← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 78

Sashe 6

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..... Bilya wacece wannan?, Habib ya yi maganar ba alamun fara'a a fuskar shi. Bilya cikin girmamawa ya fara magana, kamar haka, "Oga Habib ita ce Yarinyar da muka tsinta, kace in d'akko ta ranar da muka je kano". Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya, sannan ya ce,cikin fad'a-fad'a " da nace ka d'akkota sai kuma nace ka kaita gidana!? ". Bilya cikin alamun ban hak'uri, ya ce, "ka yi hak'uri Oga Habib, na aikata kuskure, insha Allah haka bazai sake faruwa ba". Habib banza ya yi da Bilya yaci gaba da typing d'in sakon da ya ke yi, a laptop d'in da ke gaban shi. Habib sai da yagama abinda yake yi, duk su Bilya na tsaye suna jiran sakamakonsu. Sannan ya d'ago kai ya kalli Bilya ya ce, "Bilya daga nan karku koma min gida ku dukanku". Bilya cikin tsorata da jin kalaman Oga Habib, duk da dai yasan zai iya ai kata hakan,Bilya ya ce, "Oga Habib dan Allah k........ ". Habib hannu ya d'agama Bilya, sannan ya nuna masu k'ofar fita". Baba Lami da sauri ta k'araso in da Habib ya ke, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri munsa.... ". Habib ranshi a d'an b'ace ya nuna ma Baba lami k'ofa ya ce, "Baba dan Allah ku fitarmin Office! ". Baba lami fita tayi tana mai da nasanin amincema Bilya da ta yi ta amshi Hassana, gashi abin ja mata kurarta aiki. Bilya ya je dai-dai k'ofar fita ya tsaya, cikin taushin murya raunanna, ya ce,"Ka yi hak'uri Oga Habib da abinda zan ce maka. Oga Habib amma da kasan bazaka taimaki yarinyar ba, da baka sani na d'akkota ba, Oga Habib sanin kankane bani da gida, ni ba d'an garinnan ba ne, yanzu da kakoreni ina ita zan kaita?, da ace mun barta a'inda muka ganta da Allah zai kawo wanda zai tai maketa, amma mu tai makon da mu kai mata ya zamana bashida amfani. Oga Habib ita fa mace ce,Idan munbarta tatafi ina zata?, Oga Habib dan Allah ina rok'onka dan Allah idan ka koreni tom ita dan Allah ka yi k'ok'ari ka ci ka aikin alkairin da ka yi niyyaryi tun farko akanta. Inda dama kai kayi niyyar taima kon....". Habib katse Bilya ya yi, alamun ranshi ya fara b'aci da magan-ganun Bilya. Ba kamar maganar shi ta k'arshe ba, wai dama shi ya yi niyyar taimakon ta bashi ba. Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya sannan ya ce, d'an zafafe, "Bilya ni na ce maka zan taimaketa?, dama da nace ma ka ka d'auketa sai aka cema hakan na nufin agidana zata zauna kenan!? ". Habib ya tambayi Bilya cikin d'aga murya. Bilya shima da yake sosai Habib ya b'ata mai rai, cikin k'ok'arin danne fushinshi, dan yasan in dai ya ce zai sa fushi tom Habib ba zai ya yi abinda ya ke so ba, gara ya yi hak'uri ya danne fushinshi. Hakan yasa Bilya cikin danne fushinshi ya ce, " Oga Habib hak'uri za kai ka tai maka mata, dan na tambayi yarinyar garinsu in kaita, ta ce min ita marainiya ce, shine ma dalilin da yasa nakaita gidanka". Habib cikin had'e rai ya ce, "Sai aka cema kuma shi maraya bashi da 'yan'uwa, kira min yarinyar". Bilya fita ya yi, ya iske Baba Lami da Hassana tsaye. Baba Lami kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya ya hak'ura ne? ". "Hmmm Baba wannan ne zai hak'ura da wuri haka bai wahalar da mutane ba. Ni Baba Lami dama abinda ke damuna wannan yarinyar ya nuna Hassana da ke tsaye, kuma shine yasa ni taimakonta, shine na ke son yasan yadda zai yi da ita inda shi ya yi niyyar tai makon dama bani ba, shine yanzu da nai mai complain akanta, shine ya ce in kira mai ita". Baba lami kallan Hassana ta yi, ta ce, "Je ki kinji Allah ya tai make ki, yabarki. Baba lami mai da kallanta ta yi ga Bilya ta ce, " Bilya mufa? ". "Baba Lami ki rabu da shi kinji, ni na san yadda zan mai, Hajiya turai ta yarda da ni sosai, kuma kinga kema ta yarda da ke, shiyasa ta zab'eki da ki rik'a yi ma Oga Habib girki, dan haka ki bari kawai nasan yadda zanyi, Allah dai yasa in nakirata ta d'aga". Ameen Baba Lami ta ce. Bilya kallan Hassana ya yi da har yanzu ta ke tsaye ta k'i tafiya, ya ce, "Je ki Office d'in ce inda muka fito yanzu". Hassana ko da bata fatan k'ara ganin Habib, kallan Bilya ta yi, ta ce, "Dan Allah ni dai kutai dani inda zaku, ni bana son zuwa dan Allah ". Bilya dariya ya yi, dan yaga alamar ta tsorata da Habib sosai. