← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 78

Sashe 29

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana na nan zaune Jummai tazo kusa da ita ta zauna amma Hassana bata jiba. Jimmai hannun Hassana da tai ta gumi ta kamo ta ce, "Hassana tun d'azu da kika dawo kiran Hajiya nalura kike cikin damuwa, haba Hassana meye amfanin amintata da ke, idan har bazaki iya fad'amin damuwarki ba, koda banda abinda zan miki ai na taya ki da addu'a". Hassana d'ago kai ta yi tana kallan Jimmai sannan, ta ce, "Jimmai narasa yadda zanyi, amma ni bazan iya abinda suke so in yiba". Jimmai kallan Hassana ta yi dan bata gane takan zancan ta ba, ta ce, "Meye suke so ki yi? ". Shiru Hassana ta yi, sai zuwa can ta kalli Jimmai ta ce, "Jimmai kinsan Oga Habib tunda ya fara wannan ciwan baya yarda koda Hajiya tashiga gunshi sai dai ni, idan har bani na bashi abinci ba, ko magani tom ba zai shafa, hasalima da kyar ake fiddani duk lokacinda nashiga gurinsa, tom shine fa wai yanzu Hajiya take rok'ona akan in auri Oga Habib kafin yaji sauk'i in zauna dashi in yi jinyar shi".Jimmai cikin mamaki ta ke cewa, "Hassana dan Allah da gaske kike, Hajiya ta yi miki tayin auran Oga Habib? ". Kai Hassna ta d'agama Jimmai. Jimmai cikin rud'ewa da jin maganar ta ke cewa, "Amma dai Hassana kinzo gidan nan asa'a, dama ni, tom Wallahi ina baki shawara karki sake ki yi gangancin cema Hajiya baki yarda ba, haba Hassana wai meke damunki ne, wannan babban arzik'in nakiranki tsiyana na hure miki kunne". Hassana kallan Jimmai ta yi ta ce, "Jimmai baki tunanin ranar da Oga Habib zai bud'e ido yaga ni yake aura, arzik'in kawai kike hanga? ". Shiru Jimmai ta yi, sannan ta ce, "Hassana bafa ke kika naimi haka ba, su suka rok'eki, sannan lakacinda zai warke kamar yadda kike cewa, kingama arzik'i, kinga koma auran yak'are daga nan kingama zama Hajiya. Sanna ko ba haka ba da kunya ki koma ki cema Hajiya baki yarda ba, amma idan zaki iya tom , haba Hassana ke baki da burin komai ne arayuwarki?, wannan fa dama ce Allah ya baki, karki bari wannan damar ta wuce ki". Shiru Hassana ta yi tana tunanin maganganun Jimmai sannan ta kalli Jimmai ta ce, "Jimmai kina ganin ba matsala, bazan sa kaina a damuwa da tashin hankali ba, auran Oga Habib? ". "Hassana babu matsala ki yarda dani". "Shikenan Jimmai na yarda, amma daga Oga Habib yaji sauk'i nagama zama agidan nan baki d'aya ". Jimmai cikin kwantarma Hassana hankali ta ce, "ke dai ki yi addu'a Malam, amaryar Oga Habib". Hassana duka ta kaima Jimmai a baki ta ce, "Allah zaki sa in fasa". Nan dai Jimmai tai ta ba Hassana shawarwari masu kyau ".

B'angaran Balaraba maganin da Hajiya Murja ta bata a bakin zaninta ta nannad'e shi, tana d'ora girkin ta d'akko shi ta juye tass kamar yadda su Hajiya Murja suka ce tayi.Tana gama girkin ta sanar da Hajiya ta gama, nan ta kaima Hajiya nata, da duk wani wanda ki ci ana su Hajiya irin su Bilya da Baba Lami".

Farida ko tana ganin angama girkin ta tashi da kanta ta je ta samu Hassana, Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana dan Allah abinci Oga Habib zaki kai mai? ".Hassana tom kawai ta ce ma Farida".

