← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 78

Sashe 53

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan su Habu sun tafi, Farida ta kalli Mahaifiyarta ta ce, "Mommy kin kawo shawara mai kyau, dama tuntuni haka mukai da yanzu mun huta". Dariya Hajiya Murja ta yi, ta ce, "ai shiyasa na zab'i su Habu, nasan sun iya aiki babu kuskure, kuma suna da asiri basa kamuwa".

Yau Habib da wuri ya dawo aiki, saboda yana son zuwa gaida Maifiyar shi. Hassana na falo zaune ita kad'ai, sai T,V, da keta aiki , Hasssana najin dawowar Habib, ta ji kamar ta tashi ta shige bedroom d'in ta , sai kuma ta hak'ura ta tsaya, saboda sun rabu da gaisawa, tasan yanzu k'ila yama manta da ita".

Hassana na wannan tunanin Habib ya shigo. Hassana cikin sanyin murya ta ce, "Barka da dawowa Oga Habib ". Habib kallan Hassana ya yi ya wuce ci ki, dan ko motsinta baya ji, hakan yasa yama manta su biyu suke rayuwa agidan".

Habib cikin sauri ya shirya ya nufi gidan Hajiya Turai. Habib a bedroom ya iske Hajiya Turai zaune kan abin Sallah ta Idar da sallar issha'i. Habib koda ya gaida Hajiya Turai hararar shi ta yi, ta ce, "Ina daughter fa? , bayan nace ma kazo da ita muyi sallama gobe zan wuce da safe" "Ba daga gida nake ba". Cewar Habib".

Hajiya Turai, wata leda ta mik'ama Habib ta ce, "Gashi dama ita bake son gani, yanzu ai sai ka kai mata, Habib dan Allah ka yi hak'uri ku zauna lafiya da daughter,Ni dai nasan daughter bata da damuwa, amma kai ka d'auki girman kai ka d'ora ma kanka".

Haka Hajiya Turai ta dad'e tana ma Habib nasiha, daga k'arshe ya d'auki ledar da taba shi ta ce ya kaima Hassana , Habib ta fiya ya yi tare da yima Mahaifiyar shi fatan sauka lafiya, inda tace gobe da wuri zata wuce".

Habib bashi ya dawo ba, sai 9:15PM lokacin Hassana ta yi nisa a bacci. Habib aje ledar da Hajiya Turai ta bashi ya yi a falon ya shiga bedroom d'in shi, ya kwanta dan yajiya sosai ya ke ji".

Hassana ko ta dad'e ba tai bacci ba, dan haka nan yau sai Allah ya jarabceta da tsoro, hakan yasa har sai da taji alamun dawowar Habib bacci ya kwasheta".

1:00AM, k'arar Harbin bindiga ya tada Hassana daga bacci. Su Habib sai da su kai harbi Uku sannan suka fara buga k'ofar falon Habib ".

Habib cikin tsoro ya farka ya fito. Hassana ko jikinta na rawa ta fito itama daga bedroom d'in ta. Habib ta gani tsaye yana lek'awa ta wata 'yar hududa".

Su Habu wata bingidar su ka kuma k'ara harbawa. Hassana ta fasa k'ara da k'arfi jikinta na rawa, tazo ta rik'e Habib.".

Habib ko hannu yasa ya rufe ma Hassana baki, a kunnanta ya yi mata magana, ya ce, "Ke da Allah can ki yi shiru, in ba haka ba zan bud'e k'ofar in wurgaki".

Hassana najin haka ta yi, shiru tana mai k'ara rik'e Habib".

Habib kuma so yake ya d'akko wayarshi da yabari a bedroom d'in shi, ya kira akawo masu d'auki amma Hassana ta cikwikwiye shi, ta hanashi ta fiya. Hakan yasa Habib cikin fad'a-fad'a ya ce, " Ke mahaukaciyar wana gari ce, bazaki sake ni ba in d'akko waya ta? ". "Wayyo Oga Habib muje kad'akko dan Allah, Wayyo Allah zasu shigo".

Su Habu ko wani k'arfe su kasa ji kake k'ofar ta ce, k'asssss. Hassana jin k'ofar ta b'alle wani ihu ta fasa, sannan ta .................. ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝

Comment
&
Please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Shafi na 64&65.

Su Habu ko wani k'arfe su ka sa, ji kake k'ofar ta ce, k'asssss.. Hassana jin k'ofar ta b'alle wani ihu ta fasa, sannan ta bi Habib da gudu bedroom d'in shi, tana cewa, "Wayyo Oga Habib gasu nan, sun shigo sun b'alla k'ofar". Habib ko da ke tsaye yana kiran commissioner 'yan sanda akawo masu d'auki. Hassana jin Habib ya yi banza da ita, yana tsaye ya gama wayar da tsabar rud'ewa bata ji me yake cewa ba".

Wani bugu su Habu suka kuma yima k'ofar". Hassana sosai ta rirrik'e Habib tana cewa, "Wallahi sun shigo dan Allah ka b'oye ni! ". Habib tsawa ya yi ma Hassana, dan shima kusan arud'e ya ke gashi har yanzu baiga wani alamun za'a kawo masu d'auki ba. Turai Hassana ya yi daga jikin shi, ya ce, "Idan kika sake rik'eni zakiga abinda zan miki, inda ance miki zasu iya b'alla k'ofar nan ne".

Su Habu ko kamar sunji abinda Habib ya ce, suka ce, "Wallahi idan har baku bud'e k'ofar nan ba, muka b'alleta muka shigo duk sai mun kasheku, amma yanzu idan kuka b'ode abu kawai zamu amsa mu wuce salin'-alin". Hassana kuka ta fasa tana kamo hannun Habib ta ce, "Dan Allah Oga Habib muje ka bud'e musu,kaji abinda suka ce ko?, Ni dai ka bud'e musu ". Habib ganin tabbas zasu iya b'alla k'ofar yadda suke bugunta, dan ga k'ofar nan sai wani k'ara take, na alamun ankusa cinnasara da k'ok'arin bud'eta d'in da ake. Hakan yasa Habib ya je ya bud'e k'ofar, Hassana kuma na bedroom d'in shi duk ta rud'e ".

Habib na bud'e k'ofar d'aya daga cikinsu ya d'orama Habib bindiga akai, yana nuna mai photo'n Hassana, ya ce, "Ina wannan yarinyar ta ke? ". Habib shiru ya yi bai yi magana ba. Wanda ya d'ora bindiga kan Habib ya ce, "Kai zaka yi magana koko saina bugama bindigar nan". Habib cikin jarumta ya ce, "Abu kuka ce zaku amsa ku wuce,dan haka ku fad'a min me kuke so? , ko meye zan baku".kusan atare suka tun tsire da dariya, sannan wanda ya d'ora mai bindigar ya ce, "kai allaji baka ganewa, ai ita ce abun da muke nufi, amma kaci sa'a bacin ance karmu tab'aka da yanzu kaji jiki". Babban cikin nasu, wanda ya ke kamar shine ogansu, kallan su ya yi, ya ce, "ku bincukota duk inda ta ke, nasan tana cikin gidan nan ".

Tashin farko bedroom d'in Habib suka Shiga. Allah sarki tsaye suka iske Hassana ko ina najikinta rawa yake, aiko suna zuwa suka tasa k'eyarta suka ce"Muje ". Hassana ihu ta kama tana rok'ansu tana cewa, "Dan Allah ku yi hak'uri, dan Allah ina rok'anku..... ". Haka Hassana tai ta kuka tana rok'insu su rabu da ita, amma ko sauraranta basu yiba".

Suna zuwa dai-dai saitin Habib Hassana ta rik'o hannun Habib tana kuka, tana cewa, "Wayyo Allah Oga Habib dan Allah karka bari su tafi dani... ". Habib kallan Hassana kawai ya yi, yarasa bakin magana, idan ma zai yi maganar bai san me zai ce ba".

D'aya daga cikinsu ko tun kud'a Hassana ya yi da k'arfi wanda yasa ta saki hannun Habib bata shirya ba. Habib na tsaye yana kallan su haka suka fita da Hassana tana ihu tana kiran sunan shi".

Habib cikin tashin hankali ya ciro waya ya kuma kiran commissioner of police, amma bai d'aga ba, haka Habib ya yi ta kiran shi shi kuma yak'i d'agawa. Can Habib ya ji tashin bindiga kota ina. Habib bud'e k'ofar ya yi ya fito, ji ya yi an fisgo hannun shi. Cikin tsoro Habib ya ke kallan wanda ke rik'e da hannun shi. K'asa-k'asa wanda ya rik'e hannun Habib d'in ya ce, "Ranka shidad'e karka damu, ma'aikatanmu duk suna nan, tun da kakira ai muka zo, yanzu haka anbisu,ka yi hak'uri ka koma ciki insha Allah babu abinda zasu yi mata". D'an sanda kama hannun Habib ya yi ya maida shi har falon shi, sannan yaja mai k'ofar, ya fita".

Haka Habib ya zauna yana mai jiran tsammanin ganin andawo da Hassana amma shiru. Wayar shi ya d'auka ya kuma kiran commissioner amma bai d'auka ba. Habib ya'aje wayar kamar da minti biyar kira ya shigo wayar shi, d'agawa ya yi, yana d'auka akace ranka shidad'e Allah ya bamu sa'ar amsar yarinyar, amma bamu kama ko d'aya daga cikinsu ba". "Ok, ina yarinyar... ". Bai idasa fad'in abinda ya ke son fad'a ba, Hassana ta fad'o falon a rikice tana kuka. Tana zuwa ta fad'a kan Habib jikinta ko ina rawa ya ke, dan har yanzu ba wai ta dawo natsuwarta bane".

Daga can b'angaran D'an sanda ya ce, "Yauwa kamar ita ce ta shigo ko? ". Jin kukan Hassana da ya yi".

Habib da "Eh ". ya amsa mai, sannan ya ce, "Zamuyi magana gobe, saboda baya jin shi sosai saboda kukan Hassana".

Habib kallan Hassana ya yi dake rik'e da shi ga jikinta ko ina har yanzu rawa ya ke, Habib d'ago Hassana ya yi, yana kallanta, karo na farko kenan da Habib ya tab'a kallan Hassana haka. Girgizata ya yi sannan ya ce, "Ke kinatsu mana, sun wuce, ki tashi ki je ki watsa ruwa zaki ji sanyi". Habib ya fad'i maganar yana mai tashi da Hassana".

Habib daga ya saki Hassana sai ta tafi zata fad'i, Habib cikin fad'a-fad'a ya ce, "Wallahi ki mik'e ko in sake ki ki fad'i". Hassana cikin narkarkar murya ta ce, "Wayyo tom ni ka kaini bedroom d'ina". Habib tsaki ya yi sannan ya rik'e Hassana ya kaita bedroom d'in ta. Habib juyawa ya yi zai fita, Hassana ta yi saurin kamo hannun shi, kamar za tai kuka, ta ce, "Ayyah nifa tsoro nake ji". Habib tsawa ta yi ma Hassana,ya ce, "Tsoran ya kashe ki, dama nasani bari nayi suka tafi da ke kowama ya huta". Habib na fad'in haka yaja k'ofar Hassana ya fita".

Hassana guri d'aya ta dun k'ule tana kuka dan tsoro ta ke ji sosai, gani take kamar zasu dawo, ahaka dai wani wahalallan bacci ya d'auke ta".

B'angaran Habib ko koda ya kwanta tunane-tunane ya hana shi bacci, dan sosai abin da ya faru ya d'aurai mai kai, yana mamakin wanda ya aiko atafi da Hassana, dan daga ganin abin sasu akayi, ahaka dai bacci ya kwashe Habib ".
Chapter 53 · 0% Book details