← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 78

Sashe 35

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana kuma ganin bai kuma d'aga mata kafad'a ba tashi ta yi, ta nufi toilet. Kusan tare da Habib suka isa toilet d'in. Hassana cikin jin haushin Habib d'in ta ke kallan shi, sannan ta ce, "Tom yi haka". Hassana ta rufe idonta tana numa Habib shima ya rufe".

Habib rufe idon shi ya yi kamar yadda yaga Hassana ta rufe".

Hassana ko naganin Habib ya rufe idon shi ta yi saurin cire doguwar rigar da je jikinta da bra da pant d'inta. Tana yi tana kallan Habib gudun karya bud'e idon shi. Hassama matsawa ta yi inda Shower ta ke ta kuna".

Habib ko najin sud'in fitar ruwa ya yi saurin bud'e idon shi".

Hassana ko ta juyama Habib baya, tana wanke jikinta da sauri da soso gudun kar Habib ya bud'e ido. Sai jin mutum ta yi bayanta yana k'ok'arin fusge sosan da take hannunta".

Hassana cikin rud'ewa ta juyo tana kallan Habib. Kafin ta yi wani abuma ya fusge sosan dake hannunta yana wanke jikinshi shima kamar yadda yaga tana yi".

Hassana lokaci d'aya dariya ta kamata ga b'akincin bud'e idon shi da ya yi ga kuma dariyar yadda ya ke wanke kayan jikinshi da soso shi ala dole wanka ya ke yi. Hassana baya ta kuma juyama Habib ta ci gaba da wankanta da soap ka d'ai ba soso".

Habib ma aje sosan ya yi , ya dawo d'aukar soap d'in yana gogawa a kayan shi kamar yadda yaga Hassana na gogawa ajikinta".

Hassana ko ganin Habib ya aje sosan d'auka ta yi ta ci gaba da wanke jikinta da shi"

Habib ganin ta d'auki sosan, shima aje soap d'in ya yi ya fusge sosan daga hannunta". Hassana wanke jikinta ta yi da ruwa ta d'aura towel d'in da ta gani agun an rataye".

Habib ma towel d'in ya d'akko shima ya d'aura akan kayan shi kamar yadda yaga Hassana ta yi".

Hassana ko kallan Habib ka wai ta yi tai murmushi ta barshi ta fita daga toilet d'in. Habib ma bayan Hassana ya bi shima".

Hassana dressing mirror d'in Habib ta je ta d'auki lotion d'in shi tana shafawa, Hassana jin k'amshin man ya yi yawa yasa ta kuma dubawa dan ta gani kodai turare ne bata sani ba. Dubawa ta yi taga mai ne".

Habib shima tatsa ya rik'ayi yana shafawa, kamar yadda yaga Hassana na yi".

Hassana d'aya daga cikin doguwar rigar da Jimmai ta siyo mata sata. Bayan Hassana ta gama shiryawa Habib ta kalla da ya ke tsaye yana kallanta kayan shi duk sun jik'e har d'iga suke. Hassana wajan kayan Habib ta je ta d'akko mai k'ana marasa nauyi ta kawo mai ta ce, "Oga Habib ga kayanka ka sa".

Habib kallan Hassana ya yi. Hassana tunanin Habib ba amsa zai yi ba da ta yi, yasa ta kama hannun Habib d'in ta zaunar da shi kan lover chair d'in bedroom d'in. Hassana rigar Habib da ke jik'e ta cire mai ta sa mai wata, sannan ta rufe idonta ta kama wandonma ta zare mai, ahaka dai da rintse ido Hassana ta sa ma Habib kaya ".

Hassana nagama shirya Habib aka kira sallar magriba. Toilet d'in ta koma ita da mak'ake mata d'inta suka yi alwallah, tazo ta shimfid'a sallahya ta tada sallah. Nan dai duk yadda tai Habib ya yi ahaka tai sallar. Tana idarwa Baba Lami ta kawo masu abincin dare. Hassana sai da tayi sallar Ishsha'i sannan ta tashi daga kan abin sallar".

Tuwan semo miyar kuka ta ji naman rago. Hassana hannu tasa tasa ma Habib ma nashi suka ci tare. Suna gamawa ta wankema Habib hannu itama ta wanke nata".

Dama Hassana ta sa da baccin wuri, suna gama cin abinci ba dad'ewa ta tashi ta nufi bedroom d'in Habib ta kwanta. Inda shima oganta ya mara mata baya, ya kwanta kusa da ita, 12:59Am Allah ya tai maki Hassana ta tashi ta ba Habib rubutun shi".

Washe gari Hassana bayan ankawo masu abin kari sun karya. Tashi ta yi takama rigar jikinta ta cire ta d'ora towel. Habib ma naganin haka shima ya kama tashi ya cire kamar yadda yaga Hassana ta yi. Tom da yake ita Hassana ba dogon wando gareta ba bare Habib yaga ta cire shima ya cire. Hassana toilet ta shiga Habib ya fita".

Wanka Hassana ta yi duk yadda ta yi Habib na yi kamar jiya ahaka dai suka gama wankan".

Wajan shama haka sukai duk yadda Hassana ta yi Habib na yi ahaka ya shafa mai, Hassana ta ciroma Habib kayan shi ta samai kamar jiya, itama ta sa cikin wa inda Jimmai ta siyo mata".