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "kinga ni yanzu haka nasan ni da Baba zai mai da mu, saboda Mahaifiyar shi tana son mu, da ma ke nake ji, inda bazasu yarda ba ki zauna agidansu, dan yanzu suna tsoran bak'o saboda abinda ya faru da su kwanakin baya, ki yi hak'uri ki je, idan Allah ya taimaka, duk da Oga Habib shegen mutum ne, k'ila ya barki". Hassana a tsorace ta tura Office d'in Habib ta shiga, dan ita bata son wulak'anci kuma ta lura OgaHabib irin masu wula k'anta mutanan nan ne, saboda kud'insu. Habib na zaune yana mai cigaba da typing d'in da ya ke a laptop d'in shi, kayan da za'a kawo masu ne ya ke ta aikin lissafawa. Habib na zaune ya ji anturo k'ofa anshigo ba naiman izini ba komai. Habib d'ago kai ya yi yana mata kallan baki da hankali ne, Banza Habib ya yi da ita, ya ci gaba da typing d'in shi ya barta nan tsaye. Hassana ko magana ta ke son yi tana tsoro dan taga Bilya ma yana mai fad'a bare ita. Hassana jin ya yi banza da ita babu alamunma zai gama abinda ya ke yi bare har ya yi mata magana. Hakan yasa ta ce,cikin rawar murya, kamar yadda ta lura kowa na cewa, "Oga Habib dama Oga Bilya ne ya ce min kana kirana". Habib ko cigaba da aikin da ya ke yi ya yi kamar bai jita ba, bamu ma wata ala da ta nuna mata yaji abinda ta ce, hakan yasa ta kuma cewa, "Oga Habib dama Oga bilya ne ya ce min inzo kana son gani n...... ". Tsawar da Habib ya yi mata ce yasa ta yi shiru, cikin d'aga murya Habib ya nuna ta da d'an ya tsa, ya ce, "get out from my Office ". Hassana fita ta yi jikinta na rawa, dan sosai ta tsorata da tsawar da Habib ya yi mata. Hassana inda tabar Baba lami da Bilya ta je, amma bata gansu ba. Hassana guri ta samu ta zauna ta yi shiru kamar za tai kuka, tabbas tun yanzu da ba aje ko ina ba, ta fara da na sanin barin gida. Hassana na nan zaune tana kallan ma'aikan gurin kala-kala sai aikinsu suke, can wani d'aya daga cikin staff d'in gurin wanda tun d'azu ya lura da Lokacinda Hassana ta fito daga Office d'in Oga Habib. Inda Hassana ta ke tsugunne ya zo ya sameta, kallan Hassana ya yi, ya ce, "Bai war Allah lafiya kuwa? Nalura da ke tun d'azu keke gurinnan. Idan aiki kika zo naima aiba Office d'in Oga zaki ba, gurin manager zaki". Hassana d'aga kai ta yi tana kallan shi, sannan ta ce, "Ni ba aiki nazo naima ba, amma inna samu aikinma zan yi". "Ok, amma dan Allah ko zan iya sanin mekika zo naima, in ba aiki ba? ". Hassana kallan shi ta yi, sai taji bata da zab'i kamar ta fad'a mai, inda taimo ta ke naima k'ila ya tai maketa. Hakan yasa Hassana ta kallai, ta ce, "Bansan kowa ba a nan Abuja, su Oganku suka tsinceni ahanyarsu ta tafiya kano,suka kawo ni nan, shine yanzu shi Wanda ake kira da Oga Habib, wai bazan zauna agidan shiba, shine shi Oga Bilya ya ce in je Office d'in shi ya na kirana, tom na je kuma ya Koreni". murmushi ya yi, staff d'in nan, ya ce, "Bilya ai ba wani bane staff ne kamar kowa anan, dan dai shi yana driving d'in Oga Habib ne, kuma in dai Oga Habib ne ya ce yana kiranki a Office d'in shi zai saurareki, sai dai in da kika je ne, kin mai ba dai-dai bane. Kuma maganar gaskiya in ma komawa kikayi ki mai magana kan ya d'aukeki aiki, amma maganar gaskiya Oga Habib ba zai kaiki gidan shiba, dan gidansu akwai tsaro sosai. Idan harshi ya ce kije, ki tashi ki koma ki je zai saurareki, in da yasan da zuwanki". Hassana tashi ta yi ta nufi office d'in Oga Habib, saboda bata da zab'in da ya wuce ta tashi ta je d'in. Staff d'in nan kallan Hassana ya yi da tausayawa, dan mata masu ajima Oga Habib ba saurararsu ya ke ba bare ita. Habib na zaune yana waya da Mommynshi, Hassana ta yi sallama ta shigo. Habib kallo d'aya ya yi mata ya d'auke kanshi ya ci gaba da wayar shi. Jinai Habib na cewa, "Mommyna dan Allah ki barsu kawai, idan mutum na laifi irin haka ya kamata ai funishiment d'insa. Banajin abinda akecewa daga can b'angaran, sai dai naji Habib ya ce, "Ok, Mommy zasu dawo, amma ni idan tanine ma nafi son inyi driving d'in kaina. Abinci kuma ki rabu da Baba Lami inda ga Baba dije nan". Mahaifiyar Habib sosai ta nuna ma Habib in dai bai dawo da su bilya ba ranshi zai b'ace. Tana kaiwa nan ta kashe wayarta. Habib ranshi b'ace ya kira bilya awaya, kira d'aya bilya ya d'aga, yana d'agawa Habib ya ce, "Bilya kazo Office d'ina yanzu". Habib mai da kallan shi ya yi ga, Hassana da ke gefa tsaye arakub'e. Doguwar rigar da Likitarnan ta bata ce har yanzu ajikinta, sai wani haif hijab da tasa. Habib d'auke kai ya yi daga kallanta, sannan bazato ba tsammani Hassana ta ji ya ce, "Ke 'yar wata jaha ce?,kuma me yarabo da ke daga gidan ku? ". Hassana kallan Habib ta yi taga
Chapter 6 · 0% Book details