← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 78

Sashe 13

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Can sanat yoghurt ko,haka akai aiki gun batare da anshare ba, ko angoge.
Yau kwana uku kenan Hassana na zaune gida bata da kud'in zuwa company. Tom kuma dama Hassana ce kad'ai mai sharar b'angaran, Billy duk ta ba sauran masu sharar suspension.
Yaune kuma abokan Habib wa inda su kai karatu tare suka kawo mai ziyarar bazata. Habib na zaune a office d'in shi ba zato ba tsammani, ya ji nocking. Izinin shiga Habib ya basu. Sai dai Habib sumar tsaye ya yi, da mamaki ke kallansu, rungume su su duka biyu Habib ya yi, ya ce, "Faruq, Nasir, zan rama, nima duk sanda zan yi visiting naku, sai dai ku ganni, ba bu Anousing". Habib zama ya yi yana nuna masu gurin zama. Wanda Habib ya kira da faruq, kallan Habib ya yi, ya yi murmushi ya ce, "Habib Allah ba zuwan siri bane mu kai, yanzu dai babu lokaci, mu shiga ciki Nasir yaga factory naka". Habib jagora ya yi masu yana kaisu kona suna gani. Wanda aka kira da Nasir ko sai yaba girman gurin ya ke, da tsaruwa irin ta gurin ya ke. Faruq, kallan Habib ya yi, ya ce, "Habib kasan Allah ina jin dad'in Yoghurt d'in ku sosai,dan gaskiya mutanan Taraba, suna son yughurt d'in ku sosai, dan manyan-manyan restaurant d'in Taraba duk inda kaje zaka samu sanat yoghurt". Murmushi Habib ya yi mai, ya ce, "Kasan ko kwanannan na ke son juwa Taraba dan bud'e sabon Company acan". "kai Habib, wai yanzu state nawa ke da branch a can". "Kano, Kaduna, sai nan Abuja". Habib suna tafiya suna tattauna da abokansa har suka isa, site d'in da ake Yoghurt d'in. Duk company babu inda ya kai gun girma, kuma site d'in ne Hassana ke aikin sharewa da gogewawa. Gashi yau har kwana uku kenan Hassana bata zoba, gun ya yi datti sosai dan har k'udaje ke ke waye gun saboda yadda ya yi. manager ko yau satin shi d'aya kenan da yin tafiya, yabar komai a hannun supervisor. Habib sosai ya ji kunyar yadda friend's d'in sa suka ga gurin. Hakan yasa Habib ya ja su suka koma Office d'in shi. Habib na kai su Office ya dawo gun ranshi ab'ace yana kallan ma'aikatan gun, Habib cikin daka tsawa da b'acin rai, ya kalli ma'aikatan gun ya ce, "Aikin waye wannan!? ". Yafad'i maganar ya na nuna gurin da hannu shi. Dukkan su shiru su kai dan ba sanin sunan Hassana su kai ba. Hakan yasa Habib ya kalli d'aya daga cikin staff d'in ya ce, "ki ramin supervisor ". Wanda Habib ya aika da saurinsa yabar gun ya nufi office d'in, Bill.
Billy na zaune da waya rik'e a hannunta tana charting ta ji ana mata nocking. Billy izinin shigowa ta bata. Staff d'in da Habib ya aika, kallan Billy ya yi, ya ce, "Sister Billy Oga Habib na kira". Billy kallan staff d'in ta yi, ta ce, ka ce mai ganinan zuwa, yana office d'in shi ne? ". "A, a yana site d'in mu". Yana fad'in haka ya juya ya tafi.
Billy kuwa jin Habib na kiranta powder ta k'ara shafawa da lipstick abakinta, sannan ta fita.
Habib na tsaye ranshi ab'ace, ga shi shi a ganinshi Billy ta b'ata mai lokaci. Habib na nan tsaye yana huci Billy ta tahu tana yauk'i ita Allah dole ga wadda Oga Habib ke kira. Billy na zuwa gaban Habib ta tsaya kamar zata shige jikinsa, ta ce, "Oga Habib ga ni". Habib ko, kallan k'askanci ya yi ma Billy sannan, ya ce, "Yama sunan ki? ". Billy cikin mamaki wai ita Habib ke ce ma ya sunanta. Billy kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib yanzu kamant.... ". Habib hannu ya d'agama Billy sannan ya ce,"Daga nan zuwa minti shafiyar idan har ba agyara gurin nan ba, tom ki gama aiki a sanat yoghurt, sannan wannan ya zamana na farko da na k'arshe, aiki kika zo yi ko shirme?, in dai baki gyara ba tom zamu da katar da ke! ". Habib na fad'in haka ya juya ya bar gun ranshi b'ace ya bar gun.
Billy kuka ne kawai ba tai ba , dan a cewarta Habib ya tozartata gaban staff. Hakan yasa Billy ranta b'ace ta ce, "Wata idiot d'in ce ke kula da site d'in nan". Wata daga cikin sttaf d'in ce ta ce, "supervisor new worker d'in nan ce, kuma yau kwana uku kenan bata zo ba, ina jin bata da lafiy.... ". Tsawar da Billy tai mata ce yasa tai shiru, ta ce"Allah yasa ubanta ne ya mutu tabar aiki amasana'artannan, kuma sai naci mutuncinta fiye da wanda Oga Habib ya ci min............

COMMENT
&,
SHERE
PLEASE 🙏
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Fabby baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

IDAN KA MUTU AN RUFE LABARINKA, AMMA ABUBUWA UKU SUNA RAYUWA A BAYANKA:
☝🏻ILIMI DA
✌️HAIHUWA SAI
AIKIN ALHERIN DA KA SHUKA. ALLAH KA SA MU DACE👏.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 14&15.
Chapter 13 · 0% Book details