Hassana bayan ta shirya ta shirya Habib. Kallan Habib ta yi ta ce, "Tom Oga Habib yau Mommy za mu je mu gaida ". Hassana fita ta yi ta ja k'ofar ta rufe. Habib kuma kama hannun Hassana ya yi katam ya rik'e".

Ahaka Habib da Hassana suka jera suka nufi part d'in Hajiya Turai. Duk 'yan aikin gida da mamaki suke kallan Hassana, dan duk cikinsu ba kowa bane yasan Hassana na kula da Habib, bare kuma magar auran su banda Jimmai babu wanda yasan da maganar auran Hassana da Habib ba".

Hassana dai-dai zasu shiga site d'in Hajiya Turai sai ga Farida da zuwanta kenan gidan".

Farida cikin tashin hankali da damuwa ta ke kallan Hassana da hannunta ke cikin na Habib......

Idan kin karanta d'aure ki yi Comment Sister 🤝

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA NA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Ayi hak'uri da wrong typing ina ciwan ido ne👁️👁️.

Shafi na 40 & 41.

Farida cikin tashin hankali da damuwa ta ke kallan Hassana da hannun ke cikin na Habib amak'ale.
Hassana ko da bata lura da Farida ba ta gaban Farida ta wuce, batare da ta lura da ita ba. Farida ko cikin jin zafi da haushi ta da kama Hassana tsawa, ta ce, "Ke wata irin sakarya ce!, kuma ubanwa yasa ki ki fito da Oga Habib!? ".

Hassana da kwatakwata bata lura da Farida ba, sai tsawarata ta ji, cikin tsoro ta juyo tana kallan Faridar, ta ce, "Ayyah Aunty Farida dan Allah ki yi hak'uri, Wallahi ban lura da ke bane". "Dama taya zaki lura dani, kanki narawa ke ga Amaryar Oga Habib ko?, Tom bari kiji Wallahi daga yau har uzuwa ranar da auran nan zai zo k'arshe karki yadda karki kuskura kik'ara fitowa da Oga Habib, idan kuma ba haka ba zan nuna miki ainihin kalata, dan haka ki mai dashi inda kika fito da shi sakarya kawai! ".

Hassana harga garanta bataji dad'in yadda Farida ke zaginta ba. Hassana kama hannun Habib ta yi suka juya".

Hajiya Turai ko da hayaniyar Farida ta sa ta fito, kallan Farida ta yi, tana kuma kallan bayan Hassana ta ke tafiya, ganin kamar gunta suka zo kuma ta ga sun juya, tabbas ko ba a fad'a mata ba tasan Farida ce ta koreta, inda taji yo hayaniyar fad'an Farida. Hajiya Turai kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida ke da wa kike hayaniya haka? ". Farida cikin alamun ta ji haushin abinda Hassana tai ta ce, "Mommy wannan 'yar iyayin yarinyar ce mana, ta wani kama ta fito da Oga Habib ,kowa wama yasata". "Ok kiramin ita ". Cewar Hajiya Turai ".

Farida ko cikin b'acin ciki dajin haushi ta je kiran Hassana, dan ita a ganinta rainine kamarta ta je kiran Hassana. Farida tun kan tak'arasa inda Hassana ta ke ta ce, "Ke! ". Hassana tsayawa ta yi amma bata waigoba".

Farida k'arasowa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, "Lallai, kin isa, tom Mommy na kiranki, kuma Wallahi Kin dai ji kashai din da nai miki, kar in kuma ganin kin fito da Oga Habib , idan kuma ba haka ba, zaki gani! ".

Ita dai Hassana bata ce ma Farida ko mai ba, kama hannun Habib ta yi suka k'arasa inda Hajiya Turai ke tsaye".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter lafiya kika fito ke da Habib? ". Hassana cikin sanyin muryata ta ce, "Mommy munzo gaida ke ne? ". Hajiya Turai cikin nuna jin dad'in ta ta ce, "Kai, ka ce yau inada manyan bak'i tom ku shigo ciki".

Hassama ta na rike da hannun Habib suka Shiga tan k'ameman Falon Hajiya Turai.
Bayan Hassana ta zauna ne, ta gaida Hajiya Turai cikin grimamawa kamar yadda ta saba".

Hajiya Turai da sakin fuska ta amsa ma Hassana ta ce, "Lafiya lau daughter ya kike?, ya Habib da jikin da fatan ana ganin sauk'i ? ". "Eh Mommy da sauk'i, inda kinga yafara sakewa da mutane bakamar da ba". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta ce, "Alhamdulillah Allah yak'aro sauk'i". "Ameen ya Allah ". Cewar Hassana".

Hajiya Turai shuru ta yi na 'yan second's, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Daughter mai ya had'aki da Farida? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta fara ba Hajiya Turai amsa kamar haka"fad'ata tai min wai kar in sake fitowa da Oga Habib ". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ita ta sa kika koma da shi ko? ". "Eh Mommy ita ce". K'wafa Hajiya Turai ta yi, ta ce, "zata sani dan taga ina barinta ne".

Hajiya Turai kiran Maimuna ta yi ta ce ad'ora girgi yanzu, kuma tana buk'atar abinci mai dad'i dan acewarta tana da manyan bak'i ".

Hassana dai murmushi ta yi, jin Hajiya Turai na kiransu da manyan bak'i ".
Chapter 35 · 0% Book details