← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 78

Sashe 11

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

PLEASE
COMMENT &
SHARE.
📚OGA HABIB📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Mak'iyanka mutane uku ne:Mai k'in ka, da mai k'in masoyinka, da mai son mak'iyinka. Mai son uwa dole ne ya so d'anta. Allah ka had'amu da masu son mu fisabilillahi.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 10&11

Habib da kallo ya bi Hassana da shi.
Hassana ko cikin da burcewa da kallan da ya ke mata, ya sa ta mik'a mai file d'in hannunta, ta ce, "Oga Habib ga shi inji manager ya ce ka yi marking d'in abubun da ake buk'ata". Hassana ta idasa maganar muryarta na rawa.
Habib amsar file d'in ya yi, batare da ya kalli ko inda ta ke. Habib na amsar file d'in Hassana ta juya da saurinta tafita office d'in.
Hassana na fita office d'in Habib ta had'u da wata staff itama agun ta ke aiki, amma ita tana cin masu programme d'in sanat yoghurt. Hassana da sauri ta k'arasa gunta ta ce, "Baiwar Allah dan Allah tambaya na ke? ". Wadda Hassana ta kira da ke, juyowa ta yi tana ma Hassana wani kallan lafiya.
Hassana itama kallanta ta yi, azuciyarta ta ce, kai gaskiya 'yan aikin gunnan suncika ji da kai, sai kace wasu masu aikin banking. Ita ko staff d'in nan jin Hassana ba ta ce mata ko mai ba, ya sa juya ta cigaba da tafiyarya zuwa inda zata. Hassana ganin ta tafi ta barta gun tsaye da sauri tasha gabanta, ta ce, "Yi hak'uri dan Allah office d'in manager na ke nema? ". Wani irin kallo ta ke ma Hassana dan ita bata tab'a ganin Hassana ba a ma'aikatar nan ba. Hakan yasa ta kalli Hassana ta ce, "Wacece ke? ". Hassana batare da tadamu da irin kallan da ta ke mata ba, ta ce, "Ni new worker ce a factory nan". Da hannu ta nuna mata office d'in manager ta juya tayi tafiyarya. Hassana ko kanta a k'asa ta juya ta nufi office d'in manager. Hassana na zuwa cikin girmamawa ta gaida manager dan tana ganin girmansa sosai, tai makon da ya yi mata. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Oga Manager dama bansan site d'in da zan rik'a mopping bane". Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, " supervisor zaki ma magana. Ki ji Office d'in kusa da nawa ita zata fad'a miki site d'in da zaki rik'a morpping d'in". Hassana fita ta yi daga Office d'in manager ta shiga office d'in ku sa da na shi.
KyKkyawar budurwa ce, a ganinda nai mata baza ta wuce twenty five years ba. Zaune ta ke tana ta aikin dan na laptop d'in da ke gabanta. Hassana cikin girmamawa ta ce, "Barka da aiki Aunty". Da sauri Billy ta d'ago tana kallan Hassana jin sunan da ta kirata da shi. Cikin b'acin rai Billy ta ce, dan ita jin kanta ta ke kamar wata 'yar seventeen years. Hakan yasa cikin d'aga murya Billy ta ce, "Uwar ki ce Aunty ".dan ita aganinta Hassana kallan girma tai mata shiyasa ta kirata da Aunty.
Ita ko Hassana girmamata ta yi.
Hassana cikin girmawa ta ce, "Yi hak'uri dan Allah, ban sanda sunan da zan kiraki da shi bane, shiyasa". Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "me ki ki so? ". "Ni sabuwar ma aikaciyarku ce, Oga manager ne ya d'aukan aiki zan rik'a shara da goge-goge, shine Manager ya ce inzo Office d'in ki, ke ce zaki fad'amin b'angaran da zan rik'a sharewa da gogewa".Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ai muna da 'yan mopping da yawa, amma inda ya riga ya d'auke ki, ki rik'a mopping d'in site d'in da engine su ke, amma fa dole zaki rik'a zuwa da wuri". Hassana kallan ta ta yi, ta ce, "Aunty ai bansan site d'in ba". "Ki samu wata staff d'in ki tambayeta zata nuna miki". Hassana godiya ta yi mata ta juya zata tafi.Hassana ta na fitowa daga Office d'in supervisor ta had'u da wani staff da suka had'u jiya. Cikin zakin fuska da washema Hassana baki, yak'araso inda Hassana ta ke. Kallan Hassana ya yi, ya ce, " 'Yan mata ina fatan dai kin samu aiki". Hassana cikin sakin fuska itama ta bashi amsa, ta ce, "Eh Wallahi na samu". "Kai amma nai miki murna, kina cikin masu programme d'in sanat yoghurt ko? ". Hassana kai ta girgiza mai ta ce, "Ni aikina sharane da goge- goge". "Ok, karki damu wata rana zaki