← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 78

Sashe 27

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilya sosai ya ji yana jin tausan Hajiya Turai saboda abinda zai ce, amma ganin ta matsu da ta ji, yasa, cikin sanyin murya ya ce, "Hajiya dama akan Oga Habib ne, jiya kince muje mu fito da Hassana bayan ta ba Oga Habib magani, amma Hajiya Oga Habib kinsan bai barin yarinyar nan fita, dan yanzu abin yafara cin tura ma, dan ko yau da safe dakyar nida Musa muka kwaceta daga hanun Oga Habib, Wallahi Hajiya biki ga yadda yarinyar ke kuka ba, tana rok'ona dan Allah ita dai bazata k'ara zuwa kai ma Oga Habib ko mai ba". Shiru Bilya ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Tom Hajiya shine nake son dama musan yadda zamu b'ulloma lamarin, inda ita yarinyar ta nuna gajiyawarta, duk da zuciyata na zargin kamar wani abun ya yi mata".

Hajiya Turai cikin tsantsar damuwar da ta kasa b'oyewa ta ce, "Bilya ya zanyi da Habib, dan Allah kakiramin ita ta rik'a ba Habib magani ni Wallahi konawa ne zan biyata, dan Allah Bilya, ku tai makeni, Habib shikenan min, shi kad'ai ne wanda yarage min nake kallo inji dad'i, dan Allah Baba Lami kisa baki, wa zai ba Habib magani idan yarinyar nan tak'i? ". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin rud'ewa".

Shiru Bilya ya yi, dan gaba d'aya tausan Hajiya Turai ya cika zuciyar shi. Baba Lami kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Hajiya ni inada wata shawara duk da dai kamar ba mai yuwuwa bace, amma idan aka so zata yuwu? ". Hajiya Turai kamar zata sa ihu ta ce, ", Baba Lami wata shawara ce, ina jinki? ". Shiru Baba Lami ta yi tana tunanin ta inda zata fara ba yani, dan ita kanta tasan lamarin babba ne, sai da Baba Lami, ta d'auki dogon lokaci sannan ta ce, "Hajiya ni gani nake, inda Oga Habib bai yarda da kowa sai yarinyar nan, ko abinci in bata gu bazai ciba, bare magani, rok'onta zamu taru muyi,ta auri Oga Habib kafin nan da yaji sauk'i, Allah bashi sai ayi auran asirri babu wanda zaima sani, Allah bashi duk radda Oga Habib ya warke shikenan, ki naimi zaki bata konawa ne, amma ya kika gani Hajiya? ". Hajiya Turai cikin sanyin ta ke cewa, "Dan Allah Baba Lami ku taimaka ku rok'anmin ita, Wallahi nima tunanina kenan, amma inajin shakkar furtawa dan kar aimin kallon mai son kanta da yawa".

Baba Lami kallan Bilya ta yi tace, "Bilya baka ce komai ba, ya kagani? ". "Eh gaskiya Baba Lami wannan kam shine abunda zai fi, amma kuma shi Oga Habib d'inne, baku tsoran ranar da zai farka ya riski wannan labarin? ". Shiru Baba Lami ta yi, Sannan ta ce, "Bilya ni kaina nasan Oga Habib ba zai zauna da Yarinyar nan ba, dama dai auran kafin yaji sauk'i ne".

Sosai Bilya ya amsu da shawarar dan yafi kowa sanin waye Oga Habib.
Hajiya Turai kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya kiramin Hassana yanzu ". Bilya tashi ya yi zai fita dai-dai kuma Hajiya Murja ta shigo , shigo warta kenan".

Dakyar Hajiya Turai ta daure wajan sakin fuskarta ta yi ma Hajiya Murja sannu da zuwa.
Nan dai suka gaggaisa da kyau kamar kusan yadda suka saba gaisawa. Hajiya Murja kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba Lami wannan meeting d'in fa ,na meye? ". Baba Lami ko da yake tasan abinda ke faruwa, da gayya ta ce, "Na auran d'anki ne, Habib". "Haba-haba aure kuma shidawa? ". Nan Baba Lami ta labarta mata komai game da yadda suka tsara na had'a Hassana aure da Habib kafin ya samu lafiya".

Da kyar Hajiya Murja ta iya b'oye damuwata tana washe baki ta ce, "Hakan ko ya yi ya yi kyau sosai"

Shigowar Hassana da Bilya ce, tasa Hajiya Murja ta yi shiru ta maida kallanta ga Hassana. Hajiya Turai ko hannun Hassana ta Kama, ta ce, "Hassana zaki ji". Hajiya Turai shigar da Hassana bedroom d'in ta ta yi".

Bilya ko na kawo Hassana ya Kama gaban shi, Baba Lami ma hakan ta ke. Falon ya rage daga Farida sai Hajiya Murja".

Farida ko tunda ta ji maganar had'a Hassana da Habib aure, ta tusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka, mai had'e da tashin hankali".

