Sashe 32
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farida cikin tashin hankali ta kalli Malam mai biyan buk'ata dole ta ce, ", Malam dan Allah ko me kake so zanma Wallahi, dan Allah kada katar da auran nan, kada ya yuwu, ka dawo da shi kaina, dan Allah ". "Karki damu yarinya koda ma ace auran ya yi wu, tom nai miki alk'awari babu inda auran zai je, yanzu ga wannan, ki yi k'ok'ari ki zuba shi ainda Mahaifiyar yaron zata tsallaka, Indai hakan ta faru, shikenan kar kuji komai, amma fa sai kunyi sauri, dan ana son azuba abunne kafin ta yi magana da wanda ta yi magana da shi awaya". Farida kallan Malam mai biyan buk'ata dole ta yi, cikin damuwa ta ce, "Malam idan ta riga ta yi magana da shi shikenan ko mun zuba mata ta k'etara ba zai yiba? ". "Eh hakane, ba zai yiba". Shiru Farida ta yi, sannan ta ce, "Tom gaskiya indai hakane Malam ba zanyi amfani da maganinnan ba, dan Allah Malam kai min wanda daga anyine kawai magana ta k'are". Yadad'e yana zane-zane ak'asa, sannan ya ce, "kina son aiki d'aya daga shi shikenan? ". Kai Farida ta d'agamai. Ya ce, "Hakan zai yuwu amma fa sai kinyi hak'uri anyi auran yarinyar da Yaron, dan ta hakane kad'ai zamu samu biyan buk'ata, dole sai yaron ya kusanci yarinyar, tom kinga idan akai auran ai zasu kasance tare, tom alokacinne ke kuma zaki basu maganin". Ya mik'ama Farida maganin, ya ce, "Ki yi hak'uri za ayi aure amma auran ko sati ba zai yi ba, dan dama maganin zaifi tasiri idan yarinyar tana kusanci da shi sosai. Yanzu ki yi k'ok'ari ki basu maganin abinci ko abinsha, ki kwantar da hankalinki ni Malma mai biyan buk'ata dole nai miki alk'awari sai naraba tsakanin Yarinyar nan da yaron, ke kuma aure da shi babu fashi". Farida godiya taima Malam mai biyan buk'ata dole , sannan suka tashi suka tafi jikin Farida ba wani k'wari dan bata so haka ba, taso ace kar a d'aura auran nan kwata-kwata amma yaza ta yi inda Malam ya ce ta yi hak'uri ta bari ayi, aikinsu zaifi ci tahaka".
Haka su Farida suka tafi bama mai kowa magana tsakaninta da Hajiya Murja, kowa da tunanin da ya ke yi".
Can ko b'angaran Hajiya Turai, tana zaune ta ji sallamar manager. Bayan sun gaisane, Hajiya Turai ta kalli manager ta ce, "Manager kasan Habib tunda ya fara rashin lafiyar nan, baya yadda da kowa sai Hassana da ke aiki wajanku, tom shine na yanke shawarar had'asu aure, tana bashi magani da kula dashi kafin yaji sauk'i, shine nakiraka dan Allah ka zamarma Hassana waliyi zanma musa magana shi kuma sai ya zama waliyin Habib". Manager kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Kai Hajiya amma hakan ya yi sosai, amma bakya tsoran ranar da M, d, sai ji sauk'i yaga Hassana a matsayin matar shi? ". "Eh nasan wannan, dama daga yaji sauk'i shikenan zan warware abun cikin sauk'i, insha Allah badamuwa shiyasama nake son auran yazamana nasirri".
Hajiya Turai Baba Lami tasa ta kira mata Hassana. Bayan Hassana tazo ne, Hajiya Turai ta d'akko kud'i kimanin dubu d'ari, ta mik'ama Hassana , ta ce, "My daughter amsa". Hassana amsa ta yi, bayan Hassana ta amsa ne, Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "My daughter wannan sadakinki ne, kiba Manager su, shi ne waliyinki". Hassana gabanta ne yafara fad'uwa, cikin rawar hannu ta mik'ama manager sadakin. Hajiya Turai kallan manager ta yi, ta ce, "shikenan maganar zaka iya tafiya, dan Allah daga kunshiga sallah nake son ad'aura auran, kaga yanzu 12:39pm, yanzu za a kira Sallah, dan Allah ka hanzarta "..
Manager tashi ya yi ya tafi yana mamakin had'in nan da Hajiya zata yi".
Hajiya ko kallan Hassana ta yi, ta ce, "My daughter kije kiyi duk wani shiri da zaki yi, anjima zan ne me ki".
Hassana tashi ta yi ta tafi tana mai jinta wata iri kamar mara lafiya".
B'angaran manager ko ana idar da Sallar azahar dama ya yi ma Liman bayani. Ana idarwa aka d'aura auran Hassana da Habib, abisa saki dubu d'ari. Inda manager ya zamana waliyin Hassana , Liman d'in masallacin kuma ya zama waliyin Habib, dan sun jira musa baizo ba".
Bayan and'aura auran ne manager ya taho tan sanar da Hajiya Turai an d'aura aure...........
Idan kin karanta daure ki yi Comment sister 🤝
Share
&
Comment please 🙏
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Gaisuwar ban girma gareki sister Hafsat Yahaya Bakori, Alkairin Allah ya isarmiki aduk inda kike, rashin network ya hanani jin muryarki, nayi missing d'inki da kyau Wallahi 😭😭😭😭.
