← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 78

Sashe 51

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habib ya ce, "please Mommy idan maganar aure ce da kike min zanyi yanzu, kiban duk lokacinda ya yi miki, amma ki fahimci abinda nake nufi Mommy, da farko ni ban tab'a sha'awar rayuwa da mai aiki a k'ark'ashina ba, sannan Mommy Friend's d'ina zasu yi min dariya suji Ina auran staff d'ina, kuma cleaner, dan Allah Mommy ki fahimtan, ni zanma yarinyar duk abinda kike so, amma banda wannan Mommy ". Habib ya idasa maganar cikin damuwa ".

"Habib ba wai kai ba, Hassana ma ayanzu inajin na isa da ita akan maganar nan, nariga na gama magana, yau-yau d'innan zaku tare a gidanka! ". Habib tashi tsaye ya yi daga zau nan da ya ke, yana kallan Hajiya Turai, dan sosai maganarta ta k'arshe ta furgitashi".

Habib kusa da Hajiya Turai ya dawo ya zauna, ya ce, "Mommy naji na yarda zan zauna da ita, amma Mommy a gidannan dan Allah ". Hajiya Turai kallan Habib ta yi yadda ya wani rud'e ta ce, "Habib na yanke wannan shawaran ne saboda Hassana idan taci gaba da zama a nan Fad'a zasu yi ta yi da Farida, ni kuma inada kawaici bana iya korarta, shi yasa kawai na yanke shawarar ta koma gidanka da zama". Habib cikin sauri ya ce, "Mommy ni zan kori Farida yau-yau d'innan idan ke baza ki iya ba". "Habib nagama magana dan tun jiya kafin in dawo na sa anke komai agidan, dan haka bana son wata doguwar magana nariga nagama magana, dan haka zaka iya tafiya". Cewar Hajiya Turai ".

Habib bai k'ara magana ba ya tashi ya fita. Hajiya Turai saurin juyawa ta yi tana kallan Hassana jin shashshek'ar kuka. Hajiya Turai, hannun Hassana ta kamo, ta ce, "Daughter ki yi hak'uri idan na b'ata miki, amma nasan insha Allah watarana daga ke har Habib zaku fahimce ni, dan Allah daughter ki yi hak'uri na rok'eki, idan ma zaman kad'aici kike tunani zan baki Maimuna ta rik'a d'ebe miki kewa, ke dai abinda nake so da ke karki biyema miskilanci Habib dan Allah , ki gaida shi ko ba zai amsa miki ba, mahakurci mawada ci ne, yanzu kije ki yi wanka ki kwanta ki huta".

Hassana kamar jira ta ke, da sauri ta tashi ta shiga bedroom d'in ta. Hajiya Turai da kallo tafi Hassana".

Farida ko cikin tashin hankali ta fita ta kitchen ta nufi gidan Hajiya Zaliha friend d'in Mahaifiyarta".

Farida nazuwa, ta sama Hajiya Zaliha kuka. Da kyar Hajiya Zaliha ta samu ta lallashi Farida, sannan ta ce, "Yanzu daughter fad'amin me Habib d'in ya kuma yi miki? ". Farida cikin kuka ta ba Hajiya Zaliha labarin duk abinda ya faru, ta had'a mata da tarewar da Hassana za ta yi yau, kamar yadda taji Hajiya Turai ta ce".

Hajiya Zaliha lallashin Farida ta yi, sannan ta ce, "barni da su daughter in sun san wata ai basu san wata ba, yanzu bu d'aya ya rage mana inda tabar gidan da zama, ganin Habib da ita zai miki wuya, dan haka abinda zaki yi yanzu aiki zaki naima a Sanat yughurt". "Aiki kuma Mommy? ". Cewar Farida".

"Eh aiki zaki naima Farida acan, dan dole sai kina tare da Habib burunmu zai cika idan ki kai nisa da shi abin ba zai yuwu ba, dan haka gobe ki shirya kije neman aiki gun"Wani murmushi Farida ta yi, ta ce, "Tabbas wannan dama ce babba Mommy, ni kuma zanyi amfani da dabarunki in had'a da nawa". Dariya Hajiya Zaliha ta yi, ta ce, "Yauwa daughter kin fara ganewa, yanzu sai goban in kin samu aikin sai mu tsara yadda abin zai kasance". Haka Hajiya Zaliha tafa tsarama Farida yadda zata kasan ce idan ta samu aikin".

B'angaran Hassana ko, ko da ta kwanta kasa bacci ta yi, juyi kawai ta ke, dan sosai ta ki jin furgici idan ta tuno wai yau zata tare a gidan Habib. Hassana ganin kwanciyar bayi mata za tai ba, tashi ta yi ta nufi part d'in worker's d'in gidan, ta je wajan Jimmai ko zata ji sauk'in yadda ta ke ji, dan Jimmai ta bata shawarwari masu kyau na kwantar da hankali".

Hassana inda ta saba ganin Jimmai ta sameta , Jimmai da fara'arta ta tari Hassana, tana cewa, "Tom yau kuma me yafaru, dan ni dai tunda kika bar nan na bar ganinki sai taki ta kawo ki". "Aunty Jimmai ki yi hak'uri, Ina cikin damuwa Nazo ne ki fad'amin magana mai dad'i ko zanji dad'i". Cewar Hassana ".

Jimmai hannun Hassana ta kama suka zauna, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Fad'amin damuwaki kinji Hassan? ". Hassana cikin damuwa ta ce, "Sister Jimmai yau zan tare a gidan Oga Habib, Hajiya ta nuna min fin k'arfi ta ce bazata raba auran ba, Wallahi Sister Jimmai idan kikaga yadda Oga Habib ya rud'e tsabar bai son zama dani abin zai ta damiki hankali, ni kaina nasan Hajiya ba taima Oga Habib adalci ba, saboda Oga Habib ya taka mata kai ma su girma da kwari arayuwarshi, ya kamata Hajiya ta had'ashi da dai-dai dashi amma bani ba". Hassana ta idasa maganar tana share hawayanta".

