← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 78

Sashe 58

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habib kuma Bilya ya kira awaya ya ce, "Bilya kazo yanzu". Habib na nan tsaye da Hassana Bilya yazo. Habib kallan Bilya ya yi, ya ce, "Ka kaita gida, idan ta gama abinda ta ke ka kaita nan kusa da mu d'innan inda ake makeup ai mata". Bilya cikin girmamawa ya ce, "Tom Insha Allah Oga Habib ".

Sannan Bilya ya tafi Hassana ta bi bayan shi. Billy ko da mamaki ta bi su da kallo, baka mar abinya yafi d'aure mata kai ba, ganin Habib ya ba Hassana ATM card d'in shi".

Hassana ko a hanya ta sa Bilya ya tsaya ya cirar masu kud'i, sannan suka biya suka sai duk wani abu da suke buk'ata. Hassana na zuwa ta shiga kitchen ta fara girki, ta ce," coconut rice zan yi irin wadda mu kai practice jiya. Cikin k'ank'anin lokaci Hassana ta gama duk abinda ta ke yi, sannan ta had'a masu lemun kwakwa, masha Allah. Ta jera komai a derning space. Bayan Hassana ta gama ko mai ne, ta shiga wanka, ta sa doguwar rigar da Hajiya Turai tai mata ta shadda, sanna ta samu Bilya a waje, suka tafi wajan makeup d'in ".

Bilya da kanshi ya ya yi magana da su akan ai mata mai kyau. Wayyo sister haka suka zauna suka cancara ma Hassana kwalliya. Wajan sa eyelashes ne aka samu matsala, dan Hassana cewa tai bata so, da kyar dai ta bari aka sa mata.sannan zuka amshi d'an kwalin suka d'aura mata".

Wato had'uwa iya had'uwa Hassana ta had'u, dan shi kanshi Bilya da Hassana ta fito da kyar, ya samu ya kauda idon shi akanta, azuciyar shi kuma yana ganin sakarcin Habib, ya ce, "wai kawai kasa matarka tai ma abokanka kwalliya kawai dan kar a raina ka,Allah ya kyauta ".kiran Habib ne ya katsema Bilya zan can zucinsa".

Bayan Bilya ya d'aga, Habib ya ce, "Bilya sun fa iso kun koma gida ne". "Eh gamu a mota zamu koma". Habib datse kiran ya yi, dai-dai nan kuma su Faruq suka shigo Sanat yughurt ".

Habib da fara'a ya rirrin gume su, zai yi Office d'in shi da su, Faruq ya ce, "Kai Malam gidanka za ka kai mu". Habib murmushi ya yi, sannan yaja Office d'in ya rufe, dama tun Kafin su iso Habib yasa an kawo mai mota agida. Habib da kanshi ya tuk'a motar zuwa gidan shi".

B'angaran Hassana ma kusan zuwan su kenan taji alamun hayanir zuwan abokan Habib d'in. Hassana bedroom d'in ta ta ruga. Su Faruq ko da fara'arsu suka shigo falon".

Bayan sun zauna , Faruq ya kalli Habib ya ce, "Kasan nifa banda dauriya, ina amarya?, na zaci ita zata tarbemu, ko dai kasa ta gudune". Faruq ya fad'i maganar yana dariya. Dan yau ya shirya rama duk abinda Habib ke musu akan duk budurwar da suka kawo mai, yadda ya ke kyarar su, daga ya ce bata da kaza sai ya ce, bata iya kwalliya ba, abubuwa dai Kala-kala ".

Habib tsaki ya yi, ya ce ma, "Faruq, tom bari kaji ko kad'an bana fargabar ku ganta, saboda ita d'in ba zab'ina bace kamar yadda na cema, zab'in Mommy ce, dan haka sai ku taya ni fad'ima Mommy ba ta yi ba, dan na riga ku fad'a, ya idasa maganar yana yin hanyar bedroom d'in Hassana".

Hassana zaune kusa da mirro sai kallan kanta ta ke, dan in dai mudubin nan ba k'arya ya yi mata ba, ta yi ma kanta kyau sosai ".

Ta mirro Hassana ta hango Habib, aiko da sauri ta sa hannu ta rufe fuskar. Habib ma da sauri ya idasa gunta ya sa hannu ya janye hannunta, ya ce, "Da Allah can zaki b'ata kwalliyar, ni cire hannun ki in gani ta yi kyau". Hassana cire hannunta ta yi ".

Habib ya kai minti biyar yana kallan Hassana. Dan shi dai in dai ya lura da kyau, sai ya ga kamar kwalliyar ta yi. Hassana bud'e idon ta ta yi da ke arufe, bud'ewa ta yi tana kallan Habib ta ce, "Kwalliyar ta yi kyau? ". "Friend's d'ina zasu tantance hakan, bani ba".Habib ya ba Hassana amsa. Sannan ya kamo hannun Hassana ya ce, "Meje su ganki suna falo".

Haka Hassana suka jera da Habib hannunsu cikin na juna, suka nufi falon. Faruq da sauran abokan tafiyar nasu, fira suke, amma suna ganin Hassana dukkansu bakinsu ya mutu, dan sosai kyanta ya tafi da imanin su. Jameel ne ya yi k'ok'arin sai ta nazuwar shi, ya ce, "Barka da fitowa Amrya". Sannan su Faruq ma suka dawo na tsuwar su".

