← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 78

Sashe 71

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana rufe idonta ta yi da hannu, ta ce, "Na ganta". "Ok, saki nawa akasa aciki? ". Habib ya tambayi Hassana. Hassana sai yan zu abubuwan da tai suke fad'o mata, kallan Habib ta yi, ta ce, "Tom nikam na zaci haka kasa, shi yasa". "Uhm, sabo da shine aranki ba". Cewar Habib ".

Habib shiru ya yi sannan ya kalli Hassana ya ce, "SANAT zan auri Farida gobe, kina son zaki zauna nan ne tare da Mommy ko ko, zaki koma can ne da zama? ". Hassana da taji maganar Habib kamar ya buga mata mashi a k'ahon zuciya, shiru ta yi, dan bata ma san mai zata cema Habib ".

Habib ko jin Hassana ta yi shiru kai ya d'aga yana kallan ta, abin mamaki hawaye Habib yaga yana zuba a fuskar Hassana. Habib da bai san mai ya yi ma Hassana ba, cikin damuwa ya rik'ota, ya ce, "SANAT me yasa kike da saurin kuka haka ne?, ki yi hak'uri in dai tafiya ce ni zan kaiki, ko kuma in sa Bilya ya kai ki". Hassana tashi tai tsaye ta juyama Habib ba ya, sannan ta ce, "Oga Habib wai me yasa baza ka sake ni bane!? ". Hassana ta idasa maganar da kuka".

Habib da mamaki ya kalli Hassana, sannan ya tashi ya ce, "SANAT Kin ce kinga letter da na baki bikiga abin da nasa bane ajiki?, ". Habib ya fad'i maganar a raunane".

Hassana juyowa ta yi suna fuskantar juna da Habib sannan ta ce, "Oga Habib ka aje Farida duk in da ya yi maka nan ko can, amma ni garinmu nake son tafiya ka ban takardar ta ! ". Hassana ta k'arashe maganar da tsawa".

Habib da mamaki ya ke kallan Hassana, jin yadda ta ke mai magana da ihu, wai shi yau mace ke mai magana da ihu, Habib ma cikin zafin rai ya ce, "Bazan bayar ba, idan kinga dama ko yan zu ki tafi mana". Hassana cikin kuka ta ce, "Wallahi Oga Habib sai ka ban takardata Ba zan tab'a zama da kai da Farida ba, na tsaneta bana son ta, bana son ta!!! ". Hassana duk cikin kuka ta ke maganganun nan. Habib ko zama ya yi yana kallan ta, sannan ya tashi ya jawo Hassana ya zaunar da ita gefan shi, ya na kallanta, ganin yadda ta ke kuka. Habib kallan Hassana ya yi cikin damuwa, ya ce, "Tom naji ki yi shiru please, yan zu mai kike so? ". "Aini ba ce ma ka nayi ina son wani abu ba, amma dai nace in dai ka auri Farida sai dai ka saka..". Habib saurin rufe ma Hassana baki ya yi, da hannu ya ce, " Tom ki yi shiru na fasa auran ta d'in, ya yi? ". Habib ya fad'i maganar yana kallan Hassana, ba wai ya fad'i haka da gaske bane ya fad'a ne kawai dan Hassana ta yi shiru.
Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat me yasa baka son in auri Farida, ba kya tausaya ma halinda ta ke ciki ne? ". Hassana da ta tsagaita da kukan da ta ke turo baki ta yi, ta ce, "Oga Habib ni dai Allah in dai ka ce zaka auri Farida sai dai ka sake ni". Habib tsayawa ya yi yana kallan Hassana, sannan ya ce, "Biki ji ba ne, na ce miki zuciyata ta saba da ke , hannuna ba zai iya rubuta miki saki ba. ". "Tom yan zu zaka auri Farida ke nan!? ". Habib tsoran cema Hassana Eh ya yi, gudun rigimarta, hakan yasa ya girgiza mata kai, alamun a'a. Hassana kwantar da kanta ta yi jikin kafad'ar Habib ta ce, "Oga Habib dan Allah karka aure ta". Habib kan Hassana ya shafa ya ce," tom naji". Hassana ko tsabar dad'in abin da Habib ya ce, rungume Habib ta yi, ta ce, "Yauwa Oga Habib, nagode ". Habib dai shiru ya yi, dan bai san yadda zai yi ba ya kau ce ma auran Farida inda ya riga ya furta Maganar". Hassana ko tashi ta yi, ta ce, "Oga Habib zan tafi, tashi ka rakani". "Inna rakaki ni wa zai rakoni? ". Cewar Habib. Hassana ko kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib ai kai baka jin tsoro". "Uhm sabo da ni ba mutum ba ne". Habib ya ce ma Hassana ".

Hassana ko ganin Habib ba rakata zai yi ba, ta shi ta yi tai ma Habib sallama zata tafi, Habib ya san Hassana na da tsoro hakan yasa ya ce, "Duk abin da kika gamu dashi babu ruwana". Ai Hassana kamarma taga abun, da sauri ta fad'a jikin Habib, tana cewa, "Dan Allah Oga Habib ka raka ni ". Habib kallan Hassana ya yi ce, "Nikam tashi kije, biki san kin yi k'iba ba zaki fad'o min haka salan kikaryani". Hassana turo baki ta yi, ta ce, "Oga Habib ni yau she ma nayi k'ibar da zan karya ka". Habib tashi ya yi, ya ce, "Tom sarkin surutu ni na tafi sai da safe".