zamama d'aya daga cikinmu, wasinmu duk daga haka suka fara, kin san dai aikin Company sai nada hak'uri, dan haka ki yi hak'uri ba kamar da supervisor d'in mu ba".Hassana kallan shi ta yi, ta ce, "Dan Allah inane site d'in ku d'in can ne b'angaran da ta ban aikin". Staff d'in nan da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "Kai, kin sanfa da yake batada hankali taba masu sharar gun suspension, gaskiya gun ya yi miki yawa ke kad'ai. Amma kinga yanzu ke new worker ce be kamata ki fara kai complain tun yanzu ba, amma daga kin yi one week ina yi bata dawo da wa inda ta ba suspension ba, tom ki kai ma manager complain akan haka". Hassana godiya ta yi, mai sannan suka jera ya je ya nuna mata inda zata rik'a sharewa da gogewa, duk Hassana ta saba aikin wahala agida amma tasan wannan gun yafi k'arfin sharar mutum d'aya. Hakan yasa Hassana ta kalli staff d'in da ya rakora gun ta ce, mai"gaskiya gunnan ya yi min girma, bazan iya shareshi da goge shi ba ni kad'ai ba". Kallan Hassana wannan staff d'in ya yi sannan ya ce, "Gaskiya sai dai ki yi hak'urin kwana ko biyu ne tukun nan, dan kinga wa inda ta dakatarma jiya su biyu daga sun mata magana akan tak'aro masu wasu gun ya yi masu yawa su kad'ai, shikenan wai su je gida su huta na wata biyu sai su dawo, Kin san manager gun nan sonta ya ke shiyasa ta ke abinda taga dama, ita kuma hankalinta nakan Oga Habib". Hassana shiru kawai ta yi, amma tasan zata sha wahala ace aikin da wasu sukeyi su biyu suka kasa abata shi ita kad'ai.staff d'in nan kallan Hassana ya yi, ya ce, "Tom ni dai Sunana kabiru, amma mutane na kidana da barber for ladies,ki fa ya sunan ki? ". murmushi Hassana ta yi mai sannan ta ce, "Sunana Hassana". kabiru kallan Hassana ya yi, ya ce, "kai amma gaskiya kinada suna mai dad'i , bari in je in yi abinda zanyi, sai anjima in munhad'u". Kabiru ta fiya ya yi yabar Hassana gun tsaye tana kallan yadda ma aikatan ke ta aikin d'ura yughurt d'in da akai cikin robobi. Hassana na nan tsaye tana kallan aiki ga wani irin k'amshin swtrovery da ke tashi agun. Hassana na nan tsaye ta ji, andafa ta. Da sauri Hassana ta waigo tana kallan wadda ta da fata.matashiyar budurwar ce, zasu iya zama sa'a da Hassana, kallan Hassana ta yi, ta ce, "Amma dai ke new worker ce anan ko? ". Kai Hassana ta d'aga mata. "Ai dama tunda naga kina sauraran kabiru na san ke sabuwar ma'aikaciya ce nan, abinda zan fad'amiki ki rabu da Kabiru dan daga ganinki kina da mutunci da kamun kai, kabiru ko d'an iskan mai rai ne, biki ji sunan shi ba, barber for ladies,sannan idan supervisor tazo ta ganki tsaye ahaka, zaki samu matsala. B'angaran me ye aka d'auke ki". Hassana kallanta ta yi, ta ce, "shara da goge- goge". "Tom kinga ga rack can d'akko shi zaki yi, duk abinda ya zube kina gogewa, ki tafa bata yadda ta ganka a tsaye ba". Hassana godiya ta yi mata, sannan ta zo gusa da su, da morpper d'inta duk abinda ya zube tana gogewa. Kafin lokacin tashi ya yi Hassana ta share duk inda ya ke ak'ark'ashin ai kinta. K'arfe 8:00pm Hassana ta fito domin ta fiya gida, sai a lokacin Hassana ta tuna bata da ko sisi, gashi tun d'azu taga fitar manager bare ta fad'a mai inda taga alamar yana da kirki sosai. Hassana wajan parking space ta shiga tana zuwa ta motar Oga Habib agun, azuciyar ta tace bai tafiba kenan, Ya Allah banda yadda zan yi kuma bazan gane gidan ba, Allah ka bashi ikon d'aukata. Hassana guri ta samu ta zauna tana tunanin yadda zata iya yima Oga Habib magana ya d'auketa. Wata zuciyar ta ce, kai Wallahi bazan iya ba, dan ko nayi ma ba d'aukata zai yi ba, wata zuciyar ta ce mata, tom idan baki mai magana ba, ai kin kwana a titi. Hassana na zaune tana wannan tunanin ga tunwa duk ta da meta, tun tea d'in da Jimmai ta bata da safe tasha har yanzu shi kad'ai ne a cikinta, d'azu tana gani staff d'in gunna fita cin abinci amma ita bata da kud'i sai dai ta hakura. Hassana na nan zaune, ta ga fitowar Oga Habib, yana zuwa ya fad'a motar shi. Hassana da sauri ta tashi ta nufi gun motar Oga Habib...............

TOFA IDAN OGA HABIB BAI D'AUKI HASSANA BA, YA ZATA YI????? 🙆‍♀️🙆‍♀️
Chapter 11 · 0% Book details