← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 78

Sashe 61

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hassana k'arfe 3 na rana bayan sun tashi ta biya ta Sanat dan ganin, su Billy suna nan ko sun tafi. Hassana babu inda bata duba ba, amma bata gansu ba, hakan yasa ta samu k'awarta Amina, ta tambayeta ko supervisor na nan".

Amina kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana Amma dai akwai releshanship tsakanin ki da Oga Habib ko? ". Hassana kai ta girgiza ta ce, "Babu komai tsakanin mu, malam ki ban amsa ta supervisor na nan ko ta tafi?, ita da Farida? ". "Eh naga tafiyar su, ita da Aunty Farida". Cewar Amina, tana kallan Hassana, dan bata yadda da cewar da Hassana ta yi ba babu dan gantakar komai tsakaninta da Habib".

Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Nina wuce, sai gobe insha Allah ".

Habib yau da wuri ya koma gida. Hassana ko tana dawowa gida taima Habib kunun shi d'an kullun. Hassana ba ita ta shiga side d'in Habib ba sai da ta tabbatar ya gama komai sannan ta shiga, da kununta a hannu. Lokacin Habib yana waya da Hajiya Turai tana sanar dashi da wowarta gobe. Hassana guri ta samu ta zauna ta zauna tana jiran Habib ya gama wayar. Hajiya Turai ko, fad'a tai kema Habib ta ce yaba Hassana waya ya k'i tun da tazo basu yi waya ba, kuma tana kiran wayarta a kashe, dan haka yanzu ya bata. Habib mik'ama Hassana wayar ya yi. Hassana ko kallan Habib ta yi, tana tambayar shi waye Oga Habib? ". "Kisa a kunnanki kiji". Habib ya ba Hassana amsa".

Hassana sosai tayi murna jin Muryar Hajiya Turai da ta yi. Bayan sun gaisa ne, Hajiya Turai ke tambayar Hassana lafiya tana kiran wayarta bata zuwa? ". "Mommy ruwa ta fad'a nayi-nayi tak'i kawowa". Hassana taba Hajiya Turai amsa ".

"Zan kawo miki wata kinji daughter ". Hassana godiya ta yi ma Hajiya Turai dan tana son waya sosai. Bayan Hajiya Turai ta kashe ne, Hassana ta kalli Habib ta ce, "Ina wuni Oga Habib ". Habib banza ya yi da Hassana ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma cikin sanyin murya ganin Habib ya juya mata baya sosai, dan ko inda take yak'i kallo, kuma kwana biyu ba haka yake mata ba, hakan yasa Hassana cikin sanyin murya ta ce, "Oga Habib? ". Habib banza ya yi da Hassana. Hassana kuma bata gaji ba, ta kuma cewa, "Oga Habib! ". Nan ma Shiru ba amsa. Hassana kamar za tai kuka ta ce, "Oga Habib kaga ko hannuna inajin ya yi tsagewar k'ashi, bana iya d'aukar abu mai nauyi da shi, kuma bakaji ba yadda ya ke min zafi". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Muga hannun? ".Hassana da gaske hannun yana mata zafi amma ba sosai ba, mik'ama Habib hannun ta yi". Habib ko na amsar hannun ya rik'e ya na ja mata shi da k'arfi sosai, yana d'an bubbuga hannu".

Hassana da k'arya take hanun ba wani ciwan kuzo kugani hannunke mata ba, ai take ta fara kuka, tana cewa, "Wayyo Oga Habib basshi haka dan Allah ". Habib ko be bari ba cigaba da latsama Hassana hannun ya yi, ita kuma tana ihu, tana rirrik'e hannun Habib. Habib da katawa ya yi yana kallan Hassana, ya ce, "Kin sha maganinki? ". Kai Hassana ta d'agama Habib."banyar da ba, je ki d'akko in gani? ". Cewar Habib".

Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Nafa manta shi a Office d'inka". Habib shiru ya yi ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma so take taima Habib maganar su Billy ta rasa yadda za tai, sai zuwa can ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib dan Allah karka dawo da su Billy sai nan da sati, kaga nima ai kaji dad'i kace na fidda kai kunya ko?, dan Allah Oga Habib kabar su sai sun yi sati, dan Allah, kaji Oga Habib ". Habib ko kamar jiran Hassana ya ke, ya aje wayar hannun shi, ya kalli Hassana ya ce, "Wallahi! Wallahi!! Ida har aka kuma fad'a dake a Sanat... ". Habib kai ya girgiza. "Tom aini bani ke to nan su ba, suke to nona. Hassana kunun da ta damama Habib ta mik'ama mai ta ce, "Oga Habib ga kunun ka karya huce". "Bazan shafa".Habib yaba Hassana amsa".

Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib me yasa?". Kin b'ata min rai yau". Hassana dama tun a sanat da ta kori su Billy taga irin kallan da Habib yake mata, ita yanzu tashin hankalinta d'aya kar ya ce zai cireta a matsayinta".

Hassana kallan Habib ta yi, cikin sanyin murya, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yafe min, Allah bazan kuma ba, koma sun min zan rik'a banza da su, kuma dan Allah karka cireni a matsayina". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "da ga yau karki kuma fad'a da kowa!? ". Ya fad'i maganar cikin gargad'i ".
"Allah bazan kuma ba". Cewar Hassana, sanna ta d'akko kunun ta ce, tom gashi kashi".