*ISTIGHFARI TANA SANYA NUTSUWA A ZUCIYA TANA KAWO BIYAN BUKATU WAJEN UBANGIJI UWA UBA KUMA ISTIGHFARI TANA BADA TICKET NA ALJANNA DIRECT😭*
Shafi na 36&37.
Hajiya Turai na zaune a falo, Manager ya yi sallama ya shigo.Hajiya Turai amsa Sallamar manager ta yi, sannan ta ce, "Bismillah manager ka zauna mana! ". Bayan manager ya zauna ne, ya kallai Hajiya Turai cikin nuna jin dad'insa ya ce, "Hajiya an d'aura auran". Hajiya Turai hawaye cike da idonta ta kalli manager ta ce, "Nagode manager". Can kuma sai kuka, manager cikin damuwa da ganin Hajiya Turai na kuka, cikin sanyin murya ya ce, "Hajiya dan Allah ki yi hak'uri, nasan maganar auran nan ce tasaki kuka, tom ya za'ayi haka Allah ya hukunta, addu'ar zakima m, d, Allah ya bashi lafiya". Hajiya Turai cikin muryar kuka ta ce, " Manager Wallahi ayanzu ba ciwan Habib nakema kuka ba, yanayin rayuwa nakema kuka, nagode maka manager Allah ya sakamama da alkairi nagode ". Manager sai da ya kwantarma Hajiya Turai da hankali sosai sannan ya tafi".
Hajiya Turai na zaune har kusan magriba amma shiru Hassana bata shigoba. Hajiya Turai jin shirun ya yi yawa aikawata yi aka kira mata Hassana".
Hassana ko wunin yau haka take yinshi duk bata jin dad'in jikinta, daga ta tuno wai za'a d'aura mata aure yau, gabanta sosai yake fad'uwa bakamar in ta tuno wanda za'a had'ata auran dashi ba, har wani d'an zazzab'i ke jin ya rufe ta. Hassana na zaune ita kad'ai ta yi ta gumi, d'aya daga cikin worker's d'in gidan ta zo kiranta. Hassana sai da gabanta ya fad'i jin Hajiya Turai nakiranta. Tashi ta yi kamar mara lafiya tabi bayan mai kirannata".
Hajiya Turai na zaune,Hassana ta yi sallama cikin sanyin muryarta mai tattare da rauni. Hassana guri ta samu d'annesa da Hajiya Turai ta zauna, sannan cikin girmama ta gaida Hajiya Turai, ta ce, "Hajiya gani". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi da kyau, sannan ta ce, "Zoki zauna kusa dani, kinji my daughter". Hassana tashi ta yi ta zauna inda Hajiya Turai ta nuna mata".
Hajiya Turai kud'in dake hannunta ta sama Hassana su a hannu, ta ce, "My daughter kirik'e da kyau, kud'in sadakinki ne ki yi wani abun da su".
Gaban Hassana har wani fat-fat, ya ke saboda fad'uwa. Ita kuma Hajiya Turai ta ci gaba da cewa"My daughter d'azu da Sallar azahar aka d'aura auranki da Habib". Shiru Hajiya Turai ta yi nad'an wani lakaci, sannan ta ci gaba da cewa, "My daughter dan Allah karki sama kanki damuwa kod'aya akan auran nan, Kamar yadda na fad'amiki indai Habib kikeji tom ki saki ranki, dan bazaima sanda maganar auran ba, kamar yadda na yi shi bai saniba, haka zan warware shi bai sani ba, dan Allah daughter ki saki ranki, babu abinda zai faru insha Allah ".
Hassana goge hawanda ke zubar mata ta yi, sannan ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Babu komai Hajiya, insha Allah babu damuwar da zansa maraina". "Yauwa daughterna, amma daga yau karki kuma cemin Hajiya, kirik'a cemin Mommy kinji?".kai Hassana ta d'agama Hajiya Turai ".
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "daughter daga yau zaki koma site d'in Habib da kwana, saboda rubutunda aka bashi, kinga ya kamata afara bashi rubutun, yanzu kije ki d'akko komai naki dake site d'in ku ki kai sie d'in Habib ki aje". Hassana da tom ta amsa ma Hajiya Turai, sannan ta tashi ta fita zuwa b'angaran su".
Hassana na zuwa ta iske Jimmai tana alwallar magriba, Hassana kud'in hannunta ta mik'ama Jimmai".
Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Hassana wa innan kud'infa?, ina kika samosu? ". Hassana bud'e baki ta yi za tai ma Jimmai magana kuka ya kub'uce mata".
Jimmai cikin tashin hankali ta ke tambayar Hassana ta ce, "Dan Allah Hassana kimin bayani mana, kin kawomin kud'i dayawa haka kin tasani kina kuka, kud'in waye? ". Hassana sai da tagama kukanta sannan ta kalli Jimmai ta ce, "Kud'in sadakina ke". "Kud'in sadakinki kuma!? ". "Eh, yanzu haka maganar da nake miki Hajiya ta sanar dani and'aura aur... ". Kukwane ya hana Hassana k'arasa abinda ta ke fad'i".
Jimmai ko cikin jin dad'i, ta ce, "Dan Allah and'aura auran? ". Hassana da kai ta ba Jimmai amsa".
Jimmai kallan Hassana ta yi gala-la, ta ce, "Haba Hassana yanzu wannan shine abin kuka, dan Allah meye abin kuka aciki ?, nidai indai zakiji nasihata tom kibar kukannan, ni Wallahi dani nasamu damar nan taki Hassana inajin saina yi party, dan Allah ni dai in dai kina son tarayyata da ke ta d'ore tom kibar kukan nan muyi magana! ".