← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 78

Sashe 74

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habib ko gudin kar Hajiyarsa ta sake kira kashe wayar shi ya yi, acewar shi gobe ya mai da mata Hassanar. Habib kwanciya ya yi yana tunanin yadda zai yi da Mahaifiyar Farida, Hassana ko bayan ta gama shafarta da d'an k'aramin towel d'in da ke jikinta ta nufo wajan Habib, dan Hassana ta kan manta sabon da su kai da Habib kafin ya samu lafiya ne. Habib na kwance Hassana ta zo ta kwanta gefan shi. Habib juyo wa ya yi yana kallan Hassana, Habib jawo Hassana ya yi kusa da shi ya ce, "Mommy na nai manki, gashi ni kuma ba zan iya komawa yan zu ba sai dai gobe"."A'a ni dai ka tashi ka kai ni yan zu". Habib kuma jan Hassana ya yi ya ce kwanta mu yi bacci da sassafe zan kai ki".

Hassana da dama bacci ta ke ji tana kwanciya bacci ya kwasheta, Habib kuma ga ba d'aya ya kasa bacci, d'an k'aramin lips d'in Hassana ya k'ura ma ido, can dai ya kama lips d'in yana kissing. Hassana cikin bacci taji an rik'e bakin ta. Ta shi ta yi da sauri zata zauna, Habib ya yi saurin rik'ota ya ce, "Sanat please ki yarda yau mu zama d'aya mana ". Hassana ciku-cikun kwace kanta ta ke, amma ina abun ya ci tura".

Atak'aice
acikin daran Habib ya mai da Hassana ci kakar mace".

Asubar fari Habib ya tashi ya watsa ruwa, ya yi alwallah ya yi sallah, yana nan zau ne har aka kira Sallah, sai da gari ya yi haske sannan Habib ya tada Hassana, da kan shi ya tai maka mata ta kin tsa kanta".

Hassana na yin Sallah ta koma ta kwanta in da Habib ma ya kwanta rungume da Hassana suka koma wani baccin".

Kiran wayar Habib ce ta sa Habib ya tashi, Habib na d'agawa Hajiya Murja ta ce, "Habib kazo yan zu dan Allah ". Hajiya Murja ta fad'i maganar tana kuka". Habib ta shi ya yi ya shirya yana cikin shirin Hassana ta tashi tana son yi ma Habib magana ta kasa, dan ta ji wayar da ya yi da Hajiya Murja. Hassana ta shi ta yi ta nufi side d'in ta, tana zuwa da sauri ta shirya ta zauna Falo tana jiran Habib".

Habib zau ne ya iske Hassana a falo, Hassana ta shi ta yi ta rik'e hannun Habib tana mai kauda idonta, da kallan shi, dan sosai ta ji tana jin nau yin had'a ido da Habib d'in".

Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "Sanat zaki bi ni ne? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib". Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida...... ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment Sister 🤝

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa👌👌.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa 👌👌

VIP group 300 Only👌 , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number👉 08063830828

Shafi na 90&91.

Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat za ki bi ni ne? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib. Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida".

Habib na rik'e da hannun Hassana su shiga d'akin da aka kwantar da Farida. Lokacin Hajiya Turai bata nan ta ta fi kiran likita ya duba Farida ganin yadda ta ke ta aman jini, Habib da Hassana da sauri suka k'arasa in da Farida ta ke. Habib cikin tausayin Farida ya ce, "Sannu Farida". Farida ko da ta ji Muryar Habib kamar a mafarki, cikin rauni irin na marasa lafiya Farida ta rik'a lalibar Habib. Hassana ganin haka da sauri ta rik'o hannun Farida. Farida ko a tunaninta Habib ne ya rik'e ma ta hannu".

