← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 78

Sashe 65

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa👌👌.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa 👌👌

Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number👉 08063830828.

Shafi na 79&80.

Managerrrrrrrrrrrrr.... ". Habib da fitowar shi ke nan daga Office d'in shi, ya ci karo da marin da Manager ya yi ma Hassana, manager ya kuma d'aga hannu zai k'ara mata ne Habib ya yi mai wannan kiran. Habib ranshi b'ace ya k'ara so gun, yana zuwa ya d'aga hannu sai da ya yi ma manager mari kwarara guda uku, sannan Habib ya nuna shi da hannu ya ce, "Manager ashe baka da tunani ban sani ba, yau fa ta dawo aiki daga Suspection d'in da ka bata, haka bai yi ma ba yanzu ta dawo zaka d'aga hannu ka mareta a company'na kuma!, ba komai ba laifinka ba... ". Maganar Hajiya Turai da Habib ya ji ce, ya yi saurin juyowa. Hajiya Turai zuwan ta kenan, ta hango Hassana zuk'un ne agun tana kuka, Hajiya Turai ita duk tunaninta ma Habib ne ya mari Hassana, hakan yasa, tana zuwa ta kamo hanun Hassana da ke zuk'unne agun ta ce, "Yi hak'uri daughter tashi muje gida". Daga ganin yadda Hajiya Turai ke magana kasan ranta a matuk'ar b'ace ya ke".

Habib ko da kallo ya bi Hajiya Turai, dan yama rasa ya zai ce mata, Habib bin Hajiya Turai ya yi, dai-dai zasu shiga mota, ya ce, "Mommy ki.... ". "Bana son magana a condition d'in da nake! ". Habib jin abinda Mahaifiyarsa ta ce ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru".

Habib Office d'in shi ya koma, ga ba d'aya ya rasa abinda ya ke mai dad'i, ana cikin haka ne, manager ya shigo, manager cikin hikima ya fara magana kamar haka"M'd ka yi hak'uri na kasa control d'in fushina, dan Allah ka yi hak'uri, ta kira ni da sunan da nakasa control d'in kaina ne... ". Tsawar da Habib ya yi ma manager ce tasa ya yi shiru. Habib kallan manager ya yi, ya ce, "Manager wai hak'uri zaka ban!?, kasan abinda ka aikata kuwa? , mari fa!?, tom bari kaji naji haushin korarta aiki da kayi, amma ban nuna ma ba, amma haka bai ma ba..., manager bana son yawan magana dan Allah ka fita kawai! ". Manager kallan Habib ya yi, ya ce, "M. D, dan Allah ka saurare n.. ". "Kafita nace ko!? ". Habib ya fad'i maganar da k'arfi".

Manage fita ya yi. B'anga ran Hajiya Turai ko, bayan sunje gida kallan Hassana ta yi ga sawun marin da manager ya yi mata nan kwance a fuskarta, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Habib d'in ne ya mareki haka daughter? ". Kai Hassana ta girgiza ma Hajiya Turai ta ce, "A, a Mommy ba shi bane manager ne". Hajiya Turai da mamaki ta ce, "Manager kuma?, yanzu har Habib ya ba su manager damar da zai d'aga hannu ya mareki!?, dama da nace ma Habib kar ya sake kije Sanat aiki, da ya ke yaga na tafi shine sai da ya tura ki , ba damuwa ". Ita dai Hassana bata ce ma Hajiya Turai komai ba, dan ta ga tsan tsar b'acin ran Hajiya Turai a fili, na Marin da akai mata".

Habib sai bayan magriba ya je gidan Hajiya Turai. Lokacin Hajiya Turai na falo, Habib ya shigo, tun daga yadda Hajiya Turai ta amsa ma Habib sallamar shi yasan akwai matsala. Habib d'an nesa da Hajiya Turai ya zau na, sanna ya gaida ta, Hajiya Turai da lafiya ta amsa ma Habib. Sannan Hajiya Turai ta kalli Habib ta ce, "Habib dama da nace ma kar Hassana ta je Company'ka tai aiki, shi bayan tafiya ta ka tura ta ko!?, shi ne ka wulak'anta ta gaban worker's d'in ka, har kaba wasu damar marina, babu komai bani ka wulak'an ta ba, kuma ita ma ba'ita ka wula k'anta ba, auranka ka wulak'anta". Habib kai ya d'ago ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Mommy ki yi hak'uri, insha Allah haka ba zai k'ara faruwa ba". "Tom Habib ai hak'uri ya zama dole, idan ban yi hak'uri ba, zan sa a kama manager ne?, na yi hak'uri saboda wasu 'yan da lilai". Habib jan bakin shi ya yi ya yi shiru, dan bai san mai zai kuma cema Hajiya Turai ba kuma" Hajiya Turai ko tashi tai ta bar Habib shi ka d'ai agun".