Hassana tashi ta yi, ta rik'o hannun Habib ta bi shi. Hassana na zuwa ta kwanta gefan gadon Habib ta ce, "Oga Habib tun baka da lafiya ra bona da kwana gadon nan". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Dama gadon kike kwana?, tom waya ce ki kwana min gado". "Kai kasa". Hassana taba Habib amsa".

Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Da nai me ne nasa? ". Hassana tuna ranar da Farida ta bata maganin da ya hirgitsa rayuwarta ta yi, ranar da ta fara kwana kan gadon Habib. Hassana tuna haka ne, yasa tai sauri ta juya ma Habib baya, ta ce, "Da Kai ko mai ma, tom kai Oga Habib me ye ma ba kai ba". Habib zaro ido ya yi waje , ya ce, "kamar me da me? ". Hassana kwanciya ta yi, taja bargon Habib ta rufe kanta duka, ta ce, "Oga Habib sai da safe, bacci nake ji". Habib rabuwa ya yi da ita dan maganarta ta k'arshe ta sashi tunani, da ya yi komai ma, tom kai Oga Habib me ye ma ba kai ba. Ya mai-maita maganar Hassana, kai k'arya ta ke Habib ya fad'a azuciyar shi".

Habib wanka ya shiga yana ta repeating d'in maganar Hassana, wata zuciyar ta ce mai tom ko shiyasa Mommy ta had'a aure na da ita. Habib wannan tunanin da ya yi yasa ya yi sauri ya gama wankan shi, ya fito,doguwar rigarshi ka wai yasa, ya hau gadon , Habib shiga bargon Hassana ya yi, Hassana da ba tai bacci ba tana jin duk wani motsin Habib, Habib rungumo Hassana ya yi, ya ce, "Sanat zan tambayeki ki fad'a min gaskiya please ". Hassana rintse ido ta yi, jin yadda Habib ya rik'e ta, Habib kuma ya ci gaba da cewa, "Me yasa Mommy ta had'a aure na da ke? ". Hassana shiru ta yi, sannan ta ce, "Sabo da idan nazo kawo ma abinci baka barina in tafi, sai dai in kwana nan". "Shine da lili Habib ya tambayi Hassana". "Eh shine dalili". Hassana taba Habib amsa ".

Habib kallan Hassana ya yi da idonta ke a rufe, ya ce, "Ya kika ji lokacin da Mommy tai miki ta yi aurena? ". Hassana bud'e idonta ta yi tana kallan Habib ta ce, "Na shiga tashin hankali sosai". "Me yasa kika shiga tashin hankali? ". Habib ya tambayi Hassana. "Sabo da ina tsoran ranar da zaka farga kaga ni ce Mommy ta had'a ka da ita". Cewar Hassana ".

Shiru Habib ya yi, sannan ya ce, "Tom ya kika ji lokacin da na samu lafiya? ". "tom da farko dai naji dad'i sosai lokacin da na tabbatar kaji sauk'i, danni lokacin na saba da kai, sai dai ina cikin mugun tsoran kasan Mommy ta had'a ni aure da kai". Habib shafa kan Hassana ya yi, ya ce, "Mai tsoro ka wai. "Tom Oga Habib ba dole mutum yaji tsoranka ba, kai fa ko dariya baka yi".

Murmushi Habib ya yi. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib kai ya kaji da kasan Mommy ta had'a mu aure? ". "Banji komai ba". Habib ya ba Hassana amsa".

Turo baki Hassana ta yi, ta ce, "Allah ba wani nan, abin da ina ganin ka kana hararata idan kashigo". Murmushi Habib ya sake yi, sannan ya ce, "Serious lokacin da nasan Mommy ta had'a ni aure da ke banji ko mai ba, kawai dai ina kunyar friend's d'ina suji ina auran staff d'ita". Uhm, Hassana ta ce, Sannan ta ce, "Tom yan zu fa ya ka ke ji ". "D'aya da yadda nake ji da, kawai dai na yi hak'uri ne ganin Mommy na son ki".

Hassana ta shi ta yi da sauri zata sakko kan gadon, Habib ya rik'e ta sosai yadda ko motsi bata iya yi. Hassana kamar za tai kuka ta ce, "Allah Oga Habib ka sakan ni tafiya zan yi, ba zan kwana nan ba". Haka Hassana tai ta cucu-cuku ita ala dole bazata kwana nan ba. Habib ganin da gaske ta ke, dan Hassana ta iya birkicewa. Habib cikin kunann Hassana ya fara magana kamar haka, "SANATT Allah wasa nake, yan zu Ina jinji cancikin tsakiyar lugun k'arshen zuciyata, Sanat ke d'aya ce ina soooon ki". Wayyo dad'i wato kalmar soyayya tafi komai dad'i idan ta fito daga bakin wanda kake so".

Hassana wani rin sanyin dad'i taji yana shiga cikin k'ofofin jikin ta. Hassana hannu tasa ita ma ta rungume Habib ta kasa furta komai a bakin ta. Habib ko jin Hassana ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai shige mai da ta ke kuma yi, hakan kad'ai ya tabbatar mai ta yi appreciate d'in maganar. Habib cikin kunnan Hassana ya rad'a mata ya ce, "SANAT kin yarda mu zama d'aya ni da ke a yau....... ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.

Share
&
Comment please 🙏.
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/
Chapter 71 · 0% Book details