Habib amsa ya yi, yana sha. da yake Habib kan 3 seater ya ke zaune,kafin Habib ya gama shan kunun Hassana da ke kusa da shi zaune, gafen kujerar ta kwanta, tana jiran Habib ya shanye kunun ta fita da Cup d'in. Sai dai Kafin Habib ya shanye kunun bacci ya kwashe Hassana. Habib ko yana gamawa ya ce, "Nagama tashi karki bacci, ki je ki kwanta". Abinda Habib ko bai sani ba, Hassana har ta yi baccinta".

Habib jin Hassana ta yi mai shiru, kallanta ya yi, abin mamaki sai yaga ashema baccin ta ke. Habib bubbuga Hassana ya yi, ya ce, "Ke tashi kije ki kwanta zan rufe k'ofana". "Hmmmm". Hassana da ke jin Habib sama-sama ta amsa mai".

Habib kuma buga k'afar Hassana ya yi. Hassana da bacci sosai ya kwasheta, ta ce, "Wayyo Allah na, tom ina zuwa". Habib tsaki ya yi ya tashi ya kashe wutar falon, ya nufi bedroom d'in shi, inda dama Hassana a falon shi ta sa mai".

Cikin dare Hassana ta farka fitsari, ta ganta cikin duhu, ai take ta fara ihu, dan ta mamanta kwata -kwata ba a bedroom d'in ta ta ke ba. Hakan yasa Hassana ta fara ihu tana laliban makunni amma bata gani ba, ita atunaninta wani ne ya shiga ya kashe mata wuta in da dai ita bata kashe wuta a haske ta ke kwana. Ai Hassana dagewa tai tana ihu ".

Habib ko da ya yi nisa sosai a bacci, cikin bacci ya ji yo ihun Hassana a falon shi, da sauri Habib ya tashi ya nufi falon, yana zuwa ya kunna wutar falon. Ko da ya kalli Hassana a furgice ya ga take. Tsaki Habib ya yi, ya ce, "Shikenan ke ako mai baki da hankali". Hassana baki ta turo tana cewa, "Oga Habib nifa na manta ba a bedroom d'ina nake ba, kuma ni bana kwana a duhu. Hassana da fitsari ya matseta, kallan Habib ta yi ta ce, "Oga Habib dan Allah inajin fitsari". "Kije naki toilet d'in ki yi mana". Cewar Habib".

Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib dan Allah fa, Wallahi ya matsan". Habib yana jan tsaki ya nuna ma Hassana bedroom d'in shi. Hassana da saurinta tashi ga. tana fitowa Ta nufi falon Habib. Habib koma ya koma bedroom d'in shi ya kwanta, Hassana zaune ta yi, a falon Habib, dan ita matsorarciya ce sosai. Sai da Hassana ta tabbatar ya isa ace Habib ya yi bacci sannan ta lallab'a ta shiga bedroom d'in shi ta kwanta can bayan shi, tana addu'ar karya tashi".

Habib ko bashi ya farka ba, sai asuba, ananne yaga Hassana kwance a bayanshi sai baccinta ta ke abinta. Habib da mamaki ya ke kallanta tom yaushe ma ta shigo ta kwanta bai ji ba. toilet d'in shi ya shiga ya yi alwallah ya zo ya tada sallah. Habib har ya idar da Sallah Hassana bata tashi ba, hakan yasa Habib ya ja bargon da ta rufe da shi da k'arfi. Hassana da sauri ta tashi tana sosa kai, ta ce, "Oga Habib... ". Habib hannu ya d'ora lips d'in shi alamun Hassana ta yi shiru. Hassana shiru ta yi ta tashi ta fita".

Habib wanka ya yi, ya yi shirinsa na tafiya aiki, ya tafi. Habib yana zuwa Office d'in shi babu dad'ewa, manager ya shigo. Bayan manager ya gaida Habib ne, manager ya ce, "M, d, dama game da tafiyar Supervisor gida ne, gaskiya m, d, gurin nan ace babu supervisor akwai fa damuwa, dan sanin kankane yarinyar na k'ok'ari sosai, tana kula da 'yan aiki sosai, ita Hassana ta dakatar da ita ne saboda bata yadda da rashin aikinta , ita sai take gani kamar ta tsaneta ne M, d, Supervisor tasan marketing sosai yarinyar, kuma tana da Experience sosai, Hassana ko bata san marketing ba, idan ake za'a d'auki matsayi irin wannan abata akwai matsala M, d, Dan haka ni idan har ka yarda inda na lura Hassana na son matsayi, tom sai a bata supervisor, ita kuma supervisor inda tafi ta Experience sai abata mataimakiyata. Yanzu idan har ka yarda anjima sai a had'a meeting aba kowa matsayinsa". Habib na yarda da duk wani tsarin da manager ya ke kawo, ba tun yau ba, hakan yasa ya ce, " Shikenan manager babu da damuwa, a had'a meeting d'in ".

Hassana da Billy kusan tare suka isa Sanat, inda Hassana ke mamakin ya akai Billy ta dawo aiki. Farida kuma daga baya ta zo".

Manager da kanshi ya bi kowana staff ya sanar da shi da akwai meeting k'arfe goma".

K'arfe goma nayi aka had'u a a inda aka tana da dan meeting. Kowa yana gurin hadda Habib. Manager ne ya tashi ya fara bayani kamar haka. "Tom kamar dai yadda muka saba yi a masana antar nan, duk wanda za'aba wani matsayi sai anyi meeting yau ma haka za muyi. A bisaga jajircewar Supervisor kamar yadda koma wa sani, mun k'ara mata matsayi abisaga jajircewarta na aiki, an k'ara mata matsayi izuwa ga mataimakiyata, inda ita ma Hassana zamu bata matsayin da Supervisor ta bari. ko akwai Wanda ke da magana? ".
Chapter 61 · 0% Book details