Sashe 4
Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
kash abinda Baba bata sani ba, aminiyarta wadda su ke aiki tare da ita da kanta ta kira Hajiya turai ta kai gulmar Lami ta kawo wata bak'uwar yarinya agidan, kuma abisa lurar da ta yi, Bilya ne zazo da Yarinyar ya ba Baba Lami ita". Hajiya turai ko, sosai hakan yab'ata mata rai, acewar ta ba laifin Bilya ba ne, lafin Oga Habib ne, saboda shi ya ba Bilya damar shigowa kai tsaye gidan. Hajiya turai ranta ad'an b'ace takira Habib awaya. Habib ko lokacin yana zaune a office d'in shi na SANAT YOGHURT, kiran Mahaifiyar shi abin soyuwa a zuciyar, ya shigo wayar shi Habib cikin kirarin da ya saba yi ma Mommy shi, ya d'aga kiran ya ce, "Sai Mommyna ni kad'ai Allah ya k'arami lafiya, lafiya dai ko wannan kira haka a wannan lokacin? ". Hajiya turai cikin basar da zancen Habib d'in ta ce, "Habib wacece ta ke zaune a gida". Habib cikin rashin fahimtar abinda Mahaifiyarta shi ta ce,ya ce, "Mommyna bangane maganarki ba". "Habib za kai min maganarta ka ko ta banza, tom wacece aka ce min Bilya ya kawo gidan da zama?, Habib ni fa ina tsoran abinda ya faru ne ya sake faruwa". Habib cikin kwantar ma Mahaifiyar shi hankali, dan yaga alamar ta tsorata sosai da abinda ya faru Kwanakin baya. Habib cikin sanyin muryar shi, ya ce, "Mommyna Allah ban san da zaman kowa ba, amma ki bari zan yi bincike yanzu". Hajiya turai kashe wayarta ta yi. Habib ko Mahaifiyar shi na kashe kiran, ya kira Number Bilya. Bilya na d'agawa Habib ya ce, "Bilya da kai da wadda ka kawo da kuma wadda ka ba ajiyarta, kuzo yanzu". Cikin bilya sai da ya yi k'ara jin abinda Habib ya ce, hakan yasa da sauri ya bar SANAT YOGHURT, ya koma can gidan Habib d'in. Bilya tun kafin ya isa yakira Baba Lami awaya ya ce su had'u wajan get harda Yarinyar da yabata ajiya. Bilya na zuwa suka ya iske Baba da Hassana wajan get d'in suna jiranshi. Bilya kallan Baba ya yi, ya ce, "Baba Wallahi ban tab'a ganin muna fukai ba kamar 'yan aikin gidannan ba, yanzu wai har an samu wanda ya kaima Oga Habib gulmar zaman Yarinyar nan agidannan, yanzu haka yana nai manmu mu dukanmu". Baba lami dafe k'irji ta yi, ta ce, "Bilya kasan Allah yaron nan korarmu zai yi". Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, "Baba ni ba abinda ke damuna ba yanzu kenan". Bilya a motar shi ya d'auki su Baba, zuwa SANAT YOGHURT. Koda suka shiga wajan Hassana kallan sunan da ke d'auke da tank'ameman Company ta ke, da kuma tsaruwa irin ta gurin, ko ina 'yan akine sanye da Uniform d'in su green and orange . kasan cewar Habib ya san da zuwan su Bilya , hakan yasa kai tsaye suka shiga tank'ameman Office d'in Oga Habib. Habib na zaune yana ta aikinsa a laptop d'in shi, yana jin su Bilya amma yaci gaba da aikinshi. Habib sai da yagama abinda ya ke yi, sannan ya d'ago kai yana kallan su d'aya bayan d'aya. Habib mai da kallan shi ga Bilya ya yi, ya ce.......................