Faruq yana d'an soka kai ya ce, "Barka da fitowa amarya agi dan Habib, gaskiya kin ciri tuta, ace duk gudun shi sai da kika cin mai, jinjina Amarya". Hassana da ke zaune kusa da Habib murmushi ta yi, ta ce, "Barkanku da zuwa, da fatan kunzo lafiya? ". "Lafiya kalau amarya". Cewar Usman Kenan". Bayan sun gaggaisa ne, Hassana ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib ga abincin su a darnin area, ko akawo nan". "To fa Oga Habib, kunji wani love name". Cewar Faruq yana dariya". Habib ne ya amshe zan can Kafin su Jameel su tanka, ya ce, "Da Allah can kuzo muje kuci abinci, kun tsaya kuna gulma".

Habib tasa su Faruq ya yi har derning space d'in, Hassana zuwa tai ta zizziba abincin a plate hud'u ta aje ma kowa a gaban shi, sannan ta aje jug d'in lemun kwakwa da tai masu, sannan tabar gun tana mai cewa, "aci lafiya".

Tun kan su Faruq suci abincin k'amshin da ya ke yi kad'ai ya tabbatar masu abincin ya yi. Wayyo dad'i haka suka ci gaba da ci ba ma mai kowa magana. Faruq bayan ya gama cinye wanda Hassana ta sa mai, mik'ama Habib plate d'in shi ya yi, ya ce, "Ni dai idan akwai Habib k'aramin, Wallahi ka yi da ce, yarinyar ta yi ga shi ta iya girki, wato Habib naso ace yau in huce fushina akan abubun da kai mana da, amma matarka bata da abinda zan rama abinda kai min, tabbas Hajiya ta cikama burinka da kace sai First class baby zaka aura, wannan yarinyar ta kai, wai ya sunan ta ne? ". Habib yana mai jin dad'in kunyar da Hassana ta fidda shi, ya kalli Faruq ya ce, "Sunan budurwarka da ta rasu". "Kana nufin sunanta Hassana? ". Kai Habib ya jinjina ma Faruq".

Tabbas ba a Hassanar banza, gaskiya ne dole ta zama kyakkyawa, dan kasan Allah ban tab'a ganin Hassana munmuna ba, duk inda zaka gansu zaka ga suna da diri, Allah sarki Allah ya gafarta ma Hassana". Cewar Faruq cikin damuwa. "Ameen ". Habib ya ce".

Nan dai suka kama cin abincin su suna santi. Bayan sun gama cin abincin ne, Faruq ya kalli Habib ya ce, "Habib end of this month ne fa bikin Jameel, yanzu haka yana daga cikin abinda ya kawo mu, dan haka sai ka shirya muje gidansu Yarinyar tare, dan yau d'in nan zamu juya". Habib tashi ya yi, ya ce, "Tom ku tashi muje ". "Ok, kira Hassana sai muyi sallama". Cewar Faruq ".

Habib bedroom d'in Hassana ya shiga ya kirata. Hassana zuwa tai ta ce, "Ba dai har zai ku wuce ba? ". "Wallahi amarya tafiya za muyi, zamu dawo babu dad'ewa auran Jameel". Kud'i masu yawa suka ajema Hassana a darning d'in, sannan suka tafi".

Bayan sun tafi Hassana tazo ta gyara gurin. Habib ko bashi ya dawo ba sai gaf da magriba. Lokacin Hassana na kitchen tana ma Habib kunu. Habib na zuwa side d'in shi ya shige, yana zuwa ya yi wanka, ya tada sallar magariba. Habib sai da ya yi sallar issha'i sannan ya fito falon. Lokacin Hassana bata falon. Habib guri ya samu ya zauna, yana nan zaune Hassana ta fito zata nufi kitchen d'akkoma Habib kunun shi dama wajan shi zata".

Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Zo". Hassana ci gaba da tafiyarta ta yi tai kamar bata ji ba. Habib da d'an k'arfi ya ce, "Ke bada ke nake ba". Hassana zuyowa ta yi, ta ce, "Oga Habib nifa ba Sunana ke nan ba". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Zo ki zauna nan? ". Ya nuna ma Hassana kusa da shi". Hassana dawowa ta yi ta zauna inda Habib ya nuna mata, ta ce, "Oga Habib gani".

Habib kallan Hassana ya yi ya koma hannun ta ya ce, " HaK'ik'a Kin fiddani kunyar Friend's d'ina naji dad'i sosai, dan haka ki zab'i duk abinda kike so, zan miki? ". Hassana bata san sanda ta tashi tsaye ba, ta ce, "Oga Habib kace duk abinda nake so? ".

Kai Habib ya d'aga ma Hassana. Hassana zama ta yi tana kallan Habib, ta ce, Oga Habib so nake ka ban matsayin Supervisor..... .. ✍️

Idan kin karanta daure ki comment sister 🤝

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Shafi na 70&71.

Kai Habib ya d'aga ma Hassana. Hasssana zama ta yi tana kallan Habib ta ce, Oga Habib so nake ka ban matsayin Supervisor ". Hassana ta fad'i maganar cikin k'osawa. Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "kamarya in baki matsayin Supervisor,bangane ba, yi min bayani? ". Hassana k'ara gyara zama ta yi, sannan ta ce, "Oga Habib nufina ka sauke Billy a matsayinta kaban". Kai Habib ya girgizama Hassana ya ce, "Haka ba zai yuwu ba, ki canza wani abun". "Tom kaban manager ". Cewar Hassana ".

Habib dariya ya yi, jin abinda Hassana ta ce, wai ya bata manager. Hassana tsayawa ta yi, tana kallan Habib, dan bata tab'a ganin shi yana dariya ba. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib dama kana dariya? ". Hassana ta fad'i maganar tana turo baki dan ta san ita yake ma dariya dan ta ce, ya bata manager".
Chapter 58 · 0% Book details