, ta ce, "Bana so kai ma kai kai ma kanka, ni ma ni zanma kai na". "Ok, kina sha'awar yi min ne? ". Habib ya tambayi Hassana ".

Hassana ta shi ta yi tana ba Habib amsa ta ce, "Uhm lokacin da baka da lafiya dai nai m.... ". Habib bud'e baki ya yi yana kallan Hassana ya ce, "Kin me? ". Hassana da sauri ta nufi hanayar Toilet, Habib ya ja wo ta ya yi yana kallan ta, ya ce, "Serious kin tab'a min wanka? ". Hassana kai ta juya ta ce, "Ni dai ka sakan in je in yi wanka na". "Nak'i d'in sai kin ban amsa, kin tab'a? ". Habib ya tambayi Hassana".

Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Ni fa bani kema ba, kai ne ke shiga da kanka idan ina wanka, duk yadda nayi ka yi da kanka kake ma kanka". Habib kallan Hassana ya yi ganin ta fad'i maganar tana b'oye dariya , ya ce, "Da kaya jikina ko ko? ". "Tom ni dai na ma manta kamar akwai kamar babu". Hassana ta ba Habib amsa still tana son yin dariya ".

Habib jan hanun Hassana ya yi juwa toilet d'in ya ce, "Muje nima yau ni zan miki ". Hassana k'ara ta yi, ta ce, "Tsaya in fad'ama gaskiya, Allah da kaya jikin ki". "Uhm nima muje in miki da kaya jikinki". Habib ya ce ma Hassana ".

Hassana tsayawa ta yi tana kallan Habib ta ce, "Tom inda haka ne ma na fasa wankan". Murmushi Habib ya yi, ya ce, "Aiko yau dole ki wanka". Habib da k'arfi yaja Hasssana ya kai ta toilet d'in". Hassana cikin sakin k'ara da ya ke ita mai katsaniya ce, ta ce, "Tom Oga Habib tsaya, Allah da kaya nake ma, nima ba sai na cire ba". Habib ko sauraran Hassana bai ba, ya zage zip d'in doguwar rigar jikinta. A haka akai wankan daga ita sai bra sai pant d'in jikinta. Hassana ganin wankan ya k'i k'arewa jawo towel ta yi ta d'aura tana turo baki, ta fita tana cewa, "Duk an bi an wani kalle mutum".

Habib dai murmushi kawai ya yi ma Hassana. Hassana na zaune tana shafa lotion d'in Habib, wayar Habib ta yi, ringing, Habib ganin number Hajiya Turai sai da gaban shi ya fad'i, aiko yana d'agawa Hajiya Turai ta ce, "Habib ina Hassana!? ". Habib kallan Hassana ya yi da ke zau ne tana shafa, sannan ya ce, "Mommy ga ta nan muna tare". daga can b'angaran Hajiya Turai ta ce, "Duk abin da ka ke ka bari ina son inga Daughter yan zun nan!? ". Hajiya Turai na fad'in haka ta kashe wayarta, tana mai ganin sakarcin Hassana ".

Habib ko tashi ya yi ya tada sallah, yana idarwa ya kalli Hassana ya ce, "kin yi Sallah ne? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib".
Chapter 73 · 0% Book details