Farida da kanta ta kai Hassana Falon Hajiya Turai ta d'auki abinci Oga Habib ta nufi part d'in shi".

Hassana ta yi nisa sannan Farida ta bi bayanta ta ce, "Hassana ga maganin Oga Habib ki bashi inji haji". Hassana amsa ta yi ta tafi, tana zuwa kai tsaye tashiga. Habib kamar yadda yasaba da saurinsa ya yo kan Hassana yana zuwa yarik'o mata hannu"

Hassana sai da tagama ba Habib abincin sannan ta bashi maganin da Farida ta bata ta bashi.
Farida da ke lab'e ta window tana ganin Hassana taba Habib maganin wani ihun dad'i ta yi, sannan ta je, ta kuma rufe k'ofar Falon ta baya, yadda koda Hassana ta ce zata gudu ba zata iya ba...................

Tofaaaa🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️

Idan kin karanta daure ki yi comment sister 🤝

Share
&,
Comment please 🙏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI(Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Allah ka zaunar da k'asarmu lafiya, Allah kabamu kwanciyar hankali ak'asarmu, Allah ka tsare musulminka aduk inda yake, dan Allah jama mu daure murik'a karanta HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL 11 duk sanda muka idar da sallar asuba. A bisaga Allah ya bamu zaman lafiya ak'asarmu.

Shafi na 32&33.

Farida na rufe k'ofar ta gudu ta bar gurin cikin jin dad'i.
Habib ko nashan maganin da Hassana ta bashi baifi da minti goma ba, ya fara jin wani irin yar ajikin shi. Mik'a Habib ya farayi yana kuma damtse hannun Hassana da yake rik'e da shi, yana kuma jawo ta kusa da shi.
Ita dai Hassana kallan mamaki tabi Habib da shi dan, idan ya rik'e hannunta shikenan daga haka, bai jajjawota jikinshi kamar yadda ya ke yi yanzu. Hassana kallan Habib ta yi ganin yadda ya ke rintse ido yana kuma damk'e hannunta yana ja wota jikin shi, kamar zai sata kan cinyar shi. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce cikin sanyin muryarta, "Oga Habib baka da Lafiya ne? ". Habib shi dai kallan Hassana kawai ya yi, ita kuma Hassana Sannu tai mai ganin yadda ya ke makyarkyatar sanyi, yana kuma damk'e hannunta. Can Hassana sai dai taji Habib ya fisgota da k'arfi ta fad'a kan shi, dan sai da sukai karo yana yin yadda ya fusgota d'in. Kafin Hassana ta yi yin k'urin yunk'urawa ta tashi daga jikin Habib sai ta ji, ya finciko hijab d'in jikinta yana k'ok'arin cirewa".

Hassana rik'e hijab d'in ta tayi sosai tana kallan Habib dake ciku-cikun cire mata hijab.
Hassana ganin yau Habib d'in, wani iri bakamar yadda ta saba ganin shiba, ga shi wai har yana ciku-cikun cire hijab d'in jikinta. Hassana dak'arfi ta fusge hannunta a hannun Habib, sannan ta juya da saurinta da niyyar fita. Sai dai ina kafin ta kai bakin k'ofar Habib har ya risketa, yana juwa ya rik'ota ta baya, yana rik'eta kuma Allah ya bashi sa'a ya fisge hijab d'inta"

