← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 78

Sashe 38

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana kallan Habib ta yi, tana tunanin yadda zata yi taba shi magungunan, dan babu yadda zatai mai ya tashi. Hassana maganin ta d'akko ta ce, "Oga Habib bud'e bakinka ka sha magani". Hassana ta fad'i maganar tana nufar bakin Habib. Hassana tusama Habib maganin ta yi, ta tada kan shi ta zuba mai ruwan faron da Hajiya Turai ta had'a mata dashi, da kyar Hassana ta samu da dabara ta rik'a sakama Habib maganin tana zuba mai ruwa ahaka-ahaka ya shanye magungunan".

Hassana na gama ba Habib maganin Hajiya Turai ta shigo da rubun Habib d'in. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi da ke gefan Habib zaune Habib kuma na kwance ya yi matashi da cinyarta. Hajiya Turai rubutun ta mik'ama Hassana ta ce, "Daughter ga rubutun ki bashi". Hassana cikin taushin murya ta ce, "Mommy Wallahi magungunan ma da kyar ya sha kibar rubutun sai gobe".

Hajiya Turai da tom da amsa ma Hassana badan ta saba, sai dan kawai ta lura da Habib d'in basha zai ba, dan ma Hassanar nada k'ok'ari. Hajiya Turai kallan Hassana ta ya, ta ce, "daughter karki bacci bari in kawo miki tea ki sha".

Hajiya Turai da kanta ta had'ama Hassana tea ta kawo mata. Sannan jamasu k'ofar ta baya tai masu good night".

Hassana sosai ta ji dad'in tea d'in da Hajiya Turai ta kawo mata. Bayan Hassana ta gama shan tea d'in ne ta cire kan Habib da ke kan cinyarta ta kwanta gefan shi".

Cikin dare zazzab'i sosai ya rufe Habib sai makyarkyatar sanyi ya ke, irin ta masu zazzab'i. Hassana cikin bacci ta ke jin yadda Habib ke kyarma yana k'ara shishige mata. Hassana farkawa ta yi, tana mai kai hannu kan jikin Habib d'in ganin yadda ya ke rawar sanyi, zafi sosai Hassana ta ji jikin Habib d'in, Hassana cikin tausayin Habib ta kuma rungume Habib ajikinta sosai, tana mai jan bargo ta rufe su, tana cewa, "Sannu Oga Habib Allah ya baka lafiya, nasan duk wannan maganin ne da kasha ya yajazama wannan zazzab'in , Allah yasakama, Sannu kaji. ".

Habib da ke kwance kusan rabin jikinsa ana Hassana amai ya ke sosai kusan ajikin Hassana. Hassana cikin rud'ewa da ganin halinda Habib ya ke ciki ta tashi zaune tana mai rik'e shi, tana aikin mai Sannu".

Hajiya Turai ko cikin bacci ta ji yo k'arar aman Habib. Cikin tashin hankali Hajiya Turai ta shigo d'akin. Hajiya Turai kan gadon ta hau, tana mai rik'e Habib d'in itama ".

Hajiya Turai da Hassana suna rik'e da Habib sai da ya amaye duk abinda ke cikin shi sannan ya koma ya kwanta yana nufarfashi".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi cikin damuwa, ta ce, "daughter meke damun shi ne? ". "Mommy daga zazzab'innan dai shine fa ya kuma kama amai". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "ki shiga toilet ki wanke jikinki bari in ciro miki wata rigar saiki sa, inda ya amaye maki taki, kamarke kikai amman, shi babu komai ajikinsu, Sannu kinji daughter Allah ya biyaki da mafificin alkairinsa". Da ameen Hassana ta amsa, sannan ta tashi da niyyar shiga toilet ta wanke jikinta Habib ya rik'e hannunta". Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Mommy ban rigar in sa hakanan Oga Habib bazai barni in tashi ba". Hajiya Turai abayar irin ta maka single d'in nan taba Hassana, sannan ta yaye abuwan gadon da Habib ya b'ata ta fita da su, sannan ta d'akko wani bargon ta mik'ama Hassana, tai mata good night ta wuce".

Hassana koda ta sake tab'a jikin Habib sanyi ta ji sosai, alamun zazzab'in ya sauka, Alhamdulillah ta ce sannan ta ja masu bargon ta rufe su".

Washe gari Hassana sai 6:50Am ta farka, da sauri ta sako gado ganin gari ya yi haske, Hassana na sakkowa mutuminta ya biyota. Alhamdulillah dan yauma tare sukai alwallah duk yadda ta yi ya yi, Hassana ko ga yadda taga Habib na kazar-kazar d'in shi tasan sauk'i ya samu".

B'angan Farida ko tunda taji ihun Hassana tana nai man agaji, ta shirya ta bar gidan, dan cewar ta zatafi farin ciki tazo ta iske Habib ya yi ma Hassana irin wujijjigar da yake ma mutane, ala bashi sai ta taho maganin da malam ya ce zata bar gidan da kanta ba sai an koreta ba, indai aka zuba shi ta taka ko ta k'etare".

Washe gari Farida da wuri ta yi sammakon dawowa, sai dai abinda idonta ya gane matane ya tada hankalinta, Hassana da Habib zaune a derning space, suna break fast, hannu Habib rik'e da na Hassana, ga Hajiya Turai gefe guda. Farida cikin rud'u ta juya zata fita, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Farida zonan!! ........... .. ✍️

Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister 🤝

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Shafi na 44&45.

