← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 78

Sashe 24

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida da Mahaifiyarta zaune agaban Malam mai biyan buk'ata dole. Hajiya Murja kallan shi ta yi, ta ce, "Malam kamar yadda nafad'ama aiki dai kuskure aka samu bai yiba". Bak'in katon da Hajiya Murja ta kira da Malam, cikin fad'a-fad'a ya ce, "Hajiya kunzo nan keda yarinyarki akan in muku aiki asama Yaron nan son yarinyarki nace muku ba zai yuwuba, saboda mu munayin abinda zai yuwune, sannan yaron nada wani murd'add'an hali, aikin zai bamu wahala, Nina baku shawarar juya gwagwalwar yaron nan, sannan asa mai k'inyarda da kowa sai 'yarki kad'ai, sai kuyi amfani da damar yarda da 'yarki da yake yi kuhad'asu aure, bayan aure in warware aikin da nai me, sannan kafin in baku maganinnan wana irin jan kunnene ban muku ba, na dad'e Ina nana ta muku karku sake yarinyarki tayi nesa dashi, amma taya kuka yi sakaci haka ta faru? ". Farida cikin rawar murya ta ce, "Wallahi yaron shine yajamin, yanzu dan Allah asake min wani abun wanda zaiwarware wancan konawane zan bada". "Wata irin dariya ya yi sannan ya ce, "Ya sunan yarinyar da yake yadda da ita? ". Farida da Hajiya Murja had'a baki sukai wajan cewa, "Hassana".

Wani 'yan Zane-zane ya yi sannan ya ce, " Abin bawani mai wuya bane, amma dole sai yaron nan ya kusanci yarinyar da yake yarda da ita yanzu haka, sannan koda wannan makarin sai karye, yanzu akwai abinda zan baki ki tabbatar kinba yarinyar taci shima yaron yaci, idan har ya kusanci yarinyar shikenan, zaki zama dake kad'ai yake yarda Mahaifiyarshi da kanta zata had'a auranki da shi".

Hajiya Murja kallan bak'in k'aton banza ta yi, ta ce, "Ba komai ka bata abinda zata basu d'in, sannan ita yarinyar in sonsamune gudin matsala muna so arabata da gidan ". Wata mahaukaciyar dariya yayi ya ce, "Shikenan damuwarku da zo k'arshe, sai ni Malm mai biyan buk'ata dole, da kazo gurina buk'atarka bata biyaba, gara in bar aiki". Haka yagama yi ma kanshi kirari sannan ya d'auki wani bak'in abu kamar d'inya ya ce, "Wannan abun da kike gani, daga kin je gida yanzu zaki jik'ashi aruwa ya kwana tom ruwanne zaki ba yarinyar ta sha shima yaron yasha". Wata muguwar dariya ya yi sannan ya ce, "Aikinki yagama ci yarinya".

Godiya sosai Hajiya Murja tai mai sannan takama hannun Farida suka bar gun suka je inda su kai parking d'in motarsu suka shiga suka kama hanyar gida. Suna cikin tafiya Farida ta kalli Mahaifiyarta ta ce, "Mommy nifa gaskiya ban yarda da abinda Malamin nan yace ba, gaskiya ni bazan bari ya kusan ci k'azamar yarinyar nan ba, kuma ko ba ma haka ba, ni dai ina kishin haka". Kallan baki da hankali Hajiya Murja tai ma Farida, sannan ta ce, "yanzu ya kike so ayi, kina jidai abinda ya ce hakane kad'ai makarin abin, amma idan kina da wata shawarar tom? ". Eh ina da ita Mommy..........

Idan kin karanta daure kiyi Comment sister 🖊

SHERE
&
comment please 🙏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

_🍃 Baya halatta likita ya ke6anta da mace mara lafiya (ya zanto daga shi sai ita) don duba lafiyarta, dole ya kamata a samu mijinta a wurin ko wani muharraminta a lokacin da ake dubata._
📒 فتاوى اللجنة الدائمة 422/24

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 26&27.

Farida cikin shagwab'a ta fara yi ma Mahaifiyarta bayani, "Mommy ni dai gaskiya banyarda da maganar Malam ba, inajin kishin ace Oga Habib ya kusanci yarinyar nan, gaskiy inajin kishin haka sosai Mommy, dan Allah ayi wani abun, basai Oga Habib ya kusanci Hassana ba". Hajiya Murja hannun Farida ta kamo ta ce, "Farida ki yi hak'uri, sadoda Malam mai biyan buk'ata dole abinda zai yuwu ya ke yi, amma inda kink'i yarda,yanzu idan nakira shi me kike son ince mai? ". "Mommy ce mai za ki yi, konawa ne zaki biyashi, duk yadda zai yi yayi ya k'arya abin batare da Oga Habib ya kusanci Hassana ba, zaki bashi konawa ne".

Hajiya Murja kiran Malam mai biyan buk'ata dole ta yi, yana d'agawa ta ce, "Hello Malam, dama Farida ce ta ce wai babu yadda za ai dole sai Habib ya kusanci yarinyar?, dan Allah idan akwai yadda za ai Malam dan Allah zan biya konawa ne, dan Allah atai makamin, abiyamana buk'atar nan". Cikin fad'a-fad'a Malam mai biyan buk'ata dole ya ce, "Hajiya tun farko fa sai da nafad'a muku ni abinda zai yuwu nake yi, dan haka hakane kawai makarin abin, dole sai yaron ya kusanceta sannan". Yana fad'in haka ya kashe wayar shi".