Hajiya Murja ganin Falon ba kowa sai su kad'ai tashi ta yi, ta je inda Farida ta ke tana kuka. Hajiya Murja hannun Farida ta kamo ta ce, "Kishiru Farida dan Allah, karki d'orama kanki wani ciwan". Farida kai ta d'ago tana kallan Mahaifiyarta ta ce, "Mommy ko mai bai yi ba, dan yarinyar nan bata ba Oga Habib maganin nan ba, kuma yanzu kinji maganar da suke yi, Wallahi Mommy idan har haka ta tabbata tom baki sake ganina, Mommy zan tafi wani gu wanda nima bansan inane ba, bazaki k'ara ganinba". Farida ta idasa maganar cikin matsanancin kuka". Hajiya Murja cikin tashin hankali da jin abinda Farida ta ce dan tasan zata yi fiye da abinda ta ce, Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!, kinji narantse, Wallahi auran nan ba zai yuwu ba, dan haka kima kwantar da hankalinki, ko yanzu bada ga gurin Malam me biyan buk'ata dole bane matsala ta samu, daga gurin mune, dan haka karma ki d'aga hankalinki, da ke za a d'aura auran nan, karma ki sama kanki damuwa ko d'aya". Farida kallan Hajiya Murja ta yi, dan sao taji hankalinta ya d'an fara kwanciya jin abinda Mahaifiyarta ta ce, dan tasan akanta babu abinda Hajiya Murja ba za tai ba, bakamar ce mata d'in da tayi bazata k'ara ganin ta ba".

Farida rik'e hannun Mahaifiyarta ta yi, ta ce, "Mommy ina tsoran asamu kuskure irin wannan karan? ". Murmushi Hajiya Murja ta yi ta ce, "Farida Wallahi Habib bashi da mata sai ke, tashi muje wajan Malam mai biyan buk'ata dole ayita ta k'are, ".

Farida tashi ta yi, suka tafi da Hajiya Murja..............

Idan kin karanta daure ki yi comment sister 🤝

Share
&
Comment please 🙏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group :https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Mak'iyanka Mutane uku ne:Mai k'in ka, da mai k'in masoyinka, da mai son mak'iyinka. Mai son Uwa dole ne ya so d'anta. Ya Allah ka had'amu da masu son mu a duk inda suke👏.

Ina gaisuwa, sister Hassana barrister, Allah ya tai makeki aduk inda kike, miji nagari nai miki fata🤝

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.

Shafi na 30&31.

Hajiya Murja da Farida zaune gaban Malam mai biyan buk'ata dole. Hajiya Murja cikin damuwa ta ce, "Malam Wallahi ko mai fa ya lallace! ". Bakin k'aton da aka kira da Malam, kallan Hajiya Murja ya yi da jajayan idon shi, cikin fad'a-fad'a ya ce, "Hajiya kamar ya, bangane aiki ya lallace? ".Hajiya Murja cikin damuwa ta ce, "Malam abubuwa fa sun b'ace, wato maganin da kaba Farida kace taba yarinyar ta sha ta ba Oga Habib shima ya sha, tom Wallahi Malam kuskure aka samu, yarinyar ita kad'ai tasha bata ba Oga Habib ya shaba, tom yanzu dai Malam duk ba ma wannan ba, yanzu babban abin tashin hankalin, had'a auran yarinyar da Oga Habib zu ke so suyi". Hajiya Murja ta idasa maganar cikin yanayin damuwa".

Wani 'yan zane-zane ya yi ak'asa sannan ya ce, "Yanzu me kuke so ayi, dakatar da auran za ai?, koko amintar yarinyar da shi kuke so araba?, koko gidan za a koreta gaba d'aya?". Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida mi ke so ayi, a cikin abinda Malam ya lissafo? ". Shiru Farida ta yi tana tunani, sannan zuwa can ta ce, "Malam ni yanzu auran nan da suke maganar had'awa nake so afasa, maganar ta yi shiru kamar ba ayi ba, sannan a raba yarinyar da gidan gaba d'aya".

Yadad'e yana zane-zane ak'asa sannan ya ce,"aikinki mai sauk'i ne, amma fa dole sai anraba amintar yaron da yarinyar, maganar aure kuma inda akayi ta anan za'abarta baza su k'ara tada maganar ba". Wani magani yad'akko ya mik'ama Farida, ya ce, "Wannan maganin zaki zuba shine a abinci ko abinsha, duk wanda ya ke da hannu da tsaki amaganar azuba maganin nan abinci ko abin sha aba shi yaci, magana ta k'arae, babu wanda zai kuma tadata". Wani maganin ya kuma d'akkowa ya ba Farida, ya ce, "Wannan kuma irin wanda na baki ne, zaki ba yarinyar da yaron su ci a abinci ko abin sha".

Farida amsar maganin ta yi, ta ce, "Malam kenan dole ne ya kusanci yarinyar? "."Eh dole ne, ta hakane za'araba amintar shi da yarinyar".shiru Farida ta yi, sannan ta ce, "Malam ba a iya raba yarinyar da gidan, inda idan akai hakanma kamar anraba shi da yarinyar ne". "Idan haka kike so za ai miki, amma fa zai ci gana da k'in aminta da kowa, kamar yadda ya ke yi ayanzu, idan har kina son komai ya tafi dai-dai tom dole sai anraba amintar yaron da yarinyar sannan". Shiru Farida ta yi sannan ta ce, "Shikenan Malam, ayi hakan".
Chapter 27 · 0% Book details