Habib ya dad'e zaune, sannan ya tashi ya shiga bedroom d'in Hajiya Turai ya yi mata sallama zai wuce. Hajiya Turai ba tare da ta kalli Habib ba, ta ce, "Sai da safe". Habib ganin Hajiya Turai ba tai mai maganar Hassana ba, kuma bai ga Hassanar ba, yasa ya yi tunanin tana gidan shi".

Habib yana zuwa ya shige bedroom d'in shi, ya yi duk abinda zai yi har ya kwanta shiru bai ga Hassana ba, dan kullum Hassana ta saba sai ta damama Habib kunun shi ta kawo mai, a haka zasu yi ta fira da Habib, idan zata tafi ta kwanta Habib ya raka ta".

Habib jin shirun ya yi yawa, yasa ya tashi ya nufi side d'in Hassana. Habib ko da ya shiga bai ga Hassana ba, hakan ya tabbatar mai da tana gida kenan. Habib ko mawa ya yi bedroom d'in shi ya kwanta".

Washe gari Habib bayan ya gama shirinsa na tafiya aiki, sai da ya biya ta gidan Hajiya Turai. Habib zau ne ya iske Hajiya Turai da Hassana a derning space suna break fast. Habib zama ya yi, sannan ya gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai sama-sama ta amsa ma Habib, sannan ta tura mai flaks d'in tea, Habib tsiyaya wa ya yi. Sai dai abinda ya d'aure ma Habib kai ganin Hassana ko kallan inda ya ke bata yi ba, bare ya sa ran zata gaida shi. abinda Habib ko bai sani ba, Hajiya Turai ce tasa Hassana karta sake ta gaida Habib ko da yazo. Ita kuma Hassana ta yi hakane kawai dan bin umar'nin Hajiya Turai, amma ita bata ga abinda Habib ya yi mata ba, acewarta, Manager ne ya mareta ba Habib ba, ko a yan zu Hassama ji tai ba dad'i gaida Habib d'in da ba tai ba, hakan yasa Hassana na gama shan tea d'in ta ta shi ta bar gun,Habib da kallo ya bi Hassana. Habib ka d'an yasha tea d'in ya yi ma Hajiya Turai sallama ya tafi".

Habib na zuwa babu da d'ewa manager ya shigo Office d'in, manager kallan Habib ya yi, ya ce, "M. D dan Allah... ".Habib hannu ya d'a gama manager ya ce, "Manager dan Allah kaje kawai sai na ne me ka!". Manager fita ya yi".

Billy da Farida ne suka tare manager, Billy kallan manager ta yi, ta ce, " Manager ya ku kai da Oga Habib d'in ? ". "Wai inje sai ya nai man". Manager ya basu amsa".

Farida kallan manager ta yi, ta ce, "Wai dan ka mari yarinyar nan ne ya ke ma kora da hali haka? ". "Eh haka ne". Cewar manager. Farida ranta b'ace ta bar gurin bata sake iya yin managa ba. Manager kuma fita ya yi daga Company baki d'aya . Inda ita kuma Billy ta koma ta ci gaba da aikinta".

Habib yau ma kamar jiya yana tashi aiki ya yo gidan Hajiya Turai. Babu kowa a falon, Habin zama ya yi yana jiran fitowar Hajiya Turai, yana nan zaune ko Hajiya Turai ta fito. Habib koda ya gaida Hajiya Turai da sakin fuska ta amsa mai ba kamar jiya ba, Habib ganin haka, ya sa ya ce, "Mommy kunu na ke so please ". Hajiya Turai da kanta ta shiga kitchen ta dama ma Habib kunu ta kawo mai.Hajiya Turai na ba Habib kunu ta nufi bedroom d'in ta inda ta bar Hassana, Hajiya Turai kwance ta iske Hassana, Hajiya Turai gefan Hassana ta zauna, ta ce, "daughter tashi mu yi magana". Hassana tashi ta yi ta zau na".
Chapter 65 · 0% Book details