Dayake wayar a speaker ya ke shiyasa Farida ta ji duk abinda Malam ya ce. Hajiya Murja kallan Farida ta yi ta ce, "Farida kin dai ji abinda Malam ya ce ko?, dan haka ki yi hak'uri, kinga dai ita yarinyar rabata da gidanma za ai". Farida cikin shagwab'a ta ce, "Mommy naji nayrda, amma ni ina gudun matsala ne, idan fa aka samu kuskure". Hajiya Murja cikin kwantarma Farida hankali, takamo hannunta, ta ce, "Farida Wallahi kinji narantse ko zan k'arar da abinda na mallaka ne sai kin auri Habib, dan haka kirkiji komai ni na san Waye Malam mai biyan buk'ata dole, shifa akinma da bazai iya ba baya amsar shi, karfa ki manta ko yanzu daga gurinmu aka samu matsala, ba daga gun Malam ba, tun farko da ace kina gun abin ya riski Habib da yanzu anwuce gun, dan haka ki kwantar da hankalinki, indai Habib ne ki d'auka kin aurai kin gama". Farida cikin jin dad'i ta rungume Mahaifiyarta, ta ce, "Mommy wannan shine burin rayuwata in auri Oga Habib, kai Mommy Allah da nafi kowa sa'a, ga kyau, ga Ilimi Mommy, Uwa-uba ga kud'i ".ita dai Hajiya Murja murmushi kawai ta yi ma Farida bata ce komai ba.
Nandai sukai ta firarsu. Dai-dai junction d'in area gidansu Habib Hajiya Murja tai parking, kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida ki hau napep ki k'arasa, bana son idasawa ciki, idan Hajiya Turai ta tambayeki ina kika je kice mata guna kikazo, nace gobe zanzo gaida Habib inda rud'ewa tasa ta manta bata fad'amin ba".

Farida napep ta samu ta hau tak'arasa da ita gidan su Habib. B'angaran Bilya ko tunda Hajiya Turai ta bashi maganin Habib ya samu Musa suka shiga ba Habib magani. Zaune su iske Habib inda ya ke zama. Habib na ganin shigowarsu Bily yayo kansu kamar yadda ya saba.Nan fa su Bilya suka rik'e Habib. Sai dai ina Habib ya fi k'arfinsu, dan duk yadda suka so su d'ura ma Habib rubutun abin yaci tura, dole suka hak'ura suka rabu da shi, daga k'arshe suka sashi a bedroom shi suka rufe shi, suka suka gudu".

Bilya kusan karo suka ci da Farida ita kuma lokacin zata shiga falon Hajiya Turai, shima kuma ya taho da saurinsa yana nishin wujijjigasu d'in da Habib ya yi".

Hajiya Turai na zaune Bilya ya k'araso inda take, Bilya cikin alamun damuwa ya ce, "Hajiya Wallahi duk yadda za muyi munyi, amma Oga Habib yak'i shan rubutun nan". Hajiya Turai da ta rasa abinda zata ce kawai sai ta sa, kuka. Bilya cikin damuwa ya ce,"Hajiya dan Allah ki yi hak'uri, shi kukan babu abinda zai miki, insha Allah Oga Habib zai ji sauk'i nan bada dad'ewa b, Hajiya dan Allah indai dan maganar rubutu ne ki yi hak'uri zai sha, gashinan nasa ankiramun Hassanar". Bilya be rufe baki ba sai ga Hassana ta shigo".

Hassana cikin girmamawa ta gaida Hajiya Turai, sannan ta ce, "Oga Bilya gani ance kana kirana". Bilya kallan Hassana ya yi yace, "Hassana dan Allah magani zaki ba, Oga Habib da abincin shi? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Tom Oga Bilya ".

Bilya mik'ama Hassana maganin ya yi.Hajiya Turai kallan Bilya ta yi jin bai cema Hassana da nasha biyun dare ba, ta ce, "Bilya na daranfa, wazai bashi? ". Kafin Bilya ya yi magana Hassana ta yi wuf ta ce, "Ni zan bashi Hajiya". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta rik'e hannun Hassana ta ce, "Hassana nagode Allah yasaka miki da mafificin alkairi". Da ameen Hassana ta amsa".

Hajiya Turai kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya dan Allah tai makon da kai kuma zakuyi min kai da Musa, idan Hassana taba Habib maganin sha biyun daran, ku kuma dan Allah sai kuje kufitomin da ita, Allah bashi sai ku kawota wajena ta kwana". Bilya cikin girmamawa ya ce, "Insha Allah Hajiya badamu".

Hassana bayan ta amshi rubutun da zata ba Habib, kallan Hajiya ta yi, cikin sanyin muryarta ta ce, "Hajiya duka za abashi yanzu? ". "A'a wannan nafarar gorar shine na sha biyun dare, wannan kuma sai gobe ma za afara amfani da shi".

Hassana d'aukar maganin Habib ta yi sai abincin shi ta nufi part d'in Habib d'in. Farida da kallo ta bi Hassana acewarta samun guri, wato yauma anan zata kwana, wani tunanine yazo ma Farida, aiko da saurinta ta tashi ta fita, dan Hajiya Turai na mata maganama sai ce mata tayi zata dawo yanzu".
Chapter 24 · 0% Book details