Kafin Hassana ta gama tunanin lafiya sai dai taji Habib na k'okarin yaga rigar da ke jikinta. Nan fa kusan damme ya b'arke tsakanin su. Habib k'okarin cire rigar dake jikin Hassana ya ke, Hassana kuma tak'i bashi damar haka.
Da yake zani ne single ajikinta, hakan yasa Habib yana jan shi ya kwance. Hassana k'ara ta saki ganin Habib ya kwance zanin jikinta. Hassana mak'alk'ale Habib ta yi sosai tak'i bashi dama. Habib ko da dama bacikin hankalinshi ya ke ba, kuma ank'ara birgera k'wak'walwar, hakan yasa ya zamarma Hassana mahaukacin asali. Habib da k'afin tsiya ya yi wurgi da Hassana kan caution, sannan ya yi saurin binta, kan caution d'in.
Hassana ko kafin Habib ya zo tayi sauri ta tashi zata gudu. Habib garin ya jawo Hassana yana jawota ya jawo rigar jikinta ta yage . yarage daga Hassana sai brazier da pant. Habib cikin fitar hayyaci ya cire komai da ke jikin shi ya tsaya haihuwar uwarci".

Hassana cikin rud'ewa ta fara ihu tana kiran Hajiya Turai , da Oga Bilya.
Duk yadda Habib zai yi ya kwantar da Hassana ya kasa, dan firgitar da Hassana ta yi sai hakan yasa mata k'arfi. Habib ko cikin rashin sanin meye ya zai aikata, meye ya ke yi bai sani ba. Ya damk'i breast d'in Hassana. K'ara Hassana ta yi jin azabar yadda ya damk'i breast d'in ta. Cup d'in da ke kusa da Hassana na maganin da Farida ta bata ta ba Habib, ta d'akko ta buga ma Habib shi tun k'arfinta akai".

Habib jin azaba ya sakin Hassana yana tab'a gurin da Hassana ta buga mai cup d'in".

Hassana ko Habib na sakinta ta tashi ta ruga da gudu. Tana rugawa Habib ya bita. Kafin ya kamata Allah ya bata sa'a tab'ud'e toilet d'in bedroom d'in Habib ta shige ta rufe tana nishin wahala".

Habib ko bakin k'ofar ya tsaya yana jijjiya k'ofar kamar zai b'alleta".

Hassana sosai ta rud'e dan yadda ta ji Habib na jijjigar k'ofar gani ta ke zai b'alleta. Habib ko gajiya ya yi da jijjiga k'ofar ya zauna jikin k'ofar ya jingina da ita".

Hassana tana jiyo nishin Habib daga toilet d'in. Hassana shiru ta yi da kukan da take yi tanaaa sauraron nishin Habib tare da tunanin me ya sa mai haka. Wani tunani yazoma Hassana, dan tabbas idan bazata manta ba, itama kusan shigan haka ta yi lokacinda Farida ta bata magani ta sha ta ce mata inji Hajiya Turai. Tom wannan wana irin magani ne haka?, kuma meyasa nima da nasha naji haka?, sannan meyasa Hajiya bata tab'a ban da hannunta ba sai dai ta aiko Aunty Farida ta kawo min?, shiru Hassana ta yi, tana nazarin tambayoyin da tai ma kanta, tana naiman amsarsu. "Kai gaskiya wannan maganin akwai alamar tambaya atare da shi,tom amma kuma Aunty Farida ai bazata aikata abinda zai cutar da Oga Habib ba, ko da yake ai bashi zai cutar ba ni zai cutar, dan idan har tunanina haka ne da ace Allah yaba Oga Habib sa'a akaina tom da Fyad'e ya ke k'ok'arin yi min, kai gaskiya ban yarda da Aunty Farida ba, tom wai meyasa ma rannan ta maran dan nace mata banba Oga Habib maganin da taban in bashi ba?, tom kuma nima ai aranarne nashiga irin kusan halinda Oga Habib yashiga yau, dan idan bazan mantaba nima ranar haka naima kaina tsirara, kai gaskiya ban yarda da Aunty Farida ba, tom ni yanzu wazan fad'amawa abinda ke faruwa ya taimakan da amsar tambayoyina?. Gaskiya bazan iya fad'ama Hajiya ba, kuma bazan iya fad'ama Oga Bilya ba,inajin Jimmai zan fad'amawa dan nayarda da Jimmai tana ban shawarwari masu kyau, amma gaskiya ban yarda da maganin nan da Aunty Farida ta banba".
Chapter 29 · 0% Book details