← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 78

Sashe 70

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa👌👌.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa 👌👌

VIP group 300 Only👌 , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number👉 08063830828

Shafi na 85&86.

Hajiya Turai da ranta ke ab'ace kallan Habib ta yi ta ce, "Habib ni zaka raina ma hankali ko?, ka saketa na ce! ". "Mommy ki saurare ni Please, Wallahi ban aikata abin da ta ce ba". Hajiya Turai d'aga hannu ta yi ta wanka ma Habib mari, ta ce, " Sakar mata hanni na ce!. ".
Habib wujijjiga Hassana ya yi, ya ce, "Fad'i ma Mommy gaskiya, mai na rubuta miki jikin takardar da na baki? ". Habib ya idasa maganar yana kuma wujijjiga Hassana da k'arfi. Hassana ko da ta tsorata da yadda taga Habib, cikin siririyar murya ta ce, "Ni ban karanta abin da ka rubuta ba, amma na san saki n... ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru bata k'arasa fad'in abin da ta ke fad'a ba. Cikin tsawa Habib ya ce, ", Wallahi zan fasa bakin ki kika idasa! ".

Hassana shiru ta yi tana kallan Hajiya Turai jin Hajiya Turai bata sake magana ba. Hajiya Turai ko tama rasa abin da zata cema Habib ya saki Hassana, hakan yasa ta tsaya tana kallan shi".

Habib kuma tura Hassana ya yi, Hajiya Turai na mai magama amma bai saurareta ba, ya ce, "Muje ki nuna min inda kika aje letter".

Hajiya Turai na ma Habib magana amma bai saurareta ba, haka ya ya tasa k'eyar Hassana har bedroom d'in Hassana".

Habib kallan Hassana ya yi babu alamun wasa ko fara'a afuskar shi, ya ce, "Nemo ta kardar ki ban". Hassana tsayawa ta yi, tana kallan Habib ganin yadda ya wani sha mur, Hassana ita kanta cikin ta kai cin hanata ta fiya da Habib ya yi ta ke, kallan Habib d'in ta yi, ta ce, "Oga Habib ni ina ganin babu wani amfanin sai na nemo takardar, saki ne ka rubuta min, tom yan zu kai zaka fad'i saki nawa ka rubut... ". Habib d'aga hannun da ya yi zai mari Hassana ne ya sa tai shiru, ta yi sauri ta b'oye fuskarta k'irgin Habib, tana wani irin kuka. Cikin kukan ne Hassana ta ke magana kamar haka, "Oga Habib me naima da zaka rik'a marina haka?, kasan me ke damuna?, kasan yadda nake ji azuciyata?, na had'a kayana zan tai mahaifata ka hanani, kuma bacin haka ka bini da mari, da me kake son inji? ". Hassana ta idasa maganar cikin matsanancin kuka. Habib d'ago kan Hassana ya yi da ta tusa a k'irjin shi tana kuka, sannan ya jata suka zauna bakin gadon. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat da gaske kike na rubuta miki takardar saki? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib.Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "kin karanta takardar ne? ". Kai Hassana ta girgizama Habib. Shiru Habib ya yi, sannan ya ce, " Tom me yasa zaki yan ke hukunci akan abin da bi ki sa ni ba?, Shikenan, zaki iya tashi ki bi Mommy ku tafi, ko ba komai kad'ai ci zai kare min, gobe za'a d'aura aurena da Farida". Habib na fad'i ma Hassana haka ya ja k'ofar bedroom d'in da k'arfi ya fita".

Hassana zubewa tai a gadon tana kuka. Hassana ta dad'e tana kukanta sannan ta gaji ta lallashi kan ta tai shiru.
Habib ko barin gidan ya yi baki d'aya".

Hassana had dare tana nan kwance Sallah ka wai ke ta data sai abinci da d'azu Hajiya Turai ta matsa mata sai ta ci, ta tashi ta ci. Hassana na nan kwance Hajiya Turai ta shigo d'akin, Hajiya Turai zama ta yi tana nazarin Hassana. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter dan Allah ki fad'a min gaskiya Habib ya sake ki? ". Hassana k'asa tai da kan ta, sannan ta ce, "Mommy ban bud'e takardar ba, amma lokacin da zai ban takardar ya fad'i wasu kalmomi ne masu kama da saki".Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "kalmomi kamar wasu iri? ".

Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Mommy lokacin da naje mai da Maganar ya sakan, ya ban baki nak'i, shine sai ya shiga bedroom d'in shi, ya fito da takardar da ya ban, ya ce wai yaso ace ya rayu da ni, tom amma ni da ke mun k'i yarda, shine ya ban takardar". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Tom me yasa ke biki duba ta kardar ba? ". "Mommy haka nan ni ban duba ba". Cewar Hassana ".