Farida gefan Hajiya Turai ta je, ta tsaya ta ce, "Mommy gani? ". Hajiya Turai ta dad'e tana kallan Farida sannan ta ce, "Farida daga ina kike? ". "Daga gidan Mommyna". Shiru Hajiya Turai ta yi, tana kallan Farida sannan ta ce, "Farida kina so ki canza hali,saboda da duk inda zaki kina sanar min, amma yanzu sai dai ki fita kai tsaye, tom kar hakan ya kuma faruwa kar ki sake fita kibar gidannan bada sanina ba,ke koda ban gari karki kuma". Hajiya Turai na kai haka ta ce, "zaki iya tafiya".

Farida fita ta yi tana mai jin zafin Hajiya Turai ta na tuhumarta inda ta je gaban Hassana".

Hassana ko bayan sun gama break fast, kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Mommy bari in d'akko kayan da zan sa ina son zanyi wanka". "A'a ki kama Habib ku tafi tare, abu daga zuwa gaisuwa ai anyimin k'ok'ari nagode".

Hassana ta d'an jima zaune, sannan ta tashi ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Mommy zan tafi, ina so zanyi wanka ne? ". "Tom daughter nagode sosai,dan Allah arik'a kulawa da rubutun Habib inda muna ta k'ara ganin sauk'i ". Cewar Hajiya Turai. "Insha Allah Mommy ".

Hannun Hassana cikin na Habib a haka suka jera suka koma part d'in Habib. Hassana na zuwa ta shiga wanka ita da mutu minta, inda ta cire mai shirt d'in jikin shi da dogon wandon jeans d'in shi, ta bar shi daga shi sai d'an garami na ciki. Suka shiga tare kamar yadda suka sabo, Hassana sai da ta gama wankanta sannan ta kalli Habib da ke ta famar jagwalgwalan wankan shi. Hassana amsar sosan ta yi daga hannun Habib ta wanke mai jikin shi tass, sannan suka fita".

Hassana lotion ta d'akko zata shafa, Habib ya mik'o hannu zai ta tsa kamar yadda yaga tana yi. Hassana d'akko ke man tayi tab'oye tana ta tsa kad'an-kad'an tana shafama jikinta, saboda Habib ko ta bar mai ba shafawa ya ke ba, wasa kawai ya ke yi da shi. Hassana sai da ta gama shafa man, sanna ta shafama Habib shima, tana gama shafa mai ta ciro mai wasu kayan ta sa mai kamar yadda ta saba sa mai tanayi tana rintse ido gudin kar tai mugun gani, tana gama sa mai kayan shi ta bashi rubutun shi yasha".

BAYAN SATI D'AYA.

Yau sati d'aya kenan da zuwan Hassana part d'in Hajiya Turai ita da Habib, kuma tun daga ranar bata k'ara zuwa ba, sai dai Hajiya Turai kullum zata shigo ta ga jikin Habib. Maganar abinci ko Hajiya sosai ta jama Maimaina kunne akan karta kuskura ta ka mata da aikata mata rashin gaskiya, Hajiya Turai duk da kunnan da ta jama Maimuna hakan bai mata ba, duk lokacin Maimuna zata yi girki takan je gun ta zauna. Farida ko Hajiya Turai ta hana ta fita gaba d'aya, dan tana jin tsoran fitarta gani ta ke kamar wani abun zata iya zuwa ta yima Habib".

B'angaran Farida ko, sosai ta shiga damuwa da fitar da Hajiya Turai ta hanata yi yanzu,Hassana sosai ta dage wajan kula da Habib, dan yanzu ta gama sabawa da mak'ale mata d'in da Habib ya ke yi, na duk inda zata ya ke binta, toilet ko ta gama sabawama da binta d'in da ya ke yi. Sosai Hassana ta ke kula da ba Habib maganin shi, duk da dai har yanzu babu wani cigaba da suka k'ara gani game da Habib d'in, sai dai yanzu babu ruwan shi da kowa. Yanzu haka Hassana zaune ta ke tana ba Habib magungunan shi, Hajiya Turai ta shigo, Hassana cikin jin dad'in ganin Hajiya Turai dan ta fara sakin jikinta ta ita, ta ce, "Oyoyo ga Mommy ". Murmushi Hajiya Turai ta yi, sannan ta zauna kusa da Hassana, Hajiya Turai waya ta mik'ama Hassana ta ce, "Daughter ga wayar nan kirik'eta a hannunki zan rik'a kiranki akoda yaushe inajin jikin Habib, gurin aiki sun matsamin da kira, yau zan tafi jirgin 6:00 pm zan hau"
.Numfasawa Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "Daughter zan sama muku kayan abinci a kitchen ki rik'a girka muku, kinga yanzu bananan, duk da dai na hana Farida fita ko ina, daughter ki kula sosai dan Allah,Farida kuma duk lokacin da ta kuma zuwa ta sa meki tai miki magana ki fad'amin, kuma karki yadda ta kuma baki wani abun ta ce injini kiba Habib ki amsa".

Sosai Hajiya Turai taita ankarar da Hassana wasu abubun, duk da bata fito fili ba ta fad'a mata dalilin ciwan Habib d'in ba".

Hajiya Turai fita ta yi tasa aka shigomasu Hassana da duk wani abinda zasu buk'ata na girki, aka samu su a kitchen d'in Habib, sannan Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "daughter bari zan shirya nan da minti 30 zan tafi".

Hajiya Turai cikin k'ank'anin lokaci tagama shirinta ta, sannan ta shiga part d'in Habib, Hajiya Turai cikin sanyin muryar ta ce, "Daughter na tafi kirik'a aje wayarki kusa da ke ". Hassana cikin sanyin murya mai cike da rauni ta ce, "Tom Mommy Allah ya kiyaye hanya ya kaiki lafiya".
Chapter 38 · 0% Book details