Jimmai hannun Hassana ta kamo ta ce, "Hassana ki kwantar da hankalinki Oga Habib bai isa ya raina miki ba, dan haka karma kiwani k'ara tunanin wai ya wuce da ajinki. Yanzu Hassana idan kin ce ma Habib ya sakeki, kin san kin b'atama Hajiya, kuma kina tunanin zata ci gaba da zama da ke, idan kuna kince ki koma garinku, ko kin san zaki fuskanci wata irin rayuwa fiye da wadda kika baro,dan haka ni Ina baki shawarar ki yi hak'uri ki zauna da Oga Habib lafiya, duk abinda zai miki ki yi hak'uri, watarana sai labari. Yanzu me ye kika san Oga Habib naso? ". "Ni ban san abinda ya ke so ba". Cewar Hassana ".

Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce," tom ni zan fad'amiki abinda Oga Habib ke so ai farkon zuwana gidan nan, b'angaran Hajiya na fara aiki, Oga Habib na son kunu sosai, dan haka ya kamata ki koyi kunu kala-kala". Hassana Kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Tom ta ya zan koya, idan ma na koya kina tunanin zai sha idan nayi? ". "Tsab ma kuwa zai sha, ai ke zaki sashi ya sha, akwai wata makaranta ta koyan girkegirke idan kin wuce national assembly na nan apo School d'in take, tom amma gaskiya da tsada fa, amma zaki iya girgi kala-kala, yanzu babu yadda za ai ki samu kud'i gurin Hajiya Turai? ".

Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Babu, amma tunda na fara aiki a Sanat yughurt basu tab'a biyana ba, dan haka zanma Oga Bilya magana idan suka ban sai in yi amfani dasu". "Yauwa ki mai cikin satin nan ki fara zuwa". Hassana godiya taima Jimmai sannan tai mata Sallama ta tafi".

Da daddare bayan Sallar Issha'i, Hajiya Turai jin Habib shiru har yanzu , kiran shi awaya tai, ta ce, "Hello Habib kazo yanzu Ina son ganinka". Hajiya Turai na fad'in haka ta kashe wayarta, sannan ta tashi ta shiga ciki , tana kallan Hassana da ke zaune. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Wai daughter har yanzu biki shiga wankan ba ga Habib nan zuwa, shikenan in bazaki wankan ba in kinje can kinyi ai".

Hassana batare da tace komai ba, ta tashi ta shiga wankan. Kafin Hassana ta fito Hajiya Turai ta d'akkoma Hassana wata doguwar riga fara mai ratsin pink da tazo mata da ita, rigar ta yi kyau sosai".

Hassana na fitowa Hajiya Turai ta bata rigar, sannan ta fita ta bata gu ta shirya".

Hassana sama-sama ta shafa mai ta sa rigar. Masha Allah sosai rigar ta amshi Hassana ta fito mata sosai da sharp d'in ta. Hassana bayan ta shirya ci gaba da zamanta ta yi".

Can Falo kuma, Habib zaune gaban Hajiya Turai, Hajiya Turai kallan Habib ta ti, ta ce, "Habib ga Hassana nan amana na baka ita, idan ka cutar da ita ba baki naima ba, amma Allah ba zai barka ba , Habib ko dan halaccin da taima dan Allah karik'eta amana, idan kuma ba kai mata dan haka ba, ka yi dan maraicinta, kasan dai hukuncin wanda ya zalinci maraya, bari in kirata ku tafi, ka sa Bilya ya kaima kayanka ko? ". Habib ciki-ciki ya amsa ma Hajiya Turai da cewa, "Eh ya kai".

Hajiya Turai ta shi ta yi, ta je bedroom d'in ta, zaune ta iske Hassana ta yi ta gumi. Hajiya Turai hannun Hassana da tai ta gumi ta koma, sannan ta d'akko oud aribian perfume masu k'amshi ta shafama Hassana, ta ce, "A akayanki da nasa miki, kirik'a shafawa kinji daughter, nasan kuma ke dama mai son tsabta ce, na ba tailor na d'in kayanki, ya d'inka miki, Bilya zai amso miki, dan Allah daughter karki biyema Habib kinji, ko ba komai kinga yanzu yana matsayin miji gareki ki ne, ki kyautata mai kodan kwad'ayin lada agurin Allah, ki rik'a girki da shi kullum koda ba zai ciba karki ki hanashi kinji, daughter, Allah ya yi miki Albarka Allah ya albarkaci auranku, Allah ya kauda fitina a tsakaninku".

Hassana kuka take sosai, a haka dai Hajiya Turai ta kawota Falon. Habib na zaune da wayar shi yana danne-danne. Hajiya Turai zama ta yi, ta kalli Habib ta ce, "Habib ga daughter nan nabaka amana, kaji min da ita sosai, karka sake kabar hawayanta su zuba k'asa". Habib tab'e baki ya yi".

Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, ta ce, Muje in rakaku".

Hajiya Turai har Mota ta kai Hassana wadda har yanzu ta ke kuka. Bayan Hajiya Turai ta sa Hassana mota ne Habib ma ya shiga".

Hajiya Turai tana nan, tsaye Habib ya tada motar yaja suka tafi.
Sannan Hajiya Turai ta koma cikin gida tana hawayan farinci......... ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment Sister 🤝.

Idan naga Comment da yawa, Gobe zaku ya Update idan naga kad'an tom zafa kuji🤐🤐🤐.

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
Chapter 51 · 0% Book details