Murmushi Hajiya Turai ta yi, dan tasan fargaba ce ta hana Hassana du ba takardar. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ina kika aje letter da kika shigo? ". Hassana gadon ta ta nuna ma Hajiya Turai. Hajiya Turai kuma kallan Hassana ta yi, ta ce, "Tashi mu duba mugani".

Hassana tashi ta yi suna duba ko'ina a bedroom d'in , amma ba suga letter ba. Hajiya Turai ce ta yi dabarar ya ye bedsheet d'in sai ga ko takardar. Hajiya Turai d'auka ta yi ta mik'ama Hassana sannan ta fita ta barta ita ka d'ai ".

Hassana ko zama ta yi, jin yadda zufa keketo mata, dan hannu da ta rik'e takardar ma kanshi rawa yake, dan gani take daga ta bud'e zata ga saki uku. Hassana cikin ja rumta ta bud'e letter ta fara karantawa kamar haka.
"SANAT tabbas ban san zuciyata ta shak'u da ke ba shak'uwa mai nisan gaske sai da kika bijiromin da maganar saki. SANAT hannuna ba zai iya rubuta abin da ki ke so ba, na rok'eki ki yi hak'uri, bana son kina furta min lamar da tai shigyan haka". Daga k'arshen rubutun Habib ya sa da manyan bak'i. 'ZUCIYATA TA SHAK'U DA KE SANAT".

Hassana koda ta gama karanta letter wani sanyi taji aranta, Alhamdulillah ta ke furtawa, ta ce, "Oga Habib kai zuciyarka shak'uwa ta yi da tawa, inda ni kuma tawa zuciyar ta fad'a tsantsar soyayyarka. Oga Habib ka so ni dan Allah ko rabin yadda na ke son ka ne, Wallahi zuciyata ba zata iya rayuwa ba da kai ba". Haka Hassana tai ta surutanta ita kad'ai. Ringing tone d'in wayar ta ne yasa ta dawo tunaninta. Hassana koda ta duba screen d'in wayar Number da aka kirata ce jiya Hajiya Turai ta ce karta d'aga Habib ne, Hassana tana cikin nazarin Number ne wayar ta tsinke, Wani kiran ne yak'ara shigowa.Hassana d'agawa ta yi ta kanga wayar a kunnan ta".

B'angaran Habib ko yana jin Hassana ta d'aga, ya ce, "Helloo SANAT ". Hassana da taji kiran har cikin ranta, rintse ido ta yi".

Habib kuma jin Hassana ta yi shiru, ya ce, "SANAT kin yi bacci ne, in kashe wayana? ". Hassana cikin kasalallar murya irin mai kashe jikin masoyi, ta ce, "Ogaa Habibbh ina ji". Habib da ke shingid'e sai da ya tashi ya zauna, jin yadda Hassana ta kira sunan shi, Ogaa Habibbh".

Habib numfasawa ya yi, sannan ya ce, "Kina ina yan zu ? ". "Ina bedroom d'ina". Hassana taba Habib amsa. "Ok, ina part d'ina kizo yan zu ki saman".

Hassana shiru ta yi, dan bata san ta yadda zata fita ba, tana tsoran Hajiya Turai tazo bata nan. Hakan yasa Hassana ta ce, "Oga Habib kai kazo mana ". "Ok, ke baza ki zo ba? ". Habib ya tambayi Hassana. Shiru Hassana ta ta yi, dan ba zata iya cema Habib, Eh ba".

Habib kuma jin Hassana ba ta ce komai ba, ta yi shiru ba amsa, ya ce, "SANAT ki zo yan zu, za muyi magana ne". Habib na fad'in haka ya kashe wayar shi".

Hassana ko tashi ta yi, ta lek'a falo taga Hajiya Turai bata nan, da sauri Hassana ta fito kamar muna fuka, ta fita daga Falon Hajiya Turai, ta nufi side d'in Habib".

Habib na nan kishingid'e kan caution ya ji nocking d'in Hassana, ta shi ya yi ya bud'e mata".

Hassana k'arasowa ta yi ta zauna gefan Habib, tana wasa da 'yan yatsun ta ta, Hassana gaida Habib cikin sanyi, sannan ta ce, "Oga Habib gani". Habib d'ago kai ya yi yana kallan Hassana ganin yadda yan zu-yan zu, ta canza ba kamar d'azu ba ta suka so su fasa mai kai ita da Hajiyarsa. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Ina letter da nace ki ne mo? ".
Chapter 70 · 0% Book details