Farida cikin dauriya da jarumta ta fara magana kamar haka, "Oga Habib ko da Mommy'na ta ce min zaka auran ban yarda ba, duk da ka fad'a aga bana, tabbas kai d'in raban Hassana ce, Hassana ta kasan ce mai sa'a arayuwa, Oga Habib ina ji ajikina mutuwa zan yi sonka shi zai zama sanadin ajalina, zan sanar da kai abin da baka sani ba ayau. Oga Habib ni ce nai silar auran ka da Hassana, na yi abubuwa da dama dan ganin ka zama miji agareni, amma ina abin bai yuwu ba". Farida shiru ta yi sabo da yadda taji numfashinta na fusgar mata, Farida sai da ta share wasu hawaye masu d'imi da ke zubar mata, sannan ta dafe gefan zuciyarta ta ci gaba da magana cikin kuka-kuka kamar haka, "Oga Habib ni ce sanadin haukarka, na yi haka ne ko zaka zama miji a wajena, amma da ya ke kai d'in ba rabo na bane, sai abin ya fad'a ma Hassana, mai makon karik'a yaddar da ni ni ka d'ai kamar yadda naso, sai ya zama mana da Hassana ka d'ai ka ke yadda,
Inda tunanina ya bani, idan ya kasan ce dani ka d'ai ka ke yarda na san kowa zai yi tunanin had'a ni aure da kai, tom abin sai ya fad'a akan Hassana". Nan ma Farida shiru ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Oga Habib duk da Mommy ta had'a auranka da Hassana ban yi hak'uri ba nayi abubuwa da yawa ganin na raba auranka da Hassana, shima bai yuwu ba, na tura b'arayi akan su d'auke Hassana shima bai yuwu ba. Shi ne nayi tunanin fara aiki a Sanat ko zan ja hankalinka".kukan da ya k'wace ma Farida ne ya sa tai shiru, sai da tai kukanta ta gama sannan, ta ci gaba da cewa, nayi k'ok'ari sosai ganin na ta kurama Hassana".

Farida kuma rik'e hannun Hassana ta yi d'ayan kuma ta dafe saitin zuciyar ta, da ta ke tunanin hannun Habib ne ta ci gaba da cewa, " Oga Habib kai da Hassana ku yafe min dan.....". Tarin da Farida ke yi ne, mai tattare da aman jini ya hana ta fad'in abin da ta ke so".

Allah sarki Hassana da tausan Farida ya kamata kuka ta kama, dai-dai lokacin kuma Hajiya Murja ta shigo da likita".

Wata doguwar Hajiyar zuciya Farida ta ja, daga nan tarin ya lafa. Likitan duba Farida ya yi, sannan ya kalli Hajiya Murja ya ce, "Hajiya Allah ya yi ma mata rasuwa!? Ihu d'aya Hajiya Murja ta yi ta yanke jiki ta fad'i".

Ita kanta Hassana kuka ta fasa,cikin rud'ewa ta ke "Innalilahi'wa inna ilaihirraju'un! ". Habib rasa yadda zai yi da Hassana ya yi, ganin ta rud'e da yawa, ga kuma Hajiya Murja a sume".

Habib waya ya ciro ya kira Hajiya Turai, tana d'agawa Habib ya sanar da ita mutuwar Farida yan zu haka suna asibitin. Ai Hajiya Turai bata gama saurara ba ta kashe wayar".

Cikin minti goma Hajiya Turai ta iso asibitin, tana zuwa lokacin kuma dai-dai za atai da gawar Farida gida, haka aka tafi da gawar Farida gida, da Hajiya Murja keta rusa kuka tana kiran ta bani ta shiga uku, wa'iyazubiiya, Innalmaiyata layu'azibi bibika'ilhai, lallai mamaci ina masa azaba da kukan Wanda ya ke da rai. Allah ka ki ya ye mu kasa mu dace".

Haka akai zana'idar Farida aka kaita gidan ta na gaskiya. Sai da aka gama komai sannan Habib ya d'auki Hajiya Turai da Hassana suka koma gidan Hajiya Turai ".

Hassana da zazzab'i ke damunta tun acan daurewa ka wai ta ke, suna zuwa ta kwanta kan Three seater Falon Hajiya Turai, Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy Sanat fa bata ci komai ba".Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter me zaki ci? "."Mommy tea ". Hajiya Turai Maimuna tasa ta had'ama Hassana tea ta kawo mata. Habib buga k'afar Hassana ya yi kad'an ya ce, "Tashi ki sha tea d'in ". Hassana tashi tai dama kuma yunwa ta ke ji, dan ma d'azu Habib ya kaita wani restaurant ta ci abinci. Hassana amsar tea d'in ta yi ahankaki-ahankali ta samu ta shanye tea d'in".
Chapter